Sashe 52
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma tace, "to bazai yu ba shiyasa daga wajan mai d'ori nan muka yo, bazan amince ka mayar da ita kamar jaka ba wallahi bazai yu ba, yau duka gobe duka jibi duka akan me!? Dan rashin mutunci kuma kace wai da sai ka b'alla mata k'ashin jikin ta a gabana a gaban iyayen ka, wannan shine karo hud'u da ka dake ta ko wanne da illar da kayi mata. Yusuf in ka gaji da zama da Asiya ka rabu da ita mana ai babu lallai babu dole, ka dinga wahalar da yarinya dan kaga tana yi maka biyayya? In zaka yiwa kowa ka zauna lafiya banda ni wallahi, bazan iya jurewa ba domin y'ay'ana nawa ne ni kad'ai, in baza ka daina shan giya ka daina dukan y'ata ba ka sake ta."
Wani iri yaji a jikin sa jin kalmar ka sake ta din da tace ya d'ago ya kalle ta sai ta d'auka hak'uri zai bata jin tace yayi saki sai tace, "Eh ka sake ta, ai zama da ita babu dole dan wallahi banza d'auki wannan wulakancin ba, aure ko shekara baiyi ba har yanzu ace an fara jeka gida ka dawo, ka sake ta in baza ka iya ba." _Ka sake ta._ shine abinda yake ji a zuciyar sa kawai da kuma kan harshen sa ya d'ago ya kalli Umman ya kalli Asiya da take aika masa da harara ya sake kallon Umman yace, "na sake ta!." Kamar an fizgo maganar daga bakin sa haka yaji sai ya fara kalle-kalle ko zai ga wanda ya furta maganar amma ya tabbatar shine ganin reaction din Umman ya canja ya koma na mamaki da tashin hankali ya saka shi jin dad'i a zuciyar sa dan ya tabbatar ba a mafarki hakan ta faru ba da gaske.
Wannan kalma da ya furta ba k'aramin dad'i ta yiwa Abbah da Ammah ba suka kalli juna kowa zuciyar sa tayi farin ciki d abinda yayi dan Allah ya sani basa son zaman da yake yi da ita kawai dan basa son shiga lamarin sa da ita ne ya saka suka zuba masa ido. Asiya ta wara idanu waje ta kalli Umma cikin tsoro itama ita take kallo shima Yusuf din Umman yake kallo tace, "me kace?." Yusuf ya sake kallon Umman yace, "eh na sake ta, kince in bazan iya zama da ita ba na sake ta, to bazan iya zaman da ita ba shiyasa nace na sake ta!."
"Kana cikin hankalin ka kuwa? Asiyan ka saka?." Sake kallon mutanen falon yayi ya tabbatar a gaske ne ba a mafarki ya sake ta ba ya sake kallon ta yace, "da hankalina mana, na sake ta ki d'auke ta ku tafi taje ta samu wanda zai iya zama da ita ni bazan iya ba" sai kawai ya tashi ya shiga cikin gidan ya barsu a wajan.
Asiya tace, "na shiga uku Umma kina Jin abinda yace fa? Innalillahi Umma bana so ya sake ni ina son mijina nidaj." Hararar ta Umma tayi sai ga kalli Su Ammah da suke kallon su ta mik'e tace, "lallai Yusuf a gaban idona dan tsabar wulakanci ya saki Asiya bayan yasan ni mahaifiyar tace, babu laifi ya kyauta zai kuma san dani yake zancen" ta fad'a tana yin hanyar waje Asiya ta kalli Ammah tace, "Ammah ki bashi hak'uri dan Allah ya mayar dani ." Ita dai kallon ta take yi kafin ta tashi tabi bayan mahaifiyarta tana kuka dan har ga Allah ita tana son zama da mijin ta.
Suna fita Mubarak yace, "wallahi Yusuf bai tab'a burge ni kamar yau ba, naji dad'i da ya rabu da wannan shegiyar yarinyar mai zubin aljanu, Marasa tarbiyya daga ita har babar ta, k'ananu mutane b'arayi wanda basu san abinda suke yi ba." Ammah ta kalle shi tace, "kira min Yusuf." Ya shiga ya samu Yusuf din a zaune a kan gadon Ammah ya dafe kai da hannu biyu ya kira shi suka dawo tare ya zauna kana kallon sa kasan bashi da lafiya Abbah yace, "Yusuf ka saki matar ka Asiya fa, meyasa kayi hakan a gaban babar ta?." Yusuf ya runtse ido sosai yake jin sassauci Akan abinda yake ji yace, "na jima ina son yin hakan amma na kasa, jira nake kawai wani ya bani umarni na aikata sai gashi ta bani umarni da kanta" ya dafe kansa yace, "na gaji da zama da ita wallahi, na gaji daman kawai so nake yi na aiwatar na kasa sai yanzu. HasbunallaAmmah kaina" ya fad'a yana dafe kansa da duka hannayen sa biyu Ammah ta kalli Mubakar tace, "d'auko min maganin nan nasa da sauri."
Da sauri ya d'auko a jarka baban ya mik'o mata ta karb'a ta tashi da kanta ta bashi sai da ta tabbatar yasha sosai sannan ta kalli Abbah tace, "Mu kai shi asibiti." Abbah yace, "bana asibitin bane sihirin da suka yi masa ne yake barin jikin sa." Mubakar yayi tsaki yace, "haka akwai ya d'aukowa kansa wahala yana zaune Lafiya da matar sa, Gashi ta shigo ta raba su ta dinga yi masa iskanci kala-kala ga k'arshen abun harda asiri."
"Zo nan mu kama shi a kai shi d'akin Humaira." Abbah da Mubarak ne suka kama shi zuwa d'akin Humaira aka kwantar dashi Abbah ya kalli Mubarak yace, "ka kira a duba shi in akwai wani abun a bashi magani." Mubarak da Abbah fita sukayi Ammah ta zauna a gefen sa tana kallon sa cikin matuk'ar tausayin sa.
Hankali tashe Umma da Asiya suka shiga gida Asiya ta tsaya a tsakar gida tace, "nifa Umma bazan kwana a gidan nan ba gidan mijina zan koma, haka kawai kina furta masa ya sake ni gashi yace ya sake ni, meyasa kice masa haka? Kina ganin kamar umarni kika bashi kina cewa ya furta babu b'ata lokaci. Umma in saki ne na shiga uku." Jin haka ya saka su Maimuna fitowa daga d'akin suka kalli Umma suka ce, "me yake faruwa ne haka naji Ana zancen saki?."
"Ba umma bace ta jawo Yusuf yace ya sake ni, wallahi bazan iya zama a gidan nan ba gıdana zan koma."
Maimuna tace, "garin ya ya sake ki? Ba anyi masa abinda bazai iya sakin ki ba? Ya kayi hakan ta faru ga Mari ga tsinka jaka?."
"Duk Umma ce ta jawo, tun farko daga wajan mai gyara sai da nace kar mu biya gidan su amma tace sai munje taja masa kunne a gaban iyayen sa, haka ta dinga fad'a masa in ka gaji da ita ka sake ta shi kuma yace na sake ta. Ni wallahi bazan zauna a gidan nan ba gidana na zan koma bazan iya zama cikin zafi da sauro ba wallahi." Fauzy tace, "gaskiya Umma da kin sani baki furta ba da kin sani bama aje gidan ba, yanzu ya sake ta ta dawo gida kayan d'akin aurena dame za'a yi kenan?." Momi tace, "dan yace ya sake ta ai ba saki uku yayi ba, ku kwantar da hankalin ku ni nasan Umma da Umma Sakina sai sun mayar da Asiya gidan ta."
Sai a sannan Umma ta samu k'arfin guiwa jin kalaman Momi tace, "Allah yayi miki albarka, ke kad'ai ce kika fahimci wacece ni dan ya aikata wannan abun ba komai bane ba. Ki shiga ka kwanta gobe zaki koma gidan ki, Maimuna bani dubu biyu in akwai a jakar ki." Maimuna ta shiga ciki ta d'auko Umma tace, "zan je na dawo, gobe Yusuf zai mayar dake koda baya so nayi miki wannan alqawarin." Asiya ta goge idanun ta gabad'aya ta daina jin zafin da hannun ta yake mata tashin hankalin ta kar ace Yusuf ya rabu da ita dan bata san inda zata saka ranta ba.
Umma Kai tsaye gidan Umma Sakina ta wuce ta same ta ita da yaran ta suna cin abinci ganin ta duk suka tashi bayan sun gaishe ta Umma Sakina tace, "da ganin ki ba Lafiya."
"Ina fa Lafiya, yaron nan Yusuf ne ya daki Asiya har ta karye a hannun ta daga kwana mai gyara muka wuce gidan su dan na ja masa kunne gaban iyayen sa." Kafin taje k'arshen maganar Umma Sakina tace, "Allah yasa ba cewa kika yi ya sake ta ba?." Umma tace, "haka nace masa ya kuwa ce na sake ta."
Umma Sakina ta daki cinya tace, "shikenan kin tarwatsa mana komai kin lalata shi saboda bak'in son y'ay'an ki bazai ki iya hak'uri ba har sai da kika je gidan su. Yanzu gashi nan kin b'arar mana da damar da muke da ita." Umma tace, "ai ni da gadara nace yayi sakin dan nasan bazai iya ba, kuma kallon da yayi min da nace yayi na d'auka na tuba da nan hak'uri ban d'auka zaiyi din ba ai da bazan ce ba."
"Kiris yake jira haka malam yace min jiya da naje akan maganar d'auke masa kudi da tayi a banki a hana shi d'aukar mataki a kai yake cemin kiris yake jira ya sake ta ta gama fita daga zuciyar sa, ina k'ok'arin sake cusa ta ki je kin lalata mana komai. Itama shegiyar satar ta kamar b'era da shegiyar k'zantar tace ta kawo ta wannan matakin ai."
Umma ta dafe kai tace, "Na shiga uku ni Atika, yanzu meye mafita a san abinda za'ayi in ta bar gidan Yusuf yanzu ai mun lalace."
"Yayi tafiya zuwa Abuja a jiyan, kuma aikin sa na amince dashi gashi baya nan, ban san ya za'ayi ba."
"A dan yadda za'ayi zuwa gobe ya mayar da Asiya in ba haka ba baban su ma dariya zaiyi min ba mutanen gari ba."
"Duk laifin ki ne wallahi, bakya iya sarrafa soyayyar yaran ki a zuciyar ki ke lallai komai akayi a kan su sai kin mayar kamar kece kawai mahaifiya a duniya, yanzu zuwa gidan nasu ma da kike yi ai ba siyawa kai mutunci bane, shiyasa dangin sa kaf babu mai son Asiya."