← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 93

Sashe 75

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty Aysha tace, “haka ne kam.  Baya muke gani wanda daman dole shi samu gani gaskiya amma wani lokacin ka koma din yafi sabon aure ness ba kusa ba, kowa akwai k’addarar sa. Ya tab’a min zuciya nima sosai in da rabon komawar ta wajan sa Allah ya daidaita su, in babu Alalh yasa Al’ameen ya zama alkhairi a wajan ta.” Yaya Adam yayi shiru baice komai ba har suka gama magana sannan ya tashi ya shiga ciki dan maganar da suke ma ta watse.

          Yusuf a haka Allah ya kai shi gida Lafiya yana faka motar bai fito ba ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana kuka sosai ba kad’an na, in ya tuna abinda Ameena tace sai yaji zuciyar sa na rawa sosai kansa yana sarawa jijiyiyon kan suna harbawa kamar zasu tsinke. Fitowa yayi daga motar yana dafe da kansa yana jin kan na juyawa sosai sai ya tsaya na wani lokaci sai kuma ya cigaba da tafiya zuwa cikin gidan.

Kamar ko yaushe Ammah ce kawai sai y’ay’an Abie da suka zo tana ganin sa ta bishi da kallo tace, “Yusuf Lafiya?.” A gaban ta ya  zube ya d’ora kansa a kan guiwar k’afar ta yayi shiru baice komai ba. Duk yaran suka bishi da kallo d’aya daga cikin yaran yace, “Ammah Daddy bashi da lafiya?.” Bata amsa ba ta d’ora hannun ta a kansa taji zafi sosai tace, “Yusuf yanzu baza ka sakawa zuciyar ka salama ba? Baza ka karb’i kaddarar da tazo maka ba?, Baza ka yi hak’uri ka karb’i jarabawa hannu biyu ba dan Allah?. Ameana in rabon kace zaka sake samun ta in ba rabo bace ba baza ka mallake ta ba sai dai kayi hak’uri rabon zaman ku ya k’are . Wannan damuwar da kake ciwo zata saka maka wallahi in ka kwanta ciwo kuma kanka ka cuta ba wani ba, Ameena tayi hak’urin zama da kai a baya a yanzu kuma bata son sake saka kanta a cikin abinda ta fita kwnakain baya ba, shiyasa ko ni bana son Ameena ta amince zata koma gidan ka Yusuf.”

Bai d’ago kan ba yace, “Ammah Ameena tace nayi hak’uri baza ta dawo ba, Ameena tace tana kallona matsayin mahaifin Zaitun ba wanda zata dawo gidan sa ba. Ammah meyasa takasa yarda na canja halaye na? Meyasa ta kasa amincewa da Yusuf din yanzu bana baya bane ba Ammah?.”
“Ko ni ban amince ba ai Yusuf, a yanzu baza ta amince ba daman saboda sai ta zauna dakai zata tabbatar ka canja, to in ta yarda ta sake zama dakai kuma kazo baka canja din ba?.”

Ba tare da ya d’ago ba yace, “Ammah na rasa da wanne baki zan muku jawabi Ammah, na rasa me zance muku ku fahimci na canja, na rasa da wanne yare zanyi bayani a fahimce ni, na sare na gaza bani da k’arfin guiwa. Wallahi Ammah akace Ameena zatayi aure ko tayi aure bana  jin zan sake kwana d’aya a duniyar nan.” Shiru Ammah tayi tana jin d’umin hawayen sa na shiga jikin taya sake cewa, “tace bata sona Ammah bata qaunar ganina.” 

Ammah tace, “sai kayi hak’uri kai ta addu’a, watakila rabon zaman ku ya k’are Yusuf, duk yadda ka kai ga son hakan bazai kasance ba in Allah bai yi ba.” Shiru baice komai ba a lokacin Ammah ma tayi shiru bata ce komai ba ana haka sai ga Abbah ya shigo da Mubakar a bayan da ganin yadda Yusuf yake sai yayi murmushi ya zauna yace, “Bashi da lafiya?.” Ammah kamar tayi kuka tace, “to gashi dai kamar mai Lafiyar kamar mara ita.” Ammah ta dafa kansa tace, “Kansa ciwo yake yi sosai gashi yayi zafi” ta d’ago fuskar sa sai taga idanun sa a rufe suke sai fuskar tayi ja sosai.

Abbah ya sauke numfashi yana kallon sa yace, “Yusuf ni ban san meyasa ka dawo da Ameena cikin ranka ba wallahi, a yanzu kai kasan tayi maka nisa to meye na damuwa kuma? Tun farko ai na fad’a maka ka daina zuwa inda take amma ka k’i yanzu gashi nan kana cutuwar da kanka a banza a wofi. Waye yace ka sake ta a baya? Waye yace kayi mata abinda kayi mata?. Da kana sonta ka kasa dawo da ita tun baya sai yanzu?.”
“Abbah tun a da tana raina babu inda taje ba dawo da ita nayi ba” sai ya dafe kansa yace, “kaina ciwo yake min sosai.” Mubakar yace, “Sannu, ai dole kai yayi ciwo.” Ammah tace, “ko asibiti zamu je ne?.”
“A’a yasha magani zai dawo daidai in sha Allah” ya fad’a yana kallon Ammah din.

Ammah ta sauke numfashi tace, “Mubakar kuje yasha maganin ya samu ya kwanta.” Yusuf yace, “a barni a nan.” Duk suka yi shiru ana kallon sa gabad’ayan su yanzu tausayi yake basu amma basu da abinda zai iya dan Abbah yayi rantsuwa babu shi a lamarin Ameena in tayi ruwa rijiya in bata yi ba masai.

       Ameena tana shiga d’aki ta tsaya a jikin k’ofar a ta goge idanun ta tana son kawar da damuwar da take ji a ranta duk tana jiyo maganar su wayar ta tayi k’ara ganin lamba ya saka ta share aka sake kira sai ta d’auka taji ance, “Hajiya Ameena.” Jin muryar Fiddausi sai tayi murmushi tace, “Fidy ya kike?.”
“Lafiya lau, ya su Yayan suna Lafiya?.”
“Qalau suke, wannan number fa?.”
“Ta mama ce.” Ameena tace, “oh.” Jin hakan sai Fidy tace, “akwai abinda yake damun ki ne?.” Ameena ta suka numfashi tace, “babu abinda yake damuna, me kika ji?.”

“Ga maganar ki nan ta canja. Ko maganar Yusuf din ce?.” Ameena tace, “Itace Fidy, ni nace bana son komawa gidan sa na fad’a masa fuska da fuska amma yak’i ya hak’ura.” Fidy tace, “yo meye na damuwa dan yak’i ya hak’ura Ameena?.”
“Ni ba damuwa nayi ba, kawai bana so ya dinga zuwa gidan yana ta min magiya akan abinda bazan iya ba.” Fiddausi tace, “Ameena dan kin k’i ne amma nidai nace miki ina sonki komawa wajan Yusuf, amma kince ke kad’ai kika San abinda kika ji a gidan sa nasan hakan amma wani jin dad’in yana zuwa ne a lokacin da ka fara shan wahala a rayuwa. Sannan wani kuskuren baka sanin ka aikata shi sai bayan kayi wani kuskuren kake lura ashe wancan ma kuskure ne, sannan wani tuban ko nace wani gidan tsohon mijin  in ka koma wallahi ya kan zama fiye da zaman farko farin ciki. Ana cewa kome mu k’ark’are inji Hausawa, eh haka ne akwai halin da tabbas yana nan amma wallahi irin su Yusuf da suke ganin kin kusa kubce musu kuma sukayi nadamar da suke zubar da hawaye baza su saka maimaita kuskuren baya ba.”

“Ameena ita nadama a bayyane take, kamar yadda ni babu lallai a amince nayi nadama amma ni a zuciyata nasan nayi bazan sake kuskuren baya ba to haka a wajan Yusuf din ma. Misali ko rantsuwa nawa zaki iya Ibrahim kice na canja babu lallai ya amince, saboda gani yake ban canja din ba amma ni nasan a zuciyata na canja domin naga izina da isharar da dole ma na canja din ko bana so. Haka nake ganina tare da Yusuf wallahi.”

Ameena tace, “Yanzu kina fad’a min ne dan na koma?.”
“A’a, ni ba ina fad’a miki dan ki koma bane, kawai Allah ya sani ni bama so da karancin shekarun ki ace kin auri mazaje guda biyu Ameena, ni kad’ai nasan d’acin hakan da nake ji a zuciyata duk da k’addara ce. Bana so ace Zaytun ta tashi ba a tsakanin ku ba hakan babu dad’i, duk da nasan wanda zaki aura zai rik’e yta hannu biyu amma ba kamar mahaifin ya ba. Ki kalle ni nida Amir, ya samu Uwar da ta fini iya kula dashi amma Amir bai shak’u dani ba, kallona yake kamar wata wacce ya sani a lokacin baya amma yanzu Ruky itace babar sa, ko bance na kin san zanji babu dad’i matsayina na uwa a gare shi.”

“Wallahi ni a wajena nafi so ki koma wajan Yusuf da dai ki sake aure gwara ace kin koma can kin san halin sa yasan halin ki kowa sai yaci maganin zama da d’an uwan sa.  Meye amfanin raba yara kowa baban sa daban a shekarun ki Ameena? Da kin shiga sabon gidan da kin haihu shikenan wancan baban ta daban wanda kika haifa ma baban sa daban. Nidai a nawa ra’ayin gwara ki koma wajan Yusuf.”

Ameena ta sauke numfashi tace, “Yanzu kema zaki iya komawa Ibrahim kenan?.” Fiddausi tayi murmushi tace, “ai ni nayi kuskure ba shi ne yayi kuskure ba, wallahi inda shine yayi kuskure irin na Yusuf ya dawo yace zai mayar dani irin yadda Yusuf yake yi a yanzu zan koma Ameena a guje ma kuwa. Amma ni nice nayi kuskure Ameena, sai dai in nice zan nemi ya mayar dani amma wallahi shi bazai zo yace zai mayar dani ba Ameeba saboda ya barni har abada, wannan shine banbancin.”

Ameena tace, “Meyasa kika rantse? Ni ina yi miki sha’awar komawa wajan sa duk da akwai Rukayya amma tana da sauk’in kai zaku iya zaman ku Lafiya ba tare da tashin hankali ba. Kin gane kuskuren k in yi nadama na tabbatar baza ki sake ba meye in kin koma? Yanzu kike zancen Zaytun ta taso a tsakanina da Yusuf ke meyasa bakya fatan Amir ya taso a haka?.” Tayi murmushi tace, “ki daina zancen komawa ta wajan Ibrahim wannan ba abu bane mai yuwa Ameena. Yanzu kika ce nayi nadama kuma kin san na gane kuskurena zan iya komawa wajan sa ko?.”
“Eh mana ai nadamar ki a bayyane take ai.” 
“Shi kuma nadamar Yusuf a b’oye take?, indai har kina ganin na cancanci a yafe min na koma gidan Ibrahim to shi Yusuf wacce irin cancanta ce baiyi ba?.”
Chapter 75 · 0% Book details