← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 93

Sashe 12

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aliya tayi dariya kad’an mai nuna zallar ciwon da yake zuciyar ta tace, “Ai duk wanda ya shigo gidsn nan bai isa ya fita ba sai in babu igiyar auren sa a kanta.” Fiddausi tace, “kamar ya?.”
“Da alama kema irin mu ce duk ba’a yi bincike Akan Alhaji ba aka aura masa mu. To wallahi ko nan da gate din farko baki isa kije a ‘kasa ba, sai dai a kai ki a mota kuma duk motsin ki ana kallo baki isa kije wani wajan ba sai dai in ya sake ki babu auren sa akan ki. Kinga ni daga Katsina ya auro ni amma tun bayan da naje gıda sau d’aya lokacin Muna tsaka da soyayya ban kuma zuwa ba har yanzu, akwai lokacin ma da amfani da waya sai ya hanaki gabad’aya.”

Naja’atu tace, “duk Inda kike son zuwa za’a kai ki Fiddausi amma ke dai ki fita ke kad’ai k’arya kike kuma babu inda zaki sake zuwa daga wannan waje da kika je sai gidan nan.” Fiddausi tayi shiru sai hawaye kawai da take yi ta ma rasa ne zata ce Aliya ta sake cewa, “Addu’a ce maganin mu kawai a gidan nan amma duk yadda kike tunanin uqubar gidan na ta wuce haka” ta fad’a tana danna wayar ta ta fito mata da wani hoto tace, “Kalli wannan hoton ki gani.”

Fiddausi ta d’aga jajayen idanun ta ta kalli hoton Aliya tace, “nice a jikin hoton kafin nazo cikin gidan nan” ta kashe wayar tace, “a baya ni mai kib’a ce wacce za’a kira da y’ar lukuta, amma yanzu baza ki tab’a cewa Allah yayi kib’a a jikina ba Fiddausi saboda tashin hankalin mijin ki komai zaki dinga ci wallahi bak’in cikin sa bazai barki k’iba ba.”
Fiddausi tace, “amma meyasa baku yiwa iyayen ku waya ba?.” Aliya tace, “duk wata hanya da zata Sada ki da wanda kika sani ya toshe ta, in waya ce ya saka anyi masa blocking kaf lambobin wayar ki, amfanin wayar ki kawai ki kalli wani abun ko kiji wak’a amma ko internet baza ki bud’e ba balle ki samu damar turawa bloggers kice hide my id.”

Fiddausi ta fesar da iska tana girgiza kai cikin rashin sanin abinda zata ce dan ita jin ta take yi wani iri kamar ba waccan Fiddausin ba Naja’atı tace, “ki daure ki fara addu’a in bakya yi Allah ya raba ki da wannan gidan domin zaman sa yafi zaman gidan prison.”
Aliya tace, “Akwai kud’i ko nawa kike so zai baki, akwai mota duk wacce kike so zaki hau, in Nigeria kike so ki bari zai kai ki amma kwanciyar hankali ta minti daya babu ita a wanann gidan. Amma akwai kudi dan tashin farko sai ya saka miki miliyan goma an account amma basu da amfani dan baza ki more su ba.”

Fiddausi tayi shiru ita dai ta tallafe hab’a tana zare ido tana jin maganar Aliya ta k’arshe da take cewa, _Akwai kudi, akwai mota akwai kuma zuwa duk ina kake so, to wannan ba shine kwanciyar hankali ba?._ Fiddausi ta d’ago ta kalli Aliya tace, “wannan abubuwan da kika lissafa ba Sune kwanciyar hankali ba?.” A tare Aliya da Naja’atu suka kalli juna sukayi murmushi Aliya tace, “Duk irin tunanin mu daya dake Fiddausi, amma na tabbata daga yanzu zaki fara gane kud’i ba shine kwanciyar hankali ba, kwanciyar hankali daban kudi daban Fiddausi. Domin daga dawowar ki gidan nan zuwa ynzu nasan kin tabbatar da akwai kwanciyar hankali sannan akwai kud’i, akwai kwanciyar hankalin da tafi kudi.”

Naja’atu tace, “Inda anyi cikakken bincike baza’a baki auren Alhaji Bello ba, to iyayen mu saboda shuran da yayi a fannin kudi ya aka suka bamu shi ba tare da dogon bincike ba. Wallahi Fiddausi har kud’in aurena an kawo an saka rana amma tunda Alhaji ya bayyana na bijirewa waccan auren sai da aka hak’ura hankalina ya kwanta. A budurwa ya d’auko ni ya kawo ni gidsn nan ko nace ya kaini london dan ni a can muka fara zama, ji nake babu kamata a lokacin duniya tayi min dad’i saboda na samu rayuwar da nake mafarki, daga k’arshe ga Inda na k’are” ta fad’a murya nayi rawa kafin tace, “tun ba’a je ko ina ba na fara yin dana sani wacce bata da amfani a wajena.”

Aliya tace, “Dukkan mu k’addara d’aya ce fa had’a mu a wannan gidan, kawai Fiddausi ki yi hak’uri zaki ta ganin bak’in abubuwa a gidan nan wanda ko a film baki tab’a ganin su ba. Ki kuma daure ki yiwa Nabila biyayya in ba haka ba wallahi zata saka yayi miki dukan tsiya wata ran kuma tace sai kin bata hak’uri.”

Fiddausi tace, “ina yaran nasa da yace min yana dasu?, ina Uwar gidan sa?.”
“Yana da manyan yara sosai wacce uwar gidan sa ta haifa amma yanzu basa tare tunda ya fara harkar nan ta tattara komai mata ta bar shi ita da yaran ta. Bamu sani ba ya sake ta ko bai sake ta ba Allah ne ya sani. Yana da wata matar a can New York wacce ya barwa mai gidan sa bature shugaba su a wannan fanni ita yana abinda yake so da ita bamu sani ba ko ya sake ta ko har yanzu matar sace. Yanzu sai ni sai ke sai kuma Naja’atu sai kuma wacce k’addarar take a kanta zata shigo nan gaba.”

Naja’atu tace, “a duk shekara yake yo auren budurwa ko bazawara ya danganta da abinda bokan sa yace ya samo. Dan boka zance ba Malami ba. Ki gode Allah ma da kika je New York kika dawo wannan mai gidan nasa baice yana sonki ba.” Fiddausi ta kalle ta yace, “Bokan sa kuma?.” Naja’atu tayi dariya tace, “Eh bokan sa, kin d’auka wai ya ganki dan yana so ne? Kin d’auka duk abinda ya dinga yi yayi ne dan yana son ki?. Hmmm Ki sani tun daga kan halayyar ki, kammanin ki, komai naki bokan sane yace a nemo mai irin ki ayi amfani da ita saboda samun wani abu nashi. Babu lallai ki yarda yanzu amma nan gaba da bakin sa zai fad’a miki Fiddausi kamar yadda ya fad’a mana. Ni ya auro ni saboda aikin da ake so za’a yi masa dan cin galaba akan mai gidan sa na New York kuma anyi aiki yayi nasara. Babban burin sa a yanzu bai wuce yayi amfani dake ta baya ba dan shine mafarin aikin sa a kanki.”

Fiddausi ta girgiza kai jikin ta har rawa yake yi dan abubuwan da taji kamar shocking aka jona mata a jikin ta ta girgiza kai tace, “bazai tab’a samu ba kuwa har abadah!. Indai a wajena ne ni Fiddausi bazai samu abinda yake so ba, nafi karfin sa wallahi.”

#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema

Book3
008

Aliya da Naja'atu sukayi murmushi a tare bayan sun kalli juna jin kalaman Fiddausi Wanda a wajan su tamkar busa ce Aliya ta girgiza kai ta mik’e tsaye tace, "Kawai ki cigaba da addu'a Fiddausi, amma wallahi duk yadda kike tunanin mijin ki wallahi ya wuce haka. Allah dai ya kare ki kawai." Naja'atu ma ta mik’e tsaye tace, "Abinda ya kamata kenan ba wai ko cika baki kice ke bazai yu a wajan ki ba, Alalh ya k'ara Lafiya amarya" suka fad’a suna fita suka barta a zaune tana bin su da kallo.

"Wai da gaske abinda suka fad’a gaskiya ne kuwa?." Ta fad'a a bayyane tana sake kallon k’aton d’akin da take ciki dan har lokacin zuciyar ta bata wani gamsu sosai ba. Sai ta girgiza kai tace, "Ke Anya ba amfani sukayi da mafarkin da nayi ba suka sake tsorata ni ba? Taya hakan zata kasance wai a zahiri ba a film ba?. Ko a film din America ba’a wannan k’azantar balle a zahiri.”

Tayi k’aramin tsaki tace, "Kai wannan ba gaskiya bane taya hakan zata faru kuma suke zaune a gidan nan basu nemi hanyar guduwa ba?. Kawai suna so su tsorata ni ne amma ba gaskiya bane.” Dukan kanta tayi dan ta ma rasa wanne tunani da zatayi ta kwanta a kan gado tana sake tunanin abinda suka fad’a mata wanda take jin sa tamkar almara. Tsaki ta sake yi tace, “wannan karyar banza ce ba gaskiya bane.”

            Rukayya tana kwance a kan gado suna waya da Ameena akan abinda yake gaban ta a lokacin tace, "wallahi Ameena ganin abun nake kamar a mafarki wai nice Baba yake jira yau na bashi amsar wa nake so a cikin Umar da Ibrahim. Sai naji kamar ba ni ba dan a baya in akace min wannan lokacin zai zo ko sai naga kamar kawai ana fad’a min ne dan naji dad’i.” Ameena daga b'angaren ta tace, "Shiyasa nake fad’a miki ki yi hak’uri lokaci ne gashi kuma lokacin naki yazo yanzu sai labari. Yanzu wanne kika d'auka a cikin su? Wanne zuciyar ki tafi amin cewa dashi?."

Rukayya tace, "wallahi Ameena na rasa abinda zanyi ni akan lamarin nan, dukkan su bazan ce ga wanda nake so a cikin su ba, abinda na sani ko wanne yana k’ok’ari wajan ganin ya nuna kin yana sona ba kamar Ibrahim da ya manta ni k'awar Fiddausi ce. Shi Umar yana da aure ba ko yaushe yake sakewa ayi waya ba saboda matar sa hakan kuma yana burge ni sosai, Ibrahim kuwa kalaman sa suna saka ni a nishadi, Gashi Bawai na soyayya yake amfani dashi ba; magana irin wacce muke yi yanzu haka yake yi amma sai ya bani nishadi a zuciyata. Ni ban sani bama ban san me zan ce ba wallahi Ameena, har bana so anjima tayi Baba ya kira ni dan ban San me zance masa ba.”

Ameena tace, Kiyi addu'a ki kuma istikhara duk wanda yake da alkhairi Allah ya zab’a miki. Amma kin San me?."
"Sai kin fad’a."
"Wallahi nafi son ki auri Ibrahim akan Umar?.” Rukayya tace, "Ibrahim fa tsohon mijin Fidy ne Ameena."
Ameena tace, "Tsaya mana, ki tambaye ni meyasa nake so kiji hujjata mana."
Chapter 12 · 0% Book details