← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 93

Sashe 23

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta idar ne tana zaune tana tunani mai had’e da dana sani aka kwankwasa k’ofar aka shigo sai ga wata yarinya a gaba bayan ta wata mai aiki ce baturiya ta rik’e da babban tray na abinci ta ajjiye ta juya ta fita ita kuma tabi Fiddausi da kallo da take zaune.
"Sannu fa y'ar uwa." Jin tayi hausa ya saka ta juya da sauri ta kalle ta tayi dariya tace, "kinyi mamakin jin ina hausa ko? Nima bahaushiya ce kamar ki matar mijin ki kuma, abinda ya kawo ki ayi dake shi ya kawo ni ayi dani nake zaune har wannan lokacin." Gaban Fiddausi ya fad’i tsoran ta ya ninka na baya dan lamarin Alhaji ya fara b’atar mata da hankali gani take Anya ma mutum ne, ta kasa magana sai kallo kawai waccan ta zauna tace, "inda zan baki shawara da nace ki amince kawai ayi a wuce wajan dan wallahi in baki amince ba kika koma hannun mijin ki wahalar da zaki sha Allah ne kawai ya Santa, kawo ki din nan da akayi ba k’aramin kud’i zai samu ba in kika k’i ki amince har ya saka a mayar dake kin shiga uku."

Fiddausi murya na rawa tace, "kema matar sa ce?." Tayi dariya tace, "matar sace ni, da yawa an d’auka ya sake ni basu San nan ya kawo ni yake kasuwanci dani ba." Fiddausi tace, "kuma kika amince ana lalata dake?."
"To ya zanyi? Bani da kowa bani da komai, hatta waya baza ki rik’e a gidan nan ba ko wanne motsi kika yi ana kallon ki. Ya zanyi in ban amince ba? Zan haura na gudu ne?.”
Fiddausi ta dafe kai tace, "na shiga uku ni Fiddausi na kawo kaina inda za'a hallaka ni, wacce irin masifa na jefa rayuwata a ciki?.” Yarinyar tayi murmushi tace, "kin ganni nan sunana Zainab ya auro ni shekara uku kenan dan a bayana aka auro Aliya da Naja'atu sai ke a yanzu, nida ke a yanzu bai d’auke mu matan sa ba ya barwa ogan su wannan Baturen dan nasan Kun had’u dashi wad’ancan ma sun zama hoto lokaci yake jira ya kore su ya auro wasu."

Fiddausi tana Jan numfahsi dakyar tace, "mutumin nan anya mutum ne kuwa?."
"Mutum ne, duk wacce kika gani a gidan sa son zuciya ne ya kawo ta kamar ke kamar ni kamar kowa ma, dukkan mu an aura masa mu babu bincike dan da akwai bincike babu wanda zai amince y’arsa ta aure shi. Dukkan mu yawanci son duniya ne ya kai mu ga auren sa, ke kin san y’an matan wannan zamanin mai kud’i kawai ko wanne Hali yake dashi ji muke zamu iya zama dashi indai akwai kud’i, gani muke kudin shine farin ciki shine kuma cinyewa saboda za’a dinga labari a cikin k’awaye ace ai wance matar mai kud’i ce,”

Fiddausi hawaye ya sakko mata kanta yana k’asa Zainab tace, "Yanzu kika fara kuka duk da ban San abinda kika aikata kika zo nan ba amma ina tabbatar miki da sai kinyi dana sanin zuwan ki nan. Da yawan mu guduwa mukayi muka aure shi wata kuma iyayen ta bijirewa, ni gani nake Anya baya yi mana asiri kafin yazo gare mu?.” Ganin Fiddausi ta kasa magana sai kuka da take yi tace, "Na tabbata kin tuna abinda ya wuce ne, kin ganni nan iyayena na gudawar aka d'aura mana aure dashi, babana baya so" muryar ta fara rawa kafin tace, "amma saboda kud’i da son kasancewa matar mai kud’i haka na tsallake umarnin sa na bar gıda ban koma ba sai da aka d'aura mana aure dashi, na baro iyayena suna fushi dani akan hakan amma ban damu ba kawai ina hangen zan shiga gidan sa na zama matar mai kud’i da nazo na kai su umrah shikenan zasu yafe min" sai ta tashe da kuka sosai itama ta sake cewa, "Sai gashi ranar da aka kaini wajan sa ya kawo ni k’asar nan mukayi sati biyu a lokacin ya fara bijiro min da son amfani dani ta baya, nak’i yarda yayi min ta k’arfi sai da na kwana biyar a asibiti na dawo daidai ya mayar dani Nigeria ya jibge ya hana ni waya da kowa nawa" ta goge idanun ta tace,

"A wannan lokacin ya auro Naja'atu ni kuma ya dawo dani nan ashe yarjejeniya ce a kaina za'a bashi kud’i masu yawa shi kuma zai barni a nan Ana amfani dani kamar karuwa, ko a jikin sa bai damu ba kuma bai sake ni ba. Haka nazo nan garin da farko na fara gaddama aka daina bani abinci aka daina bani abin sha tsahon kwana biyu ban sha ruwa ba" kukan ta yayi k’arfi sosai kafin ta tsagaita tace, "ina ji Ina gani wannan baturen yayi amfani dani ta gaba da ta baya a lokaci d'aya, daga rana aka fara bani abinci. Sai kuma aka bijiro min da saka min maganin bacci duk sanda yaso yin amfani dani za'a bani abinci nayi bacci daga nan ban San me yake faruwa sai dai na ganni a kwance babu kaya ko na ganni asibiti. Har gobe haka ake min na tabbata kema haka za'a yi miki dan indai ina cikin hayyacina bazan amince ba.”

Kuka suke sosai su biyun cikin k’unar rai ko wacce tana dana sanin abinda ta aikata sai ga wata baby mai kyau fara ta shigo d'akin ta nunawa Fiddausi ita tace, "yarinyar dana haifa masa ce y’ar uwa, nayi cikin shege da aure a kaina na haifawar baturen da ban San shi ba y’a gata nan ina kalllo."
"Na shiga uku ni Fiddausi, ina zan saka kaina naji dadi?, Mama da Abba kuzo ku taimaka min kafin na mutu!. Alhaji zai kashe ni bak’in cikin sa sai saka zuciyata ta buga.” Abinda ta fad'a Kenan tana kuka sosai dan abin yafi k’arfin abinda su Aliya suka fad’a mata.

Dukkan su kuka suke yi babu mai rarrashin wani a cikin su dan ko wacce dana sanin abubuwan da ta aikata take yi, ba kamar Fiddausi in ta tuna har ciki ta zubar sai taji kamar ta kurma ihuu ta dinga Marin kanta. yarinyar mai suna smart tana ta kallon su tana tsaye a gefe kamar ta san kukan ne suke yi. Bud’e k’ofar akayi aka shigo ganin wanda ya shigo ya saka Zainab mik’ewa ya bita da kallo yace, "Zuwa kika yi kina fad’a mata zancen kema haka akayi miki?." Zainab tace, "ka kiyayi karshen ka wallahi, sai kayi dana sanin abinda kayi mata."

Yayi dariya yace, "kune zakuyi dana sani, ke iyaye kika gudarwa kika aure ni ita kuka mijin ta mai sonta da kula da ita ta gujewa saboda ta auri mai kudi. To Gashi ya aura kasar da take burin zuwa gata a cikin ta sai tayi abinda take so." Magana Fiddausi take so tayi amma babu hali sai hawaye da yake ambaliya fuskar ta kamar tumatur saboda Jan da tayi. “Kaicona, kaicona ni Fiddausi. Allah ka yafe min Ibrahim ka yafe min, iyayena ku yafe min abinda na aikata. Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!.”

"Duk a cikin matan dana aura nafi sonku shiyasa na kawo ku nan dan ku samu kud’i kuji dadin rayuwar ku, ke Fiddausi yanzu yace mu koma Nigeria dake tafiyar gaggawa ta kama shi zuwa Germany a k’alla zaiyi sati biyu. Ke kuma zaki bar masa masa y’ar sa a nan daga nan ki tafi gidan ku na sake ki." Wani irin numfashi taja cikin farin ciki sai kuma hawaye ya biyo baya da tunawa da abubuwan da ta aikata kafin a sake ta din ta zube a wajan tana kuka mai matuk’ar yawa.

Sai ya kuma ta kalle ta yace, "Zee kafin ki tafi bazan barki haka ba ya kamata" ya fad'a yana jefa ta kan gadon ta tayi baya ta dire sai yayi dariya kawai yace, "bazan sake waiwayon ragowar bature ba, zamu wuce gobe zuwa Nigeria har ke daga nan ki kama gaban ki, baki San wani Alhaji Bello ba ko a mafarki." Jikin ta rawa take yi sosai ya juya ya fita har lokacin jikin ta bai daina rawa ba tana kallon Fiddausi itama ita take kallo ko wacce kuka take yi mai tsuma zuciya sautin sa ya karad’e d’akin gwanin ban tausayi.
Babu mai iya yiwa wani magana a cikin su suna nan zaune bacci ko wacce ya kauracewa idanun ta har safiya tayi ko wacce na zaune idanun ta kyam suka fito suka hau jirgi zuwa Nigeria. Zuciyar Zainab na farin ciki wani b’angaren yana bak’in ciki a haka suka tawo Nigeria.

Asiya tana tsaye a jikin madubi tana shiryawa shi kuma yana gefe yayi tagumi kamar ko yaushe ya rasa abinda yake masa dad’i ya rasa meye yake addabar zuciyar sa ya rasa sukuni, juyows tayi ta kalle shi tace, "My love dan bani kayana na saka." Bai ce komai ba kamar bazai tashi ba sai ya tashi zuwa inda kayan suke ya bud’e yace, "wanne kike so?."
"Duk wanda yayi maka shi nake so.” Ta fad’a tana murmushi tana kallon sa shi kuma gabad’aya ba wannan ne a gaban sa ba.

Kayan Gasu nan a hargitse babu gyara ko na sisi baka gane ma wanda zaka d’auko, ya tab’e baki ya jawo wata atamfa da yake gano daga can k'asa sai yaji abu ya biyo atamfar ya fad’o kan k'afar sa. Atamfar ya cilla mata yana kallon abinda ya fad’o yayi ya sunkuya ya d’auka ya kalla ya kalle ta ya sake kalla yace, "Kaii! Wannan ba sark'ar dana nema na rasa bace ba?."
Asiya ta diririce tsoro ya bayyana a tare da ita sosai amma sai ta basar ta daure tace, "a nan ka ajjiye kenan? Kaga ban ma San ka ajjiye din ba." Kallon ta yake yi da mamaki gaban sa yana fad’uwa matuk’a yace, "ya akayi tazo hannun ki? Kenan a waccan ranar kece kika dauk'a?." Banzar harara tayi masa tace, "kamar ya ni na d’auka? A ina nasan inda take da zan d’auka? Ka ajjiye abu kuma kace min nice na d’auka?. Inda ni na d’auka zata Kai yanzu ban je na siyar ba?.”
Chapter 23 · 0% Book details