← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 93

Sashe 17

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya tace, “ku bani Umma zan gyara.”
“Ai ko kin gyara baza ki daina wannan warin ba, wanna gashin da kika ajjiye a hammatar ki ko shi kad’ai ya isa ya saka ki wari, hammata a cike haka kamar kan taro ina gakuma na k’asa.” Asiya tace, “yanzu zanje nayi wanka sai na cire shi, ni wahala yake min ne shiyasa nake barin kayana ai shima ado ne.” Umma Sakina ta tab’e baki tace, “gashi nan, in kin gyara anyi abinda ake so kanki, in baki gyara bama kanki ke zaki cutu ki dawo gida da zaman zawarci.”

Asiya ta karba tace, “Yanzu zanje nasha, Umma Sakina na meye shi?.”
“Daman gaddamar da yake miki ne da Babar ki ta fad’a min na nemo naki mafita, amma naga alama babu aikin da zaiyi miki wallahi yanzu da naga yanayin ki. Haba nidai ina mamaki wallahi, in aka ce min wai yana k’aurace miki ko kuma yana miki tsaya, dan ni nasan abubuwan da nake baki ba na wasa bane, a cikin abubuwan da nake baki Wallahi akwai wanda ko kara kika ajjiye bai isa ya tsallake ba, amma sai naga babu wani cigaba ashe Matsalar daga wajan ki take.”

Asiya tace, “Zan gyara ai” ta sake tofa yawu a bayan kujera Maimuna tace, “tabdijam, Yusuf yana k’ok’ari wallahi, Umma ni kam zuciya ta tashi take yi nayi waje in kin gama mu had’e na cigaba da zama amai zanyi” ta fad’a tana tashi ta fita Umma tace, “nima bazan iya zama ba ai, Ke sai anjima” ta fad’a tana tashi ta fita ba tare da ta sake kallon Asiya ba.

Asiya ko a jikin ta dan ita bata ga k’azantar da ake fad’a tana da ita ba, a ganin ta tana tsafta daidai gwargwado wanka ne daman tasan wannan sai taga damar yi shima ba k’azanta bane ba ai tattalin ruwa ne. Ta tashi ta hau sama ko wankan bata yi ba ta fesa turare ta saka kaya ta sauko k’asa ta sha maganin ta nufi b’angaren Ameena. Tana shiga falon sai da ta lumshe ido taja numfashi tace, “Wai aljanu ne suke yiwa b’angaren nan turare oho.” Saman ta hau nan ma yana nan tas dashi sai dai k’ura kawai amma d’ankwali babu ta wuce falon ta hau saman da zata je d’akin sa.

Tana shiga ta hange shi a zaune da kofi a hannun sa yana shan abu a ciki duk a tunanin ta lemo ne tana zuwa taga babar kwalba a kusa dashi ta kalli kwalbar ta kalle shi taga idanun sa sunyi ja sosai sai lumshe su yake yi, d’aukar kwalbar ta duba jiki ta wara ido ta ajjiye tace, “Giya kake sha?.” Sai a nan yaji muryar ta dan bai ma San tazo ba ya bud’e ido yana kallon ta ya mik’e tsaye yace, “ke ni zaki yiwa abinda kika yi ko?” Ya fad’a yana nuna kansa da yatsa.

“Yusuf daman kai d’an giya ne ban sani ba?.” Cikin muryar maye yace, “keee ni kike cewa dan giya d’an Uwar ki?” Ya fad’a yana tsinke ta da mari. Tayi baya tana kallon sa da mamaki ya saka hannu a gefen sa ya d’auki belt ya nad’a hannun sa yace, “ba kince in na dake ki sai kin rama ba?, bani kika yiwa rashin kunya ba?, To rama na gani” yana fad’a ya fara dukan ta da belt d’in tana ihu tana yin baya yana saka binta ta rasa abinda zatayi sai ihu da take yi dan dukan na shigar ta sosai, a haka ta k’arasa ga k’ofa ta fita a guje tana kuka dan ta daku.

#Mai daki
#Book 3
#Paid
#500
#Nana Haleema

Book3
011

A gidan su Ameena ta ware kamar ba ita ba harkokin ta kawai take yi bata tunawa ma da Yusuf sam rayuwa take cikin farin ciki a a gidan Yayan ta mai son ta. Hakan ya yiwa Yaya Adam dad’i ganin ta saki jikin ta ta manta da rayuwar baya ta karb’i rayuwar da tazo mata ta zaman tunani, ko kad’aice kanta bata yi sai dai ka ganta tana danna waya ko tana wayar tana darıya nishad’i.

Tana zaune a dak’i suna waya ita da Humaira sai dariya take yi tace, “Kice bikin naki dai yazo, wata uku ai kamar yau ne.” Daga can b’angaren tace, “Eh wallahi, ni naji dad’i ma da aka kai shi wata uku.”
“Meyasa?.”
“Lokacin kin fita daga idda kizo a sha shagali, dan wallahi sai kin zo.”

Ameena tayi dariya tace, “Lallai ma Humaira, Umarni kike bani?.” Humaira tace, “shi nake baki, ai kema kin san Ammah baza ta yarda kice baza ki ba ko?.” Ameena tace, “nima ai bance miki bazan zo ba, me zai hana ni zuwa? In kinga ban zo ba sai rashin lafiya.”
Humaira tace, “Yauwa ni daman nasan ni ta musamman ce.” Tayi dariya Humaira tace, “Zan zo ma na d’auki Zaytun tayi min Hutu.”

Ameena tace, “Sai kinzo, kizo kafin ta shiga makaranta dan first term ma nake so mu shiga wallahi na saka ta a makaranta surutun ta yayi yawa gwara ta fara karatu.” Humaira tace, “Kinji wai ki saka ta a makaranta, Yaya Yusuf dai ya saka ta a makaranta ke meye naki?.” Ameena tayi murmushi tace, “nice zan sakata mana, in aka biye tashi ta kai shekara biyar ma bata fara ba.”

Humaira tace, “Wai dan Allah bakya jin haushi in aka ambaci Yaya Yusuf a kusa dake?.” Ameena tace, “Haushin me kuma?.”
“Akan abubuwan da yayi miki bakya jin haushin da dan Allah?. Abi mamaki yake bani sai naga in ana maganar sa bakya jin haushi sai dariya da nishadi ma da kika k’aro.”
“Hmmm! Humaira kenan, ai dashi da babu duk d’aya ne a wajena yanzu, kin San Allah mantawa nake ma ji dashi a duniya, sai Zaytun tana zancen sa nake tunawa dashi.” Humaira tace, “ai gwara hakan, ya cancanci ki manta dashi din, haushi yake bani gabad’aya ko magana bana so yayi min.” Ameena tayi dariya tace, “ke dai kika sani.”
“Da wata b’arauniyar matar sa.” Ameena zatayi magana sai ga Shukra y’ar Yaya Adam ta shigo tana cewa, “Munmy Kizo Inji Abba.” Ammeeena tace, “Yaya Adam yana kırana sai anjima” ta fad’a tana kashe wayar ta fita zuwa falon.

Su biyu ta tarar a zaune a falo shi da wani a zaune a kusa dashi tana zuwa yace, “To ga Ameena nan.” D’ago ido mutumin yayi ya kalli Ameena suka had’a ido sai tayi murmushi domin ta san shi tun a baya abokin Yaya Adam ne sosai ma kuwa tace, “Ina wuni.” Kallon ta yake yi fuskar sa da murmushi sosai yace, “Ameena kece kika koma haka?.” Tayi dariya kawai Yaya Adam ya kalle ta yace, “Koma ciki.” Ameena ta juya ta Zaytun ta bita tana kiran Mummy.

Tana barin wajan ya zare glasses d’in fuskar sa yace, “Wai dan Allah Ameenata ce wannan?.” Yaya Adam ya Harare shi yace, “na hana cewa Ameenan ka tun ba yau, amma ka kasa dainawa indai za’a zancen Ameena sai kace Ameenan ka.”
“Astagarifullah ashe tana da aure, nayi mamakin ganin ta ne wallahi rabona da ita fa tun kafin tayi aure, wannan yarinyar mai kyau y’ar tace?.” Yaya Adam yace, “y’ar ta ce mana, baka ji tana cewa Mummy ba?.”

Yayi murmushi mai bayyane da tsantsar haibar sa yace, “Gaskiya duniya na gudu sosai, har Ameena ta shekara hud’u da aure ko nace biyar ma. Allah ya cigaba da basu zaman Lafiya ya raya abinda aka Haifa.” Yaya Adam yace, “Amin, amma basa tare da mijin ya sake ta.”
A firgice Al’ameen yace, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Yarinya k’arama kamar Ameena ace a sake ta?. Adam yaushe hakan ta faru?.” Yaya Adam yace, “wallahi, kwata-kwata bata fi sati uku a gidan nan zuwa hudu, dan har yanzu bata gama iddah ba.”

“Kace kwanan ne ma.”
“Eh wallahi.”
“to Allah ya daidaita su yasa ta koma d’akin ta shine rufin asiri. Yarinya kamar wannan ace tana zaman gıda abun ai babu dad’i.”
“Ta bar wannan mijin nata, in kaga na bari ta koma to bani da rai.”
“Amma meyasa? Ka sani ko tana son sa?, ka sani k akwai wani rabon a tsakanin su?. Ka daina fad’ar haka in lokacin mutuwar auren baiyi ba zata koma.” Ya kalle shi yace, “baza ka gane ba ai shiyasa, amma da zan warware maka komai da kace tayi zaman ta ta samu wani mijin tayi auren ta. To bazan fad’a ba.”

Jin abinda Adam yace sai yayi dariya kad’an yace, “kar ka fad’a nima bance ka fad’aba ai, Allah yasa hakan ya zaman mata alkhairi. In kuma daman haka Alalh ya shirya mana nida ita to. Kasan babu ruwan Allah shiyasa ya baka damar hana ni ita a waccan lokacin, sai kaga a wannan lokacin ka kasa komai har na same ta.” Yaya Adam yayi tsaki kawai baice komai ba dan yasan daman Al’ameen sai yayi wannan zancen ganin hakan sai Al’ameen yayi dariya suka fara tattaunawa akan abinda ya zaunar dasu a wajan.

Tunda yamma tayi akace ga dangin wanda zasu kawo kud’in Rukayya sun zo ta kasa sukuni gabad’aya, ta kasa zaman d’aki sai kai kawo kawai take yi ta kuma kasa gasgata abun ta kasa tantance yanayin ta farin ciki ne ko akasin sa iya kanta bata sani ba.

Umma ce ta shigo ganin tana ta zagaye ta kasa zama ya saka tace, “Rukayya!.” Jin kiran ta da Umma tayi ya saka ta jiyo ta kalli Umman tace, “zagayen me kike yi haka kika kasa zama?.” Tayi shiru batayi magana ba Umma tace, “ba ke kika bawa Baban ku zab’i ba?.” Ta d’aga kai alamun eh tace, “Meyasa to kike tantama akan zab’in nasa? Ko kuma akwai Wanda kike so a cikin su?.”

Rukayya tace, “A’a Umma ba haka bane, na kasa banbance yanayin da nake ciki ne shiyasa na kasa sukuni.” Umma tayi dariya tace, “ki kwantar da hankalin ki kawai, ki jira su tafi na tabbatar zaki farin ciki sosai da zab’in mahaifin ki.” Umma har ta yi gaba zata fita Rukayya tace, “Umma!.” Umma ta juyo tana kallon ta tace, “Wa Baba ya zab’ar min dan Allah?.”
Chapter 17 · 0% Book details