← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 93

Sashe 6

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakin labulen yayi ya rasa abinda yake masa dadi a zuciyar sa ji yake kamar ya zubar da hawaye, bashi da mafita a wannan lokacin tunda tace zata kira Amma yasan zata iya shi kuma bazai zo hakan ba. taya zai iya had'a jiki da Asiya tana wari?, fatar ta na maik'o tana jiki duk Gashi?. Tsigar jiki sa ta tashi dan tunawa da abinda hakan zai haifar masa dan Allah ya sani baya son wari ko kusa. kai ya girgiza kawai yaje ya kulle k'ofar ya karasa wajan kayan sa ya saka ya dawo ya kwanta kusa da Zaytun baya tunanin zai iya aikata wani abun da Asiya a yanayin da take.

Kusan mintina talatin yana a haka shiru bai ji tana buga masa k'ofa ba sai ya kwanta da niyar bacci amma sai y kasa sam zuciyar sa a cushe take yana ta hasashe abubuwa kala-kala akan abun  sai akwai ya sakko daga kan gadon ya fita zuwa d'akin ta. Bud'ewa yayi ya shiga yana kallon ta a kan gado gaban sa yana fad'uwa zuciyar sa na yin rawa saboda abinda ya gani wanda bai kawo hakan a zuciyar ba shine ya kwo masa sanyin jiki da tsinkewar zuciya lokaci d'aya.

#Mai daki
#Book3
#Paid
#500
#Nana Haleema

Book2
004

Duf duf duf haka gaban sa take bugawa ya had’d’iye abinda yazo masa wuya yana takawa a hankali yana sake wara idanun sa akan Asiya da bata san ma yana shigo ba saboda hankalin ta da tunanin ta basa tare da ita a wannan lokacin balle taji sautin bud’e k’ofa ko sautin takun takalmin sa. Idanun ta a lumshe suke sai sauke numfashi take yi tana k’ananun maganganu hannun ta d'aya yana kirjin d’ayan kuma tana wasa da gaban ta cikin fitar hankali da son cimma abinda zuciya take so.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya maimaita a bayyane ganin har lokacin fa bata san ma yana wajan ba da hanzari ya k’arasa inda take yace, "Asiya!." Yadda yayi maganar da k’arfin gaske a zabure ta mik’e zaune tana kallon sa shima ita yake kallo yana sauke numfashi saboda abinda ya gani ita kuma tana saukewa idanun ta akan fuskar sa.

Ba alamun tsoro ko kunya a tare da ita sai ma hararar sa da tayi idanun ta kyam a kan nasa, muryar sa har rawa take yace, "me kike aikatawa haka? Kina da hankali kuwa?, meye hakan?." Bata yi magana ba har lokacin numfashi take saukewa a hankali sai tana so ta tattaro nutsuwar ta gabad’aya ta dawo da ita jikin ta daga baya tace, "Abinda ka gani shi nake aikatawa."
"Kina da hankali kuwa?, wai kin San me kika aikata kuwa? Mastrubation fa kike aikatawa?, hauka kike Asiya?.”

"Koma me na aikata ai kaine sıla; laifin kane kaine kaso hakan da baka so ba da bazan yi ba" ta fad'a tana kallon sa sai kuma ta fara kuka tana fad’in, "Allah ya isana, ka saka na aikata abinda ban tab'a yi ba saboda rashin samun had’in kanka. Inda ka bani abinda nake so da duk hakan bata kasance ba. Na fad’a maka ai ina buk’atar ka k’arshe sai kace nazo nan ka kulle kofar ka, ya kake so nayi maka?, ne kake so nayi in ba hakan nayi na samarwa kaina mafita ba?. Tunda abin naka haka ne wallahi bazan d’auka ba zan kai k’arar ka zan kai wajan iyayen ka."

Yusuf da yake kallon cikin tashin hankali da mamakin abinda ya gani wanda bai tab’a gani a zahiri ba yace, "It's just a few days fa, ba wata ba balle shekara shine har abin ya kai da nazo na same ki a wannan yanayin?, ina hankalin ki da tunanin ki ya tafi? A ganin ki wannan abun wasa ne?” Ya fad’a a fusace cikin fad’a yana kallon ta.
"Kar ka soma yi min masifa ko kace zaka d’aga min murya, kai a ganin ka kwanakin ai basu da yawa ni a ganina suna da yawa kuma wallahi bazan d’auka ba dole na sanar da na sama dakai a dauki mataki da gaggawa.”
"Amma kin sa aikata hakan haramun ne ko? Sannan lafiyance babbar illa ce a gare ki ko?."
Ta kama k’ugu tana kallon sa tace, "Mata kake so na nema ko maza to? Fad’a min sai na canja daga salo daga yau."

Sai ta sake fusata shi ya zabura kamar zai dake ta yace, "ina miki magana akan abinda kika aikata kina min maganar wai maza zaki bi ko mata?, meyasa baki da hankali ne kewai?, kin san illar abinda kika yi?.” Ta ja baya tana kallon sa tace, "koda wasa kar hannun ka yazo jikina da sunan duka wallahi daga ranar zaka yi dana sanin fara dukana. Ina ruwan ka da illar da abin yake dashi naga jikina ne ko?.”
"İn na dake ki din me zaki yi?."
"Ka gwada ka gani mana sai ka gwada zaka tabbatar da abinda zanyi, ni ka fita ka bani waje bazai yu ayi min laifi ba kuma azo an yi min ihu a kaina ba, ga mari ga tsinka jaka kai kasan bazai yu ba.” Sai kuwa yayi kwafa ya fita daga d'akin ta bishi da harara ta tashi ta shiga band’aki.

Tana fitowa daga bandakin ya sake shigowa ta kalle shi ta d’auke kanta ya k’araso ya zauna itama ta zauna yace, "kar ki sake aikata abinda kika aikata Asiya, na yarda laifina ne amma hakan bai kai da ki jefa kanki cikin wannan mummunar dabi'ar ba. Yanzu in kika sabarwa kanki shikenan ko me za’a yi miki sai kin yi zaki ji dad’i, hakan ba daidai bane ba abu bane mai kyau na fad’a miki. Daidai yake da aikata zina.”
"Kar ma ka yarda laifin naka ne mana, ka zauna kana yi min fad’a ni kuma naje na sanar da na gaba dakai.”
"Wai ke baki iya magana bane?, baki San ta yadda zaki magana da mutane ba?. Ina kyale ki amma bakya ganewa kika kai ni bango wallahi zaki mamakin waye ni.” Ta murguda baki bata sake kallon sa ba balle tayi magana.

Yace, "Nidai na fad’a miki kar na sake ganin kina wannan abun in ba haka ba zan d’auki mataki a kanki wallahi, bazan zauna da mace mai irin wannan Hali ba, ba dabi'a ta gari bace ba kuma abin burgewa bane, cutar kanki zaki yi domin abinda kika fara zai iya hana ki zaman aure.” Shiru tayi bata amsa ba yace, "Daman kin saba aikata hakan ne?." Ta kalle shi ta girgiza kai tace, "ban tab'a ba sai yanzu, kuma laifin kane ai na fad’a maka amma sai ka k'i ji" ta fad'a kamar zatay kuka.

"Shikenan nasan laifina bazan sake ba amma dan Allah kar ki sake abinda kika yi domin zai iya sakawa na yanke wani hukuncin a kanki.” Kai ta d’ag alamun to ya kalle ta yace, "ba gudun ki nake ba Asiya matsalar daga wajan ki ne, bakya gyara jikin ki gabad’aya ko turare bakya amfani dashi taya kike ganin zan iya wani abun dake a wannan yanayin?. Da da nake zuwa gidsn ku ba haka kike ba ko yaushe cikin khamshi kike yanzu kin canja. Zuciyata har tashi take wani lokacin kamar zan yi amai in nazo kusa dake, dan Allah ko gyara in ba haka ba samun kaina zai dinga miki wahala."

Lallai ma gayen nan ya raina min hankali, ni zai kalla yana fadawa wannan maganar ba kunya ba tsoron Allah?, lallai ya kamata na sake d’aukar mataki a kansa tunda aka fara zuwa wannan gab'ar, tace, "Me kake nufi?."
"Kin San me nake nufi, dan Allah ki dinga gyarawa; gabad’aya gidan nan ya canja saboda rashin kulawar ki, bana son k'azanta wallahi, hankalina tashi yake in naga ina waje kuma ana k'azanta a wajan."

Ta zuba masa ido tace, "kenan ni k'azama ce?." Ya kalle ta shima yace, "Nidai ban ce k'azama bace ba amma ya kamata ki gyara." Shiru tayi bata ce komai ba sai ya mik’e zai fita ya rik’o hannun sa tace, "to ina kuma zaka je?." Ya dawo ya zauna yace, "ai naga rashin kunya kike ji da ita ne shiyasa zan baki waje kafin na kasa jurewa.”
"To kayi hakuri" ta fad'a tana matsowa jikin sa ta kwanta duk da tayi wanka amma wallahi wari yake ji a jikin ta amma babu yadda zai iya. Shi dai kawai ya daure yayi abinda take so tunda yaga hakan yana neman kawo matsala amma wai dan son ransa ko dan yana so bazai aikata komai ba domin sai da tsafta zai samu nutsuwa.

                Yana komawa d’aki Zaytun ta farka tana cewa, "Mummy ruwa." Ji abinda take cewa sai ya d’auki ruwa ya karasa inda take ya zauna ya bata ta kalle shi cikin karamin hasken d’akin tace, "Daddy wajan Mummy zan je."
"Shiii ki yi bacci zan kai ki" ya fad'a yana kwantar da ita a jikin sa a hankali ta fara komawa baccin.

Tunani ya tafi yi rabon sa da wani abun ya had’a shi da Ameena kusan watanni zai ce ba kwanaki ba, ya kwantar da Zaytun lokacin bacci ya dauke ya ya sake tashi yaje yana kallon tagar Ameena, _indai Asiya zata aikata abinda ta aikata dan anyi kwanaki goma zuwa sama da haka ban kula ta ba Ameena ya kenan?, wanne irin yanayi ta shiga a wannan watannin dan nasan Ameena bazata aikata abinda Asiya ta aikata ba._ yayi Ajiyar zuciya ya sake labulen ya koma ya zauna ya dafe kansa gabad’aya ya rasa abinda yake yi masa dadi a zuciyar sa.

Wayar sa ya d’auka ya shiga WhatsApp ya dubo lambar ta message din ta na karshe shine wanda take fad’a masa zata je asibiti, online ya gani a k’asan My Choice sai ya kifa wayar a kan gado ya saka hannu yana shafa dukkan fuskar sa a bayyane yace, "Meyasa nake jin wani iri in ana yi min maganar Ameena? Meyasa ma...?" Sai kuma yayi shiru ya dafe kansa ya koma ya kwanta da baya yana kallon sama kafin ya kulle idanun sa.
Chapter 6 · 0% Book details