Sashe 30
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har ya dawo bata idar da sallah ba sallah take tayi kamar baza ta tsaya ba ya zauna yana kallon gidan sosai ya masa kyau kamar ba mallakin sa ba. Har mamaki yake wai wannan gidan mai kyau da tsari mallakin sane shi Ibrahim, abun yana masa dad’i sosai dan shi kansa yasan abubuwa da yawa sun canja a rayuwar sa. A lokacin ta idar zata tashi daga inda take yace, “kar ki taso, bara nazo muyi wata sallar.” Ta koma ta zauna ya taso sukayi sallar kamar ko wacce amarya da ango.
Bayan sun idar ya kalle ta yace, “Kici abincin ko?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “bacci nake ji.”
“Zaki iya ci ai sannan ki yi bacci.” Ta sake girgiza kai yace, “meyasa?.”
“Dare yayi in naci na kwanta zan ji kamar zanyi amai.”
“In kika ci ba sai ki k’i kwanciyar ba.” Ta d’ago ido ta kalle shi tace, “to me zanyi?.”
Ya d’an bud’e idanun sa yace, “kina so kusan abinda zakiyi?, kina so kice ma baki sani ba? Lallai ma to na fad’a miki?.” D’auke idanun ta tayi bata bashi amsa ba ya tashi yace, “sai kinci abinci ba’a kwanciya da yunwa a gidana.” Abincin ya bud’e mata a roba irin ta wajan biki fara harda cokalin roba a kai alamun siyowa akayi daga wani wajan abincin yace, “ki d’auka kici ko kuma na zauna na baki da kaina.”
_na shiga uku, wai wannan mutumin daman haka yake? Ni duk ya takura ni wallahi._ abinda take fad’a a zuciyar ta kenan sai taga ya zauna kusa da ita ya bud’e robar cikin nutsuwa kamar ko yaushe yace, “rashin cin abinci bazai hana abinda yake zuciyar ki, cin abincin ma bazai hana ba. Tunda kin san da hakan kin san kuma sai ya faru meyasa baza ki ci ba kawai ki huta? Rashin ci ai ba mafita bane ba.” Ya fad’a yana bud’e robar ba tare da ya kalle ta ba.
Gaban ta fad’uwa yake sosai ta kalli abincin bata fara ci ba sannan bata motsa ba yace, “kici abinci.” Hannayen ta ta fito dasu daga cikin mayafin ya kalli hannyen ta farare marasa kauri sosai tasha kunshi gaba da baya yayi mata kyau sosai a hannun kamar an d’ora shi a kai. Hannun ta rik’e ya bud’e tafin hannun ta yana sake kallon zanen kunshin yace, “yau na rik’e hannun matata Rakiya.” Yana d’ago ido suka had’a ido da ita sai ya kawar da kai yayi dariya yace, “ko na tab’a rik’ewa ne ake kallona?.”sai yayi murmushi dan yasan baza ta bashi amsa ba tace, “kina son kallon mijin ki amma ban San meyasa da Mun had’a ido sai ki kawar da fuska ba.”
Abincin ya d’iba a cokali ya kai bakin ta amma bata karb’a ba yace, “na gane, bakya cin shinkafa kin fi son kazar ki ko?.” Da sauri ta kalle shi sai taga ya d’aga mata gira sai ta saka kawar da kai zuciyar ya bugawa take tana so ya fahimci halin da take ciki amma bazai yu ba ya sake da ita sosai baya jin wani nauyin ta ko kunya kamar sun shekara haka yake mata magana baya jin komai ita kuma ba haka yake ji ba. Sai kuwa ya tashi ya d’auko wata ledar ya ajjiye mata yace, “to gata ai sai ki ci.”
Babu abinda take tunawa sai lokacin da aka kai Fiddausi gidan sa itace kan gaba wajan Karb’ar kudi a hannun abokan sa na siyan baki, suna ta yiwa Fiddausi rad’a ana dariya suna ce mata sai sunzo jinya ana tayi mata tsokana irin ta k’awaye balle ita aka fara aurarwa a cikin su. Tunanin ya dabaibaiye zuciyar ta ta kasa kawar dashi. a wannan lokacin shiyasa ta kasa sukuni kwata-kwata.
“Rukayya tunanin me kike?.” Ta kalle shi ta girgiza kai alamun babu yayi murmushi yace, “Kici abinci ki bar wannan tunanin babu abinda zai miki.” Haka kuwa akayi ta d’an ci abincin kad’an tace, “ya ishe ni.” Baice komai ba ya rufe baya son takura mata dan bata sake dashi har lokacin, tana so ta tambaye shi bazai ci ba amma kuma ta kasa dole tayi shiru.
Ya tashi tsaye ya saka hannu ya d’ago ta gabad’aya ta tashi itama yace, “muje ki kwanta inda gaske kike baccin zaki yi.” Sai a lokacin taje inda dakuna suke taga guda biyu ne d’aya yana kallon d’aya ya bud’e na hannun haggu taga gado ne babba a ciki an gyara shi tsaf yayi kyau sai khamshi yake yi. Gidan amarya daban yake dan kana kallon gidsn Rukayya kasan na amarya ne komai daidai da ita.
Ya tsaya daga gefe yace, “ina zuwa.” Ganin ya fita ya saka ta kallon d’an sosai a nan fa fahimci shi Zuhra yake fad’a mata ta ajjiye mata kayan ta a ciki ta tashi ta shiga band’aki ta fito ta canja kaya har lokacin bai dawo ba ta kashe hasken d’akin ta kwanta.
Shima yana sane ya kyale ta dan ta sake sosai tayi abinda take so sai bayan ta kwanta taji an bud’e k’ofar an shigo, tayi kamar bacci ya d’auke ta shi kuwa yasan ba bacci take yi ba amma bai nuna mata ba ya fita ya kyale ta dan ta samu tayi baccin sosai in tayi baccin ya shiga ya kwanta.
Bayan kwana biyu.
Ameena na zaune a gaban Yaya Adam yana kallon ta yace, “Yauwa daman kiran ki nayi akan kar na sake ganin kina tuk’a mota da kanki. Ko makarantar zan samar miki mai kai ki amma ban yarda ki sake fita da kanki ba kin gane?.”Ameena ta girgiza kai yace, “in ba fita ta gaggawa ba ban amince da ki dinga driving ba sai in Kinyi aure. Ba kuma saboda wani abun ba kawai haka tsarina yake.”
Ameena tace, “in sha Allah Yaya.”
“Ya batun makarantar? Komai yana tafiya daidai ko?.”
“Sosai ma Yaya, naji dad’in makarantar duk da daga level two na fara amma bana jin wahalar karatun gaskiya, sai dai math ne bana ganewa.” Yayi dariya yace, “Nima ba iyawa nayi ba balle na dinga koya miki, sai dai ko Al’ameen in wani abun ya shige miki duhu ki tambaye shi ya iya lissafi fiye da tunanin ki.”
“Ai kuwa zan tambaya, dakyar nake iyawa in an koya mana.”
“To yayi kyau, Allah ya bada nasara.”
“Amin Yaya, na gode.”
“An kawo min iv na bikin gidan su Yusuf, zaki je amma dai ko?.”
Ameena tayi shiru kamar baza tayi magana ba kafin tace, “eh zanje.” Yaya yace, “ya dai kamata kije din, suna sonki sosai gwara kije in baki je ba baza su ji dad’i ba.” Ameena tayi murmushi yace, “tashi kije Allah ya taimaka mana.” Ta tashi ya shiga d’aki a lokacin wayar Humaira ta shigo.
Tana d’auka Humaira tace, “Sis ranar alhamis za’a fara fa.” Ameena tayi murmushi tace, “Humaira babu lallai nazo duka gaskiya, nafi daman tunanin zuwa kamu kawai ranar juma’a.”
“Ai da Ammah bata ji dadi ba kuwa, iya kamu banda dinner banda yini? Haba Sis yanzu a bikin nawa?.”
Ameena tace, “kiyi hak’uri ba da wani abun nace bazan zo ba.”
“To dan meye? Dan Alalh kizo kawai ayi shagali dake.”
“To naji zan zo.”
Humaira tayi dariya tace, “Ko Kefa, har naji dad’i wallahi. Zan shigo gobe ai in sha Allah.” Ameena ta amsa mata kafin sukayi sallama. Ajiyar zuciya tayi bayan ta kashe wayar tana kallon wayar tace, “taya zan iya zuwa gidan ku Humaira?, bazan iya sakewa ba musamman akan…..” Sai kuma tayi murmushi ganin kiran Rukayya yana shigowa ta d’auka ta saka a kunne tace, “Amaryar Ibrahim kin sha khamshi daga waja ma jin khamshi nake.”
Rukayya tayi dariya tace, “fadi ki sake fad’a amaryar ce ta gaske ba ta wasa ba.” Ameena tace, “Allah? Lallai Ruky baki ya bud’e.” Tayi dariya tace, “har yanzu baki dawo ba ko?.”
“Bari akwai Ruky makaranta ta sako ni gaba, so nake na nutsu nayi karatuna da kyau wallahi.” Rukayya tace, “ya labarin Fiddausi kuwa?.”
“Har yanzu babu labari wallahi, ni abun tsoro yake bani fa wallahi.”
“Nima haka wallahi, Allah yasa ba wani abun ne ya same ta ba.”
“Amin dai. Ya amarci?.”
Rukayya tace, “ban sani ba.” Ameena tayi dariya sannan Ruky tace, “kin san da muka je gidan su yadda Hajiyan sa tayi min inda kika san ta goya ni, Gashi daman nayi girki na tafi dash ke baki ji saka albarka ba. Ai naji dadi dana samu iyayen miji masu qaunata kamar ke da Ammah.” Ameena tace, “ke samun dangin miji masu sonka yana da dadi sosai wallahi, yana daga cikin abinda ya saka nake juriya a zamana da Yusuf. Wani abun badan shi nake yi ba dan iyayen sa nake yi.”
“Ai yanzu na gane wallahi, inda kika san yadda Ammah take miki haka Hajiya take min. Komai ta samu aiko min dashi su albasa, kuka, daddawa, kub’ewa harda kayan Miya komai a bani.”
“Ke ai ta ko ina auren nan alkhairi ne a wajan ki wallahi.”
“Na gani Ameena, duk da akan ce amarya bata gane halin mijin ta amma juma’ar da zatayi kyau tun daga laraba ake gane ta. Wallahi Ameena bani da abinda zan cewa Allah sai gode, jinkiri kuwa ya zamar min alkhairi.”
Ameena tace, “Ana ta soyayya, Allah yasa baki da ciki soyayyar sai tafi armashi.” Rukayya tayi dariya tace, “ku wallahi baku da kunya, haka Zakiyya ma da tazo ke baki ji magana ba.” Ameena tayi dariya tace, “banza, ke ai itace dake
“Ameena kinga yadda Zakiyya ma ta koma kuwa? Tunanin mijin ta bai san da cikin ba ya d’auka ta zubar baban tashin hankalin ta kar ya sani yace ya sake ta ya zatayi.”
Ameena tace, “mu dai Mun shiga uku, daga wannan sai wannan?. In wannan ta fita daga matsala sai wannan ta shiga, nida ke mu fita ita da Fiddausi sun shiga. Allah ya kawo mafita kamar yadda ya baki mafita nima ya bani.” Ta amsa da amin kafin tace, “bikin Humairan Ammah za’a yi fa.”
“Amma dai zaki je?.”
“Tunanin da nake yi kenan Ruky.”