Sashe 63
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rukayya tunda sukayi wannan maganar da Ibrahim shikenan baya walwalaa ta rasa gane kansa gashi ranar juma’a ce washe gari tafiyar su hankalin ta gabad’aya baya tare da ita sai Umma ce take fad’a mata yadda ake had’a kayan tafiya tana had’awa saboda mantuwa. Bayan sallar juma’a ya dawo da leda a hannun sa ya ajjiye mata a gaban ta yace, “ki saka a jakar ki” yana fad’a ya shiga d’aki ta d’auki ledar ta bud’e taga soson wanka ne da sabulu da sabon abin wanke baki da sauran su.
Ta d’auki ledar tabi bayan sa ta same shi a zaune ya cire rigar jikin sa ta zauna tace, “Wai duk akan maganar ranar nan ne shine har yanzu ka ke fushi dani? Na baka hak’uri ya kamata ace ka hak’ura ban fad’i maganar saboda wani abun ba kai ka sani.” Ya zauna sosai yace, “Akan maganar Fiddausi zanyi fushi Rukayya? To akan wanne dalili ma zanyi fushi a kan maganar ta?.”
“To gashi kana fushi ka kasa sakewa kamar baya.”
“ni ba fushi nake dake ba, domin banga abin fushi a abinda kika ce ba balle nayi, magana kika yi akan gab’ar b’acin ran da nake ciki a lokacin shiyasa ban ma saurare ki ba, in nayi fushi dake magana ma bazan miki ba dan ban iya fushi ba. Ban tab’a fushin bane kiyi fatan kar nayi, bana yawan fushi ko da yaushe, amma in nayi sai kin gwammace gwara nayi kad’an-kad’an na hak’ura.”
Tace, “to kayi hak’uri dan Allah.”
“Nace miki ba laifi kika yi ba kece kike ganin kamar laifi kika yi shiyasa kike baya-baya dani, Amma ni baki min komai ba meye abin b’acin rai a maganar ki to?.” Tayi Ajiyar zuciya tace, “har naji dad’i wallahi.” Yayi murmushi yace, “da gaske?.” Ta daga Kai alamun eh ya sake yin murmushi yace, “kin gama had’a komai naki? Kar kiyi mantuwa fa.” Rukayya tace, “Komai na had’a sai abinda ka bani yanzu, shima yanzu zan saka. Umma tace min ana tafiya da yaji wai harda maggi, gashi can na daka d’azu da yawa har su Hajiya na saka a jakar.”
Yayi dariya yace, “kin had’a kayan Amir?.”
“Eh na had’a, d’azu da Zuhra ma tazo har na bayar ta tafi dashi wajan Umman.” Ya girgiza kai yace, “ki fad’awa Umma a barshi ya kwana biyu a wajan babar tashi, koda yake ma ai a Unguwa d’aya ne basai ya kwana ba zai dinga zuwa ko yaushe kamar ma yana wajan nata ne ko?.” Rukayya tayi dariya kad’an tace, “Gaskiya ne kam kusan ko yaushe ma yana wajan ta, zatayi farin ciki da hakan mum gode.” Baiyi magana ba sai Rukayya ta sake cewa, “wai baka ji kamar a mafarki zamu tafi makka?.”
“Nifa sai naga mun tafi zan tabbatar gaskiya ne ba mafarki ba. Dan yanzu kam kallon abin nake kawai gashi nan dai ba gaskiya bane.”
Tayi dariya tace, “balle ni da ban san ma tafiyar zata kasance har ni ba.” Yayi murmushi yana kallon ta itama shi take yi yace, “daman Allah yayi dake za’a je.” Ta girgiza kai tace, “haka ne kam.”
“Yanzu meye Abu na gaba?.”
“Sai dai mu jira goben mu gani” yayi dariya yace, “to Allah ya kaimu” ta amsa da amin suka cigaba da hirar su.
Kamar yadda Yaya Adam ya cewa Ameena zata fad’a masa Sakamakon Al’ameen da yamma ya kira ta ta zauna ya kalle ta a nutse yace, “yau mukayi zaki tsayar min da magana, ya kike gani?.” Ameena ta sauke numfashi tayi shiru tana tunani kafin tace, “na amince Yaya.”
“Kina nufin kin amince da auren Al’ameen?.” Ta daga kai alamun eh yayi murmushi yace, “shikenan to, Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Ina tabbatar miki da baza kiyi dana sanin zab’ar Al’ameen ba.” Murmushi take yi tana kallon sa kafin yace, “tashi kije.”
Tashi tayi ta shiga ciki shi kuma ta fita ya shiga gidan Al’ameen din dan sanar dashi abinda yake faruwa. Murna wajan Al’ameen kamar an d’aura auren y dinga godewa Yaya Adam shi dai dariya yake masa kawai yana ce masa mai son auren yara shi kuwa murna kawai yake yi dan yaji dadi sosai kuma yana son Ameena ba kad’an ba.
Asiya babu wanda take ragawa a gidan su har Umman gabad’aya su sun fita daga sabgar ta kowa harkar sa yake yi a share ta dan kiris take jira ka kula ta ta fara yi maka rashin kunya. Fitowa tayi d’aga d’aki ta zauna kusa da Umma tace, “Umma nida na gashi wallah, zan shirya naje har gidan Ammah na bashi hak’uri bazan iya cigaba da zama a gidan nan. Zanje ni na bashi hak’uri tunda shi bai zo ba. Ta Inda aka hau ai ta nan ake sauka.”
Maimuna ta harare ta tayi tsaki tace, “in sha Alalh bazai mayar dake ba. Naira dubu d’ari biyar kawai ki bayar a biyawa Umma bashi kin kasa baya akan ki taci bashin, kuma kud’in nan ba da gumin ki kika samu ba balle kice kin san zafin nema, ajjiyewa akayi kika d’auka amma wai sai dai a fad’a miki yaushe za’a biya ki dan ma baki da mutunci baki san mutunci ba, dan Umma zata karb’i abin ki sai ta biya ki?.”
“Kinga Yaya ni nasan wahalar da nasha na tara kudina dan haka bazan yi asarar dubu d’ari biyar a banza a biyan bashi ba, in za’a fad’a min ranar da za’a biya na bayar in ba’a za’a fad’a min ba bazan bayar ba.” Umma da take kallon ta tace, “kar ki bayar Asiya ki rik’e kayan ki bana so.” Asiya ta turo baki gaba tace, “Nidai zan tafi naje nayi bikon mijina, an kashe min aure an cuce ni” ta fad’a tana shiga d’aki sai gata da mayafi ta yafa ta fita da hannun ta guda d’aya.
Maimuna yaja tsaki tace, “Ashe dai bata da hankali, da gaske zuwan zatayi fa.”
Umma tace, “kyale ta, zata dawo da k’afar ta.”
“Asiya bata da mutunci bata da hankali kuma.” Umma tace, “gashi ban san inda zan samo kud’in ba kuma Sakina akan kud’in nan sai ta kama ni.” Maimuna tace, “bara na je na binciko inda Atm din ta yake muje a d’auko kud’in koda bata so. İn yaso in ta dawo mu k’ona gidan.” Tashi tayi ta shiga d’akin da Asiya ta fito ta duba ko ina amma babu alamun ta kwashe kayan ta ta fito ta kalli Umms tace, “Wallahi ta kwashe komai.” Umma tayi Ajiyar zuciya kawai bata ce komai ba zuciyar ta amma cike take da takaicin halin Asiya abinda bata tab’a ji ba.
Asiya kuwa kai tsaye gidan su Yusuf ta wuce mai gadin ya barta ta shiga dan ya Santa ta shiga falon da sallama a nutse suka amsa kowa ya juyo yana kallon ta dan Abbah ma yana nan tunda ya dawo daga masallaci bai sake fita ba sai sallah. Ammah tace, “A’a Asiya kece tafe?.” Tayi murmushi Jin Ammah ta kira sunan ta tace, “eh Ammah.”
“Shigo ki zauna mana.” Ba musu ta k’araso ta zauna tace, “Abbah ina yini.” Ya kalle ta yace, “lafiya lau.”
“Ammah ina yini.”
“Lafiya lau Asiya, ya gidan naku?.”
“Lafiya lau.” Daga nan tayi shiru bata ce komai ba Ammah ma tayi mata shiru daga baya tace, “Ammah daman nazo ne akan naji shiru har yanzu bai je ya dawo dani ba, wallahi na daina duk abinda nake yi bazan sake ba. Kuma ni ba dukana ma yayi ba fad’uwa nayi akan hannun shine ya karye, dan Allah ki bashi hak’uri ya mayar dani.”
Ammah tayi murmushi tace, “Biko kika zo kenan?.” Ta d’aga kai alamun eh Ammah ta sake yin murmushi tace, “to ai bani zaki samu ba shi ya kamata kije ki samu da maganar bani ba. İn yaga zai mayar dake sai ya mayar tunda abin naku ya canja salo mace ce take zuwa biko.”
“Eh kamun k’afa zanyi dake Ammah, ki taimaka min ki saka ya mayar dani wallah ko bacci bana iya yi.” Ammah ta kalli Abbah da su suke kallo ta sukayi dariya kad’an ta sake kallon Asiya yace, “Asiya sanda kuka yi fad’an ku bana wajan, kije ki same shi tunda shi bai je ba ke kin zo kinga shikenan sai ku daidaita.”
“Asslamu alaikum” ya fad’a yana shigowa falon a snayaye kamar ko yaushe Ammah ta amsa kafin tace, “shikenan ma gashi nan yazo, Yusuf ga Asiya tazo bikon auren ka.” Ya kalle ta ya kalli Ammah zai wuce Ammah tace, “dawo nana kana gani kayi bak’uwa gata a zaune zaka shiga ciki kuma.” Yusuf yace, “Ammah ai na fad’a miki ni babu aure a tsakani na da ita” ya kalli Asiya yace, “kee! Na sake ki saki d’aya, biyu,uku. Kinji abinda nace ko? Na sake ki saki uku kar na sake ganin k’afar a gidan nan daga yau din nan.”
Asiya ta dora hannu d’aya a kai tace, “Wayyo Allah na shiga uku, Yusuf kar kayi min haka ka taimaka min kar kace ka sake ni saki uku in ba haka ba ban san ina zan saka rai na ba, ka daure kayi hak’uri ka mayar dani wallahi zan canja daga yau.” Kamar zai magana sai ya fasa ya tsaya sosai yace, “kina so na mayar dake?.” Ta d’aga kai da sauri yayi murmushi k’arfin hali dan ta bashi dariya da alama ta haukace yace, “fad’a min duk abinda kika shirya a kaina tun kafin na aure ki har bayan aure ki.”
Asiya tace, “ban gane ba.” Yusuf yace, “ina so nasan ya akayi ma kika saka na aure ki? Sannan wanne irin abubuwa kika yi a zama na dake a a kaina?.” Asiya tace, “indai na fad’a zaka mayar dani d’akina?.” Murmushi yayi jin abinda tace ya tabbatar bata da hankali yace, “eh.” Asiya ta gyara zama tace, “Tunda ka fara cewa kana sona muka tabbatar ba da gaske kake ba shine muka ce baka isa ka gudu ba sai ka aure ni, daga nan na fara saka maka magani in kazo gidan mu a abinci ko abin sha a haka har ka furta cewa zaka aure ni” ta tsaya sosa kai yace, “ina jin ki.”