← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 93

Sashe 35

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon sa suke yi babu wanda ya iya magana kafin Abie yace, “Sai ka tashi kaje asibitin inda take ka biya komai kafin ta sake biyo ka nan tayi maka sabon lissafi.” Bai isa motsawa ba yana kan k’afar Ammah baice kanzil ba dan bazai iya magana ba a wannan lokacin ba. Abie yace, “Ammah ni na wuce sai anjima, naga an fara yin decoration, me humaira zatay ne yau?.” Yayan Abuja tace, “Wai henna party zatayi.”
“Bidi’a Kala-kala” ya fad’a yana fita har lokacin Ammah bata ce masa komai ba shima bai ce ba bai kuma d’ago kansa daga k’afar ta ba.

Humaira ce ta shigo tana waya tana cewa, “Yauwa sis na gode sosai sai na ganki.” Ta fad’a tana kashe wayar tace, “Ammah Ameena ce tace ta saka masu small chops zasu zo yanzu nan daman kuma kamar na sani ban kira ko ba.” Ammah tace, “banda kayan rabon da tayi harda wannan wahalar? Zata zo din ne?.”
“Tace min dai wai gata nan dai amma gobe dai zata je.” Ammah tayi murmushi akwai bata cse komai ba Humairs tace, “Wai Yaya Yusuf ne a kwance haka?.”

Yayan Abuja ta tab’e baki itama haka bata ce komai ba ta wuce zuwa ciki dan an kusa fara mata make up. Ammah ce ta gaji da shirun da yayi sai ta d’ago kansa daga jikin ta taji jikin sa zafi sosai tace, “Subahanallahi Yusuf baka da lafiya daman?.” Kallon sa tayi taga fuskar sa kamar an zuqe ta tace, “me yake damun ka? Jikin ka yayi zafi sosai.”

Baice komai ba sai kallo kawai ya mik’e tsaye ya fita daga falon Ammah ta kalle shi tace, “Yaron nan akwai abinda yake damun da fa. Kalli yadda ya koma kamar ba shi ba.” Yayan Abuja tace, “ba haka suka bar Yusuf ba fa Ammah sun had’a da asiri wallahi, tun farkon neman auren yadda yake rawar kan nan wallahi nasan akwai asiri a ciki, amma sun min daidai ita wacce bata asirce shi ba ai azabtar da ita yake yi.” Amma bata ce komai ba tayi shiru kawai dan duk abinda ya faru shine ya jawowa kansa da kansa.

Yusuf baice asibitin ba gida ya wuce kawai ya shiga b’angaren Ameena ya wuce sama har d’akin Ameena ya kwanta a kan gadon ta da har lokacin yana nan kamar tana gidan dan ba komai suka d’auka ba, a wannan lokacin ne zuciyar sa ta kasa rik’e abinda yake zuciyar ya fashe da kukan da bai san dalilin sa ba a wannan lokacin kawai yaji zubar su ne dan bazai iya cigaba da rik’e su ba. Kuka yake sosai kamar d’an yaro gashi bai san dalili ba abinda ya sani in baiyi kukan ba zuciyar sa zata iya bugawa.

Ya jima yana kukan sosai kafin ya koma sauke numfashi a hankali bacci ya d’auke shi. Sai la’asar ya tashi ya shiga band’akin ta yana kallo ga shower gel dinta nan da komai a ajjiye kamar tana ciki ya jingina da bango yana kallon komai yana ji a ransa kamar zai ganta. Dakyar ya lallab’a yayi alwala ya fito yayi sallah a d’akin nata ya zauna inda take zama tana jan charbi yayi tagumi ba tare da yasan abinda yake damun sa ba. Abinda ya sani yana tunanin Ameena a wannan lokacin, yana jin kewar ta sosai a zuciyar sa da gangar jikin sa, yana ji kamar a mafarki in ya tuna wai babu Ameena a gidan sa, wai shi da kansa ya sake ta abin yana d’aure masa kai sosai.

Abbah ya gani yana yi amsa waya ya d’auka Abbah yace, “malam duk inda kake ka wuce asibitin da matar ka take kaje can ka biya abubuwan d aka kashe, dan rashin hankali ka yiwa yarinya illa kuma kayi zaman ka a wani wajan baka je inda take ba? Ka tashi ko me kaka yi ka tafi kaje can ka biya komai, wallahi na sake kira baka je ba sai ranka ya b’aci.” Datse kiran Abbah yayi Yusuf babu yadda zaiyi dan badan Abbah ba wallah baza shi ba ya tashi ya fita ya hau sama yayi wanka ya canja kaya ya fito kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ya hau mota ya tafi asibitin da Abbah yace masa.

Sai baya ya shiga ne ma ya tuna ashe fa bai san a inda suke ba gashi babu wanda zai tambaya balle a raka shi, yana ajjiye motar yaga Momi k’anwar ta tana magana da wani mutum a tsaye sai ya fito lokacin yaga ta shiga ciki yabi bayan ta har d’akin da yaga ta bud’e ta shiga, shima bud’e k’ofar yayi ya shiga da sallama ya same su a zaune gabad’aya su harda Umman da Umma Sakina suka amsa kowa fuska a d’aure ana kawar da kai a lallai anyi musu laifi, “Barkan ku da yamma.”
“Sai yanzu kaga damar zuwa kenan?” Umma ta fad’a tana kallon sa.
“Yanzu na samu lokaci” ya fad’a Tana kallon Asiyan da take kwance. Umma da mamaki tace, “da Baka da lokacin zuwa ka ganta kenan? Ka yiwa yarinya wannan asarar kace sai yanzu ka samu lokaci?, dan Kaga na bada dama a sake ka shine kake min gadara?.” Banza yayi mata bai amsa ba dan yadda yake ji a zuciyar sa tsaf zai iya fad’a mata magana.

“Bashi bill din abubuwan da aka kashe wanda kika biya ya biya ki kudin ki” umma ta fad’a tana kallon Maimuna. Maimuna ta mik’a masa takarda ya karb’a yana kalla ganin kudin kasan k’arya ne sai ya kalle ta yayi murmushi kawai yace, “Zan tura miki.”
“Tura yanzu” ta fad’a tana kallon sa yayi dariya kad’an ya d’auko waya yana dannawa tana fad’a masa yana rubutawa har ya tura mata Umma tace, “Wallahi ko nan gaba kar ka sake dukar min yarinya ba jaka bace ba.”

Yusuf yace, “a ja mata kunne ko nan gaba kar ta sake saka iyayena a maganar ta, daga yau kuma in ta sake yi min sata ko mai aka kashe a asibiti za’a dauka a kudin satar da take ajjiyewa a biya. İn kuma ta saka duka yanzu ta fara shan sa” ya fad’a ba tare da ya kalle su ba ya juya ya fita Umma Sakina tace, “Lallai akwai sake akan lamarin nan, mu yake kalla ya fad’awa wannan maganar?. sai mun sake mik’ewa akan wannan yaron matuk’ar ba so muke nan gaba yafi karfin mu ba.” Umma mamaki ya cika mata zuciya ganin abinda yayi amma sai tace, “shi d’in banza ai bai isa ba wallahi, amma zamu sake zage dantse dan nuna masa wanda ya tab’9 ba wanda aka ake tab’awa a zauna lafiya bane ba wallahi, Mun fi karfin sa nesa ba kusa ba.” Maimuna tace, “Wai harda a ja mata kunne, Kaji wannan mutumin dan Allah.” Duk sukayi kwafa alamun za’a sake had’uwa dan sai sunyi maganin sa.

Washe gari juma’a Ameena ta shirya ta fito tayi kyau sosai dan kayan da ta saka sun amshe sosai ta riga da siket ta saka rigar har guiwa mai fad’i tayi rolling kanta da mayafi ta d’auki jaka yayi matuk’ar kyau sosai kamar wacce bata haihu ba. Aunty Aisha ce take kallon ta tunda ta fito tana cewa, “kai yarinyar nan kinga yadda kika yi kyau kuwa?. Wallahi babu wanda zai ce ke kika haifo Zaitun.” Tayi dariya tace, “Kai Aunty, dan Allah wai yanzu baza ki je ba?.”

“Babu Inda zani mijina zai dawo anjima, kije kedai amma banda ni.”
“Wallahi bana son zuwa ni kad’ai ga Zaytun tana can.”
“Ba Rukayya kika ce zata raka ki ba?.”
“Bata da lafiya bazata je ba.”
“Sai ki yii hak’uri ki tafi haka, nikam na wuce sai kin dawo” ta fad’a tana wucewa ciki dole Ameena ta fita harabar gidan amma babu wanda Yaya yace ya dinga kaita duk inda zata je.

Dawowa ciki tayi ta masa waya bai d’auka ba tana nan zaune har akayi magriba Aisha ta fito tace, “baki tafi ba?.” Tace, “eh Aunty, baya nan wanda zai kai ni din.”
“Gashi ya hana ki Jan mota, kuma fita ki gani ko yana nan yanzu, ni ban san dalilin sa na hana ki Jan mota ba wallahi.” Ta amsa da to ta tashi ta fita amma baya nan sai Al’ameen da yake a tsaye a wajan mai gadi sun magana ta nufi wajan da niyar tambayar mai gadin.
Kallon Ameena yake da dukka hankalin sa dan tayi masa kyau fiye da tunanin sa a lokacin ta k’araso wajan sa tace, “ina yini.” Yayi murmushi yace, “lafiya lau Ameena, ina zuwa da magriba nan?.”

Ameena tace, “biki zanje ga Yaya yace akwai Salisu zai dinga kaini amma ban ganshi ba.” Mai gadin gidan Yaya yace, “Salisu yaje Wudil wallahi, duk yadda akayi bai san da fita yau din ba.” Ameena tace, “shikenan to bara na hak’ura na koma ciki.” Al’ameen yace, “an ina ne wajan bikin?.”
“A nan cikin nasarawa wajan yake.”
“To bara na d’auko mota sai na kai ki.” Ta amsa da to ta shiga ta fad’awa Aisha ganin ta bada goyan bayan hakan sai hankalin ta ya kwanta dan tsoron fad’an Yaya take yi.

Ba jimawa Al’ameen yazo suka tafi wajan bikin shida Ameena tana gaba a zaune, suna tafiya babu mai magana a cikin su yace, “wacce makarantar kike yanzu?.” Ameena tace, “wata private university ce a nan cikin hotoro.”
“Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya bada nasara.” Ta amsa da amin tayi shiru bata sake magana ba sai satar kallon ta yake ita kuma kallon ne bata so dan tana Lura dashi kawai tana basarwa ne kamar bata gani ba.
Chapter 35 · 0% Book details