Sashe 89
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikin Ruky yayi sanyi sosai ta kalle shi tace, "Amma Fiddausi tayi nadama walalhi, abinda tayi a baya duk yayi danasani."
"Duk ta banza ce sai da tasha wahala sannan tayi, ke yanzu kika ce min wanna labarin da na baki ba dan Allah yake sonta ba, Nima Indai na dawo da ita ta zauna ba dan Allah take sona ba wallahi. Da zarar abinda na samu ya k'are zata sake guduwa ne saboda ita ba kalar zama da irin İbrahim baca, kalar matar manya ce kiyi mata fatan Allah ya bata manyan amma ba irin ibrahim ba.” Rukayya zatayi magana ya dakatar da ita yace, "na fiki sanin halin ta, kar kice min komai abinda kike fad'a ba abu bane wanda zai yu. Na yafe mata duk kuskuren da tayi saboda d'anta Amir da kuma mahaifin ta, amma bayan wannan babu wani abu da zai sake had'a ni da ita."
Rukayya tace, "kodan saboda Amir din zaka dawo da ita, itace ta haife shi amma bai saba da ita sosai ba, akwai ciwo ace ka haifo yaro kuma bai shak'u da kai ba Khalil, dan Allah ka San abinda zakayi."
"Amir ai d'an tane tana da ikon zuwa ta d'auke shi yayi kwanaki a wajan ta ko yaushe, bar mata shine ko zata mutu ta dawo bata isa ba wallahi. İn zamu koma Abuja ma zai zauna a hannun ta kafin muje muga ya yanayin garin da makarantar da za'a sake shi ya koma."
Rukayya ta kalle shi kafin tayi magana yace, "kar ki sake wahalar da kanki bazai yu ba, Alhaji ma yayi min maganar saboda rashin mahimmacin ta ya saka ban miki maganar bama na share."
"Tunda har Alhaji yayi maka magana akwai dacewar ka dawo da ita din."
"To bazan yi ba. Ni Wallahi kin ma bani mamaki, duk soyayyar da kike nuna min ashe daman zaki iya kawo min tallan wata kice na aura?. Kishin ashe duk na banza ne babu inda yaje."
Tayi murmushi tace, "to kishin me zanyi bayan Fiddausi itace ka fara aura kafin ni? Har kawo gobe kuma kana sonta kawai abinda tayi maka ne yake yawo a zuciyar ka amma soyayyar ta da wahala ta bar zuciyar ka.”
Ya kalle ta yana tab'e fuska yace, “haka nace miki?." Tace, "hakan ne ma, kar ka manta mu ne yan tayin hira kai da ita, mun san adadin soyayyar da kake mata, ko ni ka kalla ka fad'awa kana son ‘kawa ta son da baka San Adadin sa ba. Duk wata soyayyar ku mun sani saboda ta kasance ta farko a cikin mu da ta fara aure duk wani labarin soyayya a bakin ta muke ji, kana sonta itama tana sonka, domin dukkan ku akan juna kuka fara sanin meye so har ta kai ku ga aure, meyasa baza ka kawar da haushin ta da kake ji ka juyo da soyayyar ka mayar da ita ba?."
Kallon ya yake kawai baice komai ba ta d’ora hannun ta a k’irjin sa daidai zuciyar sa tace, "Akwai Fiddausi a nan, haushi ne ya saka kake ganin kamar babu ita amma da zaka manta da b'acin ran tabbas zaka gano tana nan daram Rukayya sai dai ta biye mata baya. Domin Fiddausi ce ta fara shiga cikin nan kafin Rukayya. Kayi tunani Khalil ba dan ita zakayi ba dan mahaifinta da ya tsaya akan aurena da kai, dan kuma d'anta Amir da take bukatar sa a kusa da ita. Kayi tunani, kayi tunani zaka gano dacewar abinda nake fad’a.” ta fad'a tana d'auke hannun tana sake mayarwa kamar tana dukan wajan.
Zata d’auke hannun gabad'aya ya rik'e ya kalle ta yace, "babu ko wacce mace a zuciyar nan in ba ke ba, a baya wacce kike magana ta zauna a cikin ta amma a yanzu babu koda b'urb'ushin ta a ciki kin saka tsintsiya kin share kin kuma goge ko ina kyallin ki ne kawai a cikin sa. Ki daina tunanin ina son Fiddausi har gobe domin kuwa yaudarar kanki kike wallahi, indai kika ce ni Ibrshim ina son wata halitta Fiddausi kinyi karya kin kwana da yunwa domin kuwa in ba zance ta akayi ba mantawa nake da ita wallahi. sannan ki nutsu a bar zancen haka tun bai b'ata min rai ba kar yazo ya b'ata min rai. An kuma nuna min iyakar matsayin da nake dashi tunda har zaki iya yi min tallah wata mace kice na aure ta."
Kallon sa take yi har ya gama maganar tace, "ka sake yin tunani dan ka dawo da ita zai iya zama alkhairi a rayuwar ka. Ka duba Ameena ta koma gidan Yusuf zaman yanzu yafi mata zaman baya dadi da farin ciki, meyasa kaima baza ka hango hakan ba?."
"Bazai tab'a zama alkhairi ba, sanda nake tare da ita k'ofar wahala ce a bud'e a tare dani, daga lokacin da akace bata nan k'ofar wahala ta kulle k'ofar alkhairi ta bud'e a rayuwata. Komai yana da sila silar duk abinda nake dashi a yanzu kece silar sa, dan haka kar ki sake yi min maganar a barta a wajan nan a hak'a rami a binne ta in dai bakya son b'acin raina."
Zatayi magana yace, "nace a bar maganar, bana son ta, a ajjiye ta har abada kar a sake dawo da ita. In ba haka ba kuma raine zai zo ya b’aci.” Jin yadda yayi maganar sai ta sauke numfashi tace, "Inda rabo Allah ya daidai." Murmushi yayi wanda bai shirya ba wato baza ta bar maganar ba kenan ya girgiza kai baice komai ba.
Noor ce tashi ta fara kuka ta d'auke ta ya tashi ya kalle ta yace, "in kika cike kwana arba'in zamu tafi Abuja gida da komai akwai a can. Ki fara shiryawa tun yanzu saboda gudun mantuwa" yana fad'a ya fita ya barta tayi ajiyar zuciya har zuciyar tana so ya dawo da Fiddausi amma taga alama bazai yi hakan ba dole ta kama kanta.
Fiddausi da Zakiyya suna gidan Ameena suna hira cikin nishadi suna ta darıya Ameena tace, "yanzu Fiddausi zawara suna ta zuwa ko?." Fiddausi tayi murmushi tace, "Eh to babu laifi zance, akwai mutum biyu yanzu da suka fito suna so." Ameena ta sauke numfashi tace, "ni wallahi gidan Ibrahim nake so ki koma kamar yadda na dawo hannun Yusuf."
Fiddausi ya wara idanu tace, "Ibrahim fa kika ce Ameena?." Zakiyya tace, "Ai bata san abinda aka aikata masa bane shiyasa take cewa haka."
"Ko mai aka aikata ai gani ai a gidan Yusuf na dawo duk abinda yayi min."
"Ai ke ba kece kike yi kuskuren ba shine, kuna kuskuren Fiddausi yafi na Yusuf wallahi. Kinga dai ban san abubuwan da suka faru tsakanin ku ba ko? Amma wallahi na tabbatar laifin ta yafi na yuusf."
Fiddausi tace, "fad'a mata dai, ni bana kawo hakan a zuciyata Allah ma ya sani."
Ameena tace, "tunda aka yafewa Yusuf to meye in an yafe miki? Kodan saboda Amir ai ya kamata yayi duba akan dawo dake." Fiddausi tace, "magana kike akan abinda bazai yu ba, kuma koda zai yu ni bazzan auri mijin Rukayya ba.” Ameena tace, "wannan duk ba abin dubawa bane, abinda ya kamata ayi shi ya dace ayi wanda ya kamata a bari shi ya kamata a bari. Rukayya tafi kowa son ya mayar dake wallahi, ko jiya sai da mukayi waya da ita akan hakan ta tabbatar min da zata same shi da maganar ko meye zai faru."
Fiddausi zatayi magana wayar Ameena tayi k'ara ta kalle su tace, "yar halak" ta d'auka ta saka speaker daga can b'angaren Rukayya tace, "Ameena munyi maganar dashi fitar sa kenan yanzu na kira ki." Ameena ta kalle su tace, "ya ake ciki?."
"Ameena da muna zancen da wasa da dariya na d'auka abin zai zo da sauk’i amma ya tirje yace na sake masa maganar ma sai raina ya b'aci. Dan Allah meye laifin Fiddausi da bazai dawo da ita kodan saboda mahaifin ta da kuma Amir ba?. Abba shine ya bada gudunmawa da goyan baya wajan aurena dashi, indai ana cin albarkacin wasu meyasa ita baza tacı albarka sa ba?."
Ameena ta sauke numfashi tace, "to ke yanzu ya kuka yi?."
"Yak'i fa, wai wanda ya guje ka lokacin da baka dashi yanzu da ka samu abinda ka samu in ya dawo ka sake karb’ar sa nan gaba ka sake rasa abinda ka samu zai sake gudun kane. Kuma shi wai baya ma tunanin dawo da ita yana kallon ta matsayin k’awa ta kuma babar Amir. Kuma kin san Allah baza'a rasa soyayyar ta a zuciyar sa ba, ke shaida ce ya so Fiddausi. Ni wallahi gabad'aya raina ya b'aci."
Fiddausi da take jin abinda yake cewa ta goge idanun ta tana farin cikin samun kawaye na gari da tayi tace, "Rukayya kar ki b’atawa mijin ki rai saboda ni, kar ki lalata zamantakewar ku saboda na tabbatar Ibrahim bazai sake kallona matsayin matar sa ba nima bazan kuma kallon sa a matsayin mijina ba sai dai mijin Rukayya. Ki bar maganar nan akwai Ruky Amir yana da uwar da ta fini gaki nan, kawai ku taya ni addu'a Allah yayi min zab’i mafi alkhairi."
Rukayya da take jin abinda take cewa, "Fiddausi bazan daina ba, yanzu kuma na fara sai inda karfina ya kare akan dawo dake. Kina son kasancewa da yaron ki meyasa baza ki amince ba?.”
"Bazai tab'a dawo dani ba wallahi, wallahi Ibrahim bazai saurare ki ba kin san halin mijin ki. Ki daina wahalar da kanki da bakin ki domin abinda kike nema baza ki samu ba. Ke koda zai amince ni wallahil azim bazan amince na auri mijin ki ba.”
"Mtsww! Zancen kike so" ta fad'a yana yanke wayar Ameena tayi dariya tace, "Rukayya ta matsa akan komawar ki, ni har mamaki ma take bani Rukayya mai kishin tsiya amma itace ta tsaya kai da fata akan sai ya dawo dake?, ko da yake tace wai kishin me zatayi ai ke kika fara auren sa.”