Sashe 79
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameena tace, “Yaya a nutse nake kuma daman ko Yaya Al’ameen bai same ni ba hukunci na kenan a yanzu, na amince da hakan fatana Allah yasa silar canjin ne ya saka muka rabu.” Yaya Adam yace, “Amin ya Allah. Tunda kince haka shikenan, Amma kafin a ki koma sai na gindaya masa sharud’an da dole sai yabi, kinga dukan nan wallahi bazan d’auke shi ba.” Ta girgiza kai tace, “nima haka Yaya, duk abinda kaga daidai ne kayi.”
“Shikenan Ameena, Allah yasa alkhairi ne hakan a rayuwar ki.” Ta amsa da amin ya fita ita kuma ta kwanta da baya tana ji a ranta komai zai warware da ikon Allah, ita kuma Allah ya bawa lamarin tasan bazai barta ta sake kuka ba kamar wancan lokacin.
Bayan kwana biyu.
Yaya Adam ya samu mahaifin Yusuf da maganar abinda ya bashi mamaki bai amince da farko ba sai da ya tabbatar da Adam din ya amince sannan ya amince ya nuna farin cikin sa akan hakan sosai. Ammah da ta samu labari kuka ta dinga yi kukan soyayyar Ameena da tausayin ta da kuma shi kansa Yusuf din dan in tace bata ki dadi ba karya take yi. Amma duk da haka bata nuna ba har gida taje ta samu Ameena tana sake nusar da ita kar tayi kuskure fa a karo na biyu, Ameena tasan duk fad’a take kawai dan tayi mata kara amma ba wai har zuciya ba Ameena ta tabbatar mata da babu komai in sha Allah.
Kowa yasan labarin banda Yusuf da ya dawo gida yanzu ya samu sauki babu laifi. Babu wanda yayi masa maganar ana ta yi masa magani musamman addu’a ayar Allah ake bashi yana sha kuma yana damun sauki sosai. A Daren ranar laraba Yaya Adam ya kira Yusuf suka zo gidan shida Usman da ba kwari gare shi ba sai an rik’e shi wani lokacin ya same ai shida Al’ameen a zaune suka shiga suka gaisa sannan suka zauna ba tare da sun San dalilin kiran ba.
Yaya Adam yace, “daman abinda ya saka na kira ka ba wani abun bane, Yusuf na amince kayi nadama har nayi gangancin amincewa dakai a zuciyata, dan ganganci zance tunda ban tabbatar nadamar taka taje zuciya ba.” Yusuf ya d’ago muryar sa ta dashe sosai dakyar ake jin me yake cewa yace, “Allah yana ganin zuciyata, ni kuma bazan yi karya da Allah ba.” Yaya Adam yace, “haka ne Allah ya san komai, kuma in kayi karya da Allah kai kasan sauran ai.” Yusuf ya sunkuyar da kai gaban sa sai fad’uwa yake yi dan bai san dalilin kiran ba.
Adam yace, “na amince zan sake baka Ameena a karo na biyu” Yusuf ya d’aga da sauri ya kalle shi Yaya Adam yace, “amma ina da sharad’i, in Kaga zaka iya bi shikenan in baza ka iya ba kowa ya kama gaban sa.” Yusuf ya kalli Usman ya sake kallon Yaya Adam sai ya sake kallon Usman yace, “mafarki nake ko?.” Usman ya girgiza kai yace, “Gaskiya ne ba mafarki ba, ka saurare shi Kaji abinda zai ce maka.”
“Usman mafarki ne.”
“Ba mafarki bane! Ka tsaya kajiabinda za’a ce ka nutsu kaji abinda za’a ce maka!” Ya fad’a da tsawa yana kallon sa dan ya tabbatar gaske ne ba k’arya ba.
Sai kuwa Yusuf ya nutsu sosai ya kalli Yaya Adam da yake kallon sa Yaya Adam ya kalli Al’ameen ya sake kallon Yusuf yace, “ba mafarki kake ba da gaske ne, na amince da zaka gyara kuskuren ka darajar iyayen ka zan sake baka ita a karo na biyu.” Yusuf ya fara sauke Ajiyar zuciya duk da har lokacin bai tabbatar da gaske bane kawai gani yake kamar wasa ake masa Yaya Adam yace, “sharad’ina na farko Ameena zata cigaba da karatun ta tunda ta fara baza ta tsaya ba, na biyu kuma da wasa hannun ka ya sake zuwa jikin ta da niyar duka a ranar baza ta kwana a gidan ba, kai kuma kasan matuk’ar ta sake kubce maka baza ta saka dawowa hannun ka ba dan a yanzu kafi kowa sanin wahalar da ka sha kafin azo wannan gab’ar. Na uku kuma nasan yazo ranka a yanzu to ka d’auka shi nake nufi, wallahi bazan d’auka a sake wannan gangancin a karo na biyu ba, kai duk wani abun ma da kasan kana yi aka sake maimaitawa bazan d’aga maka k’afa ba.” Yusuf ya d’ago kai ya kalli Adam dan shi wallahi ji yake kamar a mafarki Al’ameen yayi murmushi yace, “bafa mafarki kake ba Yusuf da gaske ne abinda kake ji ba mafarki kake ba, ka amsa sharud’an da aka baka in zama iya shikenan.”
Yusuf ya rasa tantance ma a wanne yanayi yake ciki a wannan lokacinsaboda farin cikin da yake jin zuciyar sa a ciki ya kalli Usmsn yace, “ban San me zance ba Usman.” Usman yace, “amsawa zaka yi.” sai ya kasa magana ma dan ya gigice ya dafe kai yace, “ni yanzu sai an bani sharad’i ma Usman? Umarni kawai za’a bani kuma dole na tabbatar dashi.” Yaya Adam yace, “Akwai abinda in kaga baza ka iya ba zaka iya hak’ura da auren nata tunda ba dole bane.”
“Babu shi wallahi, in ma cewa kayi na zauna Ameena ta rama duk abinda nayi mata zan zauna balle wannan abubuwan da aji an fad’a. Sake samun ta shine burina dan haka kome akace min a shirye nake dana tabbatar dashi, bana fata ko burin tsallake wani abun koda ba’a fad’a min ba. Samun ta yafi min komai zan iya rasa duk abinda nake dashi indai zan same ta, na amince da koma meye na yarda da duk abinda akace koda zata dinga yankar naman jikina nata gasawa ne.” Yaya Adam ganin ya fara hawaye sai yace, “To tunda ka amince shikenan, amma zan sake jaddada maka, wallahi aka sake samun kuskure bazan kyale ka.”
“Duk abinda kaga ya dace a lokacin kayi min, in sakawa zakayi a dauki raina a lokaci na amince wallahi na yarda da koma meye.”
Adam yace, “shikenan, akwai tafiyar da zanyi ranar Monday dan haka jibi juma’a nake so a mayar da auren ka da ita kafin litinin amanar ta ta dawo hannun ka. Amma ina so kayi min alqawarin da kasa zaka cika ba irin wanda kayiwa mahaifin ta ka kasa cikawa ba.” Sai ganin Yusuf sukayi ya zube yana sujjadar godiya ga Allah, ya jima a haka kafin ya d’ago ya kalli Yaya Adam yace, “Nayi alqawari canjawa daga wancan Yusuf din zuwa wani sabo daban, nayi alqawarin bata farin cikin da ban bata a wancan Zaman ba, nayi alqawarin zamu zauna lafiya babu cuta babu cutarwa. Komai ma nayi alqawari wallahi ni zanyi koma me akace, in ma wani abun take so wanda zan yi ga bata nishad’i kawai zanyi.” Adam yayi dariya dan ya fahimci baya cikin ma hayyacin sa farin ciki yayi masa yawan da ya kasa sarrafa farin cikin sa.
Al’ameen yayi dariya shima dan yadda ya rud’e din abin darıya ne, “shikenan mu kuma munyi alqawarin saka baka Ameena a karo na biyu, kaje ka shirya jibi Ameena matar kace in sha Allah.”
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500
Book3
040
Yusuf ya gigice saboda murna hankalin sa yana neman yin balaguro daga jikin sa tsabar tsantsar farin cikin da yake ciki a wannan lokacin ya kalli Usman ya saka kallon Al’ameen da yayi magana a k’arshe yace, “ni fa ban gane ba, yanzu kenan Ameena zata sake zama mallarına a karo na biyu?.” Al’ameen yayi murmushi yace, “da gaske ne mana Yusuf.”
Sai ya kasa magana ya rasa abinda zaice ganin hakan sai Adam yace, “ba sai kace komai ba kaje kawai jibi in Alalh ya kaimu za’a mayar da auren ku zuwa litinin zan tafi cross river bana son tafiya na barta a nan shiyasa nake so kafin ranar ta koma gidan ka.” Godiya yake so yayi amma sak ya kasa sai kallo da yake yi ya rasa ma abinda zaice saboda farin cikin da yake ji a cikin zuciyar sa ya hana bakin sa furta komai.
Dakyar ya iya cewa, “na gode, na gode Allah ya saka maka da gidan Aljanna.” Adam yace, “amin, amma bani zaka yiwa godiya ba ga wanda zaka yiwa godiya nan, shine zai auri Ameena amma yace kayi nadama ya sake bar maka ita a wannan lokacin. Abokina ne, kuma aminina sannan kuma yayan Ameena ne. Koda bana nan shine idona yadda zan d’aga maka akan b’atawa Ameena wallahi shi bazai d’aga maka k’afa ba. İn kayi hankali kanka, in baka yi bama kanka.” Yusuf ya kalli Al’ameen da yake kallon sa yana murmushi ya rasa maganar ma da zaiyi Al’ameen yace, “basai kace komai ba farin ciki ya hanaka magana, abinda nake so dakai yadda kaji wannan farin cikin a zuciyar ka ka ninkawa Ameena shi a cikin rayuwar ta gabad’aya har abada. Kar ka barta tayi kuka, kar ka barta da damuwa, kar ka Bari tayi maraicin iyaye, kar ka bari tayi kukan nisa da d’an uwanta, hakan akwai zakayi ka nuna mana kayi farin ciki ka kuma gode da karamcin da akayi maka, amma godiya ta fatar baki bana son ta, ka nuna mana ka gode ta hanyar rik’e mana k’anwa hannu biyu kar ayi sakin da akayi a baya.”
Kai yake girgizawa kawai kamar k’adangare amma ya kasa magana sai Usman ne kawai yake magana amma shi ya kasa. Ganin haka sai Adam ya kalli Usman yace, “kaine kake da nutsuwa a yanzu, kana ji jibi za’a mayar da auren saboda tafiyar da zanyi Al’ameen ma zai je Lagos a Monday din. To duk wani abu a tanade shi kafin ranar Monday dan bazan barta ta kwana a nan ita kad’ai ba shiyasa za’a yi auren a huta.” Usman yace, “in sha Allah Yaya. Alalh ya jikan iyaye yasa suna aljanna amin.”