Sashe 82
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Humaira tayi dariya Ameena ma murmushi take ta k’arasa wajan Abbah ta gaishe shi ta gaishe da Ammah ma suka amsa da farin ciki sosai a zuciyar ta, Ameena ta gaishe su dukka suka amsa Yayan Abuja tace, “ki zauna mana kamar sabuwa a cikin mu.” Tayi dariya ta zauna a kan carpet tana kallon Humaira da take ta d’aga mata gira sai take bata dariya. Ammah share hawaye take farin ciki da murnar dawowar Ameena cikin su ya cika mata zuciya sosai dan hakan ya bayyana a tare da ita. Ta kasa sarrafa farin cikin bata hakan ya saka ta zubar da hawaye.
Abbah ya kalli Yusuf da yake zaune sai murmushi yake yi suna had’a ido da Abbah sai ya sha jinin jikin sa ya d’an murmusa Abbah yace, “to Yusuf ga Ameena nan a karo na biyu, zamu gani ko nadamar har zuciya take ko kuma a iya fatar baki ta tsaya. Abinda nake so ka sani kamar abinda babar ka tace ka sake ka wulakanta Ameena nima nace Allah ya isa.” Murmushi yake yi dan shi dai yasan hakan baza ta faru ba balle Allah ya isa iya aiki a kansa yace, “Abbah wancan Yusuf in ya mutu wannan sabo ne a gaban ku a zaune zai baku mamaki in sha Allah.”
Ita dai Ameena murmushi take yi har ga Allah tana son iyalan gidan saboda son da suke nuna mata da zuciya d’aya dukkan su babu wanda yake k’i ta kowa burin sa yaga tana farin ciki. İn ba tsantsar soyayya ba ina mahaifi ina yiwa d’an sa alqawarin Allah ya isa in bai kyautata mata ba?. Abie yace, “Allah ya baku zaman Lafiya ya kawar da idanun mak’iya daga kan ku.” Aka amsa da amin Mubakar yace, “Allah kar ya sake kawo irin su b’eriya.” Humaira tayi dariya kowa ma yayi dariya Ammah tace, “A ina zaku zauna yanzu?, naga tsohon gidan naku ba’a gyara ba.” Yusuf yace, “sabon gida.” Abbah yace, “wanda ka siya wai shekaran jiyan?.” Ya d’aga kai alamun eh Yyan Abuja tace, “har ka gama zuba komai kenan?.” Nan ma ya d’aga kai alamun eh tace, “lallai yaron nan kana abinda kake so.” Yayi murmushi kawai Ammah tace, “Ameena zo kiji” ta fad’a tana rik’e hannun ta suka shiga ciki.
Abbah ma nasiha yayi masa sosai da kuma jan hankali akan abubuwan da suka wuce ya sake d’aukar alqawari akan bazai sake faruwa ba. Ba jimawa sosai Ammah da Ameena suka fito suka tafi zuwa sabon gidan da yake kusa dasu Ammah dan daga gidan Ammah ana hango shi ba kamar wancan ba ya shiga da motar har cikin gidan.
#mai daki
#Book3
#Nana Haleema
Book3
041
Babban gida ne sosai dan yafi wanda suk zauna a baya kyau da k’eruwa da girma yafi na baya sosai ba kad’an ba. Ameena kallon gidan tayi komai fari tun daga waje hatta k’ofa da gate farare. Kallon ta yayi bayan ya kashe motar kansa ciwo yake sosai amma baya son nunawa kar taga gazawar sa tun ba’-a je ko ina ba yace, “mu shiga ko?.” Bata kalle shi ba ta sakko daga motar shi kuma ya fito shida Zaytun suka shiga cikin gidan.
A falon ta zauna tana kallon falon komai sabo ne a ciki yayi kyau sosai ya tsaru kamar ba a cikin k’aramın lokaci akayi komai ba. Ganin ta zauna shima sai ya zauna Zaytun na kusa dashi ta kalle ta taga babu wayar ta a hannun ta sai ta ganta a hannun sa sai ta share bata ce komai ba. Magana yake so yayi mata amma ya kasa dan tsoron ta yake ji tun da akayi maganar auren babu abinda ya had’a su shiyasa ya rasa da abin zai fara.
Kafin yayi tunani yaga ta tashi tace, “ina ne mazauni na?.” Sai shima ya Mike yace, “ina ne mazaunan mu dai ko?.” Kallon k’asan idanu akayi masa tace, “ban tambayi naka ba ai nawa na tambaya, yana ina?.” Yayi Murmushin k’arfin hali yace, “muje na raka ki.” Yayi gaba tana bayan sa ita da Zaytun suka hau sama suka shiga wani falon yayi gaba tace, “ka dakata ma, naga inda zan zauna” ta fad’a tana bud’e wani d’aki tana kallon sa dan yayi kyau sosai gashi kuma mai girma.
Shiga ciki tayi shima sai ya biyo bayan ta ta cire mayafin ta ajjiye a kan gadon tana kallon Zaytun tace, “zo ki cire kayan nan kar su dame ki.” Zaytun ta maqale kafad’a tace, “wajan Daddy.”
“Sai kin dawo” ta fad’a ba tare da ta kalle shi ba fuskar ta ba yabo babu fallasa. Yayi murmushi ya shigo ya zauna a daf da ita baice komai ba bata ce komai ba, ya ciro wayar ta daga aljihu ya bata ta karb’a ta bud’e tana dannawa.
Ya kasa magana sai kallon ta kawai da yake yi amma ya kasa furta ko wacce kalma daga bakin sa, itama kuma ko zasu kai shekara a wajan baza tayi magana ba. suna zaune shiru a haka sai yaji tace, “idan baka da abin fad’a kwanciya nake so nayi.” Ya kalle ta yace, “nima kwanciyar zanyi a nan ne masauki na.” Sai ta kalle shi tace, “ayya ai ban sani ba, sai na canja d’aki” ta fad’a tana niyar tashi ya rik’e hannun ta t dawo ta zauna yace, “ina nufin duk inda ya kasance masaukin ki nan ne masauki na.” Bata ce komai ba ta sake kallon Zaytun da take jin bacci amma ta maqale a jikin sa ta girgiza kai kawai bata ce komai ba.
“Mtsw! Ko Kaya ma bani dasu” ta fad’a tana tashi ta shiga k’ofar da take gani wacce tasan band’aki ce.
Zaytun ya d’auke daga jikin sa ya cire mata rigar ya kwantar da ita a kan gadon ya zauna yayi shiru farin ciki ya cika masa zuciya amma kuma tsoro da shakkar magana da Ameena yafi damun sa. Fitowa tayi daga band’akin tayi alwala ta kalle shi tace, “zan kwanta.” Ya kalle ta yace, “bismillah.”K’arasowa tayi ta hau kan gadon ta zauna bata kwanta ba gabad’aya wani iri take ji a zuciyar ta kuma ta fahimci tsoron yi mata magana yake ita kuma haka take so dan bata shiryawa maganar ba a yanzu.
“Ameena!.” Sai kuma yayi shiru ta kalle shi bata amsa ba yana jiran k’arin bayani amma sai ya kasa yayi shiru na wani lokaci kafin ya sake cewa, “Ameena ki yi hak’uri, dan Allah ki manta da baya ki d’auki yanzu a matsayin sabuwar rayuwa.”
“To, nayi” abinda tace kenan ya kalle ta yadda take magana kamar yadda take yi gab da rabuwar auren su yayi murmushi yace, “na gode. Akwai abinda kike so? Zaki kwanta baki ci komai ba?.” Kai ta girgiza alamun babu yace, “in kin yi min alfarma ina so zan kwanta a gefen ki.”
Wajan ta nuna masa da hannu alamun gashi nan ta kwanta ta tare da ta sake cewa komai ba, ya sauke numfashi a hankali ya tashi ya kashe hasken d’akin ya kwanta Zaytun na tsakiyar su. Bacci take son yi amma ta kasa tunani ne yake zuwa zuciyar ta kala-kala shaid’an yana sake zuga ta akan share shi har sai ta wahalar dashi sannan in zasu gyara zaman nasu sa gyara daga baya. A haka bacci ya d’auke ta shi kam idanun sa biyu ciwon kai bazai barshi baccin ba.
Tashi zaune yayi bayan tayi bacci ya dafe kansa da hannayen sa gıda biyu ciwo suke masa sosai kamar zai raba gida biyu haka yake ji, ya kasa jurewa saboda azaba ga maganin sa yana cikin mota a k’asa ga dare yayi lokacin karfe d’aya na dare. Ameena tana jin motsin sa dan bata da nauyin bacci motsi akayi na kirki zata bud’e idanu ta jiyo sai ta ganshi a zaune yana juya kansa gashi ya dafe kan, tashi zaune tayi tana kallon sa tace, “Lafiya?.” Hannu d’aya ya mik’a mata ta taso ta rik’e hannun nasa sai ta wara ido jin tafin hannun nasa ma yayi zafi tace, “Subahanallahi, baka da lafiya?.” Kusa dashi tadawo da ita ta zauna ya kasa magana saboda ciwon kai tace, “kan ka ne yake ciwo? Ina maganin ka yake?.” Baice komai ba ya dai rike hannun ta gam gam tace, “ina maganin ka yake na d’auko kasha?.”
“Yana mota. Kar ki fita zai daina” ya fad’a dakyar tace, “taya zai daina baka sha magani ba? Ina key din motar na d’auko?.” Sake rik’e ta yayi yana girgiza kai alamun baza ta sauka ba tace, “zan iya zuwa” ta da da tana zame hannun ta daga nasa taga key din a gefen bedside ta d’auka ta fita daga d’akin ta sauka ta fita zuwa harabar gidan sai ayatul kursi take karantawa a zuciyar ta.
Baba mai gadin tsohon gidan tane ya bata tsoro ganin an hasko ta da fitili ta razana ganin itace sai ya k’araso yana tambayar lafiya. Bud’e motar tayi ta d’auko maganin a leda a baya ta kulle motar ta ta koma ciki ta d’auki ruwa a falon ta hau saman ta samu har ya samo daga kan gado ya dafe kansa ta k’araso tace, “ga maganin” ta fad’a tana bud’ewa tana gani duk daily dose ne ta ciro dukkan su tace, “karb’i kasha.” ya karb’a yasha din tana zaune a gefen sa sai ya kwantar da kansa a jikin ta tana jin yadda jijiyar kan yake bugawa sosai sai bata hana hakan ba.
Suna zaune a haka kusan mintina talatin kafin bacci ya d’auke shi ta kalle shi tana mamakin ciwon kai irin wannan ta kwantar dashi a gefe ta koma daya b’angaren ta kwnata itama. Tun karfe hud’u ta tashi shi kuwa bacci yake sosai ta wuce tayi alwala ta fito tana sallah kamar ko yaushe har akayi asuba tana so ta tashe shi yayi sallah amma kuma taga baccin yake sosai da alama ya samu saukin kan. K’arasowa tayi kawai tana yi masa magana amma bai motsa ba hakan ya bata tabbacin baccin yayi nisa dan bashi d a nauyin bacci shima.