← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 93

Sashe 27

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta bishi da kallo tayi murmushi tace, “to yayi kyau. Sai kuma kudin da aka kashe da aka kaita asibiti, Mun kashe dubu d’ari biyar saboda asibitin kud’i muka je, ka bada kudin yanzu.” Yusuf yace, “sai dai bani account number na saka.” Umma ta kalli Maimuna tace, “bashi ya saka.” Maimuna ta karanto masa yana rubutawa kafin yace, “na saka kudin.”

Umma tace, “ina zuwa bara na turo maka ita dan tayi fushi akan lamarin sosai.” Yana zaune Umma ta tashi ta shiga ta samu Asiya har ta saka kaya Umma tace, “au har kin shirya ma kenan?.” Asiya tace, “to ga gidana inda zanje naci abinda nake so nan an bani bak’in shayi babu madara.” Umma tace, “aikin mu ya kama shi sosai, duk aikin da muke ma zan iya cewa sai yanzu ya shiga jikin sa tunda kika ga ya kawo kansa har yana neman a bashi ke ku koma. Lokacin mulkin ki yayi yanzu sannan lokacin da zaki tara mana yayi.”

Asiya tace, “Allah yasa dai, wani lokacin kamar aikin ya kama shi sai kiga ya sake komawa daidai.”
“Wannan ya kama shi kenan kuma ai. Yanzu ina abinda yace kin d’aukar masa dan nasan kin d’auka wallahi.” Asiya tace, “Kai Umma, sark’a ce fa tana nan kuma.”
“Ki turo da ita a siyar a ajjiye kudin.” Asiya ta turo baki tace, “to Umma duk abinda na tara indai zan dinga aiko muku ai bazan tashi da komai ba kenan.”

“To dan uban ki kin san kudin dana kashe kafin ma ya aure ki? Bana son shashanci da shirmen banza in badan ni ba kin isa ma ya aure ki kina fama da wannan shegiyar k’azantar?.” Ta saka hijjabin Momi tace, “Nidai a bar min sark’ar zan samo kud’i na turo miki dashi.” Momi da ya shigo tace, “kika saka min hijjabi? Wallahi ki cire min domin sai ya kwana goma yana warin jikin ki.”
Umma tace, “meye haka ke kuma?.” Momi ta Harare Asiya tace, “Wallahi Umma in ta saka duk wankin da za’a yi masa kafin ya fita sai an sha wahala.” Asiya suka fito ita da Umma yana ganin Asiya sai yayi murmushi amma zuciyar sa kuka yake yi ya mik’e tsaye Umma tace, “gata nan na sake dawo maka da ita Yusuf kar wani abun ya sske faruwa dan Allah.” Yusuf yace, “in sha Allah babu abinda zai kuma faruwa.”

“A’a Yusuf.” Baba ya fad’a yana shigowa. Yusuf ya tsuguna har ‘kasa ya gaishe shi ya amsa yana cewa, “Yusuf ka tsaya tsayin daka akan iyalan gidan ka, kar ka bari wani ki wata ta shiga tsakanin ka da iyalan ka, in namiji bai zama tsayayaye a gidan sa ba zai zama tamkar bola a wajan matar sa komai ta d’auko zata watsa masa ne, koda yaso gyarawa a gaba bazai yu ba domin ya riga yayi sake tun farko ya bar ragamar gidan sa a hannun mace. Ina mai baka shawara da kar ka bar ragamar gidan ka a hannun mace domin nan gaba zaka yi dana sani. Sannan ka tsaya ka nutsu akwai abinda bazai gyaru ba koda kayi k’ok’arin gyarawa domin hakan ya samo asali tun daga tushe, haka zaka gaji da magana ka gaji da yawo k’arshe sai ka bar wannan abun hankalin ka zai dawo jikin ka. Ka kuma dinga addu’a rashin ta yana daga cikin abinda ya kawo ka nan.”

Shi dai Yusuf gabad’aya ya rasa gane inda maganar Baba ta nufa amma sai yayi murmushi yace, “In sha Allah.” Baba yace, “Allah ya kiyaye hanya ya bada zaman Lafiya” ya fad’a yana shigewa ciki Yusuf suka fita. Umma tabi bayan Baba zuwa d’aki tace, “malam me kake nufi da bayanin da ka yiwa Yusuf?.” Baba ya kalle ta yace, “in kina tunanin akwai abinda nake nufi to ki d’auka akwai din kawai.” Umma tace, “in ma dai zuga shi kake akan Asiya wallah babu abinda zai faru In sha Allah, Haba ni tab’a ganin uban da yake yiwa yar sa bak’in ciki ba sai kai” ta fad’a tana fita yayi dariya ya girgiza kai domin kuwa yasan za’a gab’ar da Yusuf zai dawo da Asiya gida.

Bayan kwana biyu.

Bikin Rukayya ya kankama ana ta shirye-shirye ta ko wanne b’angare babu kamar gidan su Rukayya da ake fito da tsofaffin ajiyar kayan kitchen da aka siya mata ana wankewa. Amarya Rukayya ita da Ameena da Zakiyya suke shirin su sun d’auke mata kewa gabad’aya sun cire mata fargabar auren Ibrahim ta sake sosai dashi suna shansoyayya dashi.

Ya rage saura sati d’aya ta tare suna zaune ita da Zakiyya suna jiran Ameena tace zata bata zo ba Rukayya tana yi mata waya sai gata ta shigo Rukayya tace, “Na d’auka baza kizo ba ai.” Ameena tace, “Yaya ne baya barina fita wallahi, dakyar ya barni nazo m yanzu ma wallahi.”
Zakiyya tace, “eh gashi nan ai sai kyau kike yi wallahi kin mayar da jikin ki kamar ba ke ba.” Tayi murmushi tace, “ke wai har yanzu ba’a samu Fiddausi a waya bane? Rashin samun nan nata yayi yawa sosai.” Zakiyya tace, “Bari kawai, wallahi shiru ba’a samun ta ta ko wanne bangare. Amma yanzu gidan su zan shiga wajan Mama naji ko sun samu labarin ta.”

“Ya dai kamata wallahi, ke baki da lambar Alhajin?.”
“Wacce nake da ita batayi yanzu wallahi.”
“To Allah yasa dai Lafiya” Rukayya ta fad’a tana zama kusa dasu. Suka amsa da amin Ameena tace, “yanzu ya ake ciki?.”
“Jiya baki zo ba muje gidan amarya, ke kinga gidan İbrahim Ameena?” Zakiyya ta fad’a tana dariya kafin tace, “hmmm gida mai kyau da falo da dakuna ke baki gani ba, komai ma sha Allah babu inda ba’a sakawa kaya ba nace daman wannan ai shine bikin y’ar gata.”

Ameena tace, “Alhamdulillah, haka muke so ai, nima nazo a kaini in Yaya ya barni. Ya batun maganin kin Shan na sanyin?.”
Rukayya tace, “eh Zakiyya ta bani na wajan wannan Surayya Halin yau din gaskiya yana da kyau sosai nima na gani.” Ameena tace, “to kar dai kice zaki sha wani kayan matsi ko wani abun, kije masa a natural taste din ko ya kika je Zakiyya?.”

Sukayi dariya tare da tafawa Zakiyya tace, “Gaskiya ne wallahi. Abin mamaki wai Rukayya matar Ibrahim ce a yanzu, ikon Allah kenan.” Ameena tace, “babu mamaki an ikon nasa ai daman Kiyya. Yanzu me kike ganin zaki gabatar a bikin?.” Rukayya tace, “ni babu komai wallahi, da zaku zo dai a hadu ayi saukar alkur’ani zai fi min dad’i.” Ameena tace, “me zai hana muzo? Bikin kine fa Ruky.”
Zakiyya tace, “zamu zo in sha Allah, Allah dai ya nuna mana wannan lokaci.” Suka amsa da amin suka cigaba da hirar bikin.

A gidan su Fiddausi Maman su ce a tsaye tana jiran Abban su ya fito daga d’aki yana fitowa tace, “Alhaji.” Ya tsaya ya kalle ta yace, “Lafiya dai?.”
Mama tace, “Fiddausi.” Abba ya gyara ta tsayuwa yace, “me ya same ta?.”
“Malam rabon da mu samu Fiddausi a waya har mun manta, mun rasa dalilin da ya saka bama samun ta a waya dan Allah ko zaka taimaka a kira mana mijin nata ko hankalin mu zai kwanta,”

Abba ya kalle ta yace, “Ni nake da lambar mijin ta?.” Mama tace, “na d’auka kana da ita ai.”
“Auren da kuka d’aura shi bana nan an ina zan samu lambar sa? Kije ki samu Kawun ta ai ta inda aka hau ta nan ake sauka ya samo muku lambar sa sai kuyi magana.”
Mama tace, “munyi magana dashi yace baya samun lambar sa, dan Allah Alhaji ka daure ko wani daga gidan dangin mijin nata ne a nema a tambaya. Hankalina ya tashi wallahi ko Lafiya ce ta haifar da shirin ya kamata mu sani.” Alhaji yace, “babu wanda na sani a dangin mijin ta ki koma wajan wanda ya bada auren nata ki tambaya bani ba. Baku sam mutum ba baku yi bincike a kansa ba kuka d’auki yarinya kuka bashi a cikin sati biyu kawai dan kar na dawo na hana auren akayi aka kaita Abuja a jirgi. Watakila dan yankan kaine ya kai an yanke mata kai amfanin ta ya k’are a wajan sa.”

Mama tace, “Haba Alhaji, dan Allah ka daina fad’ar wannan maganar mahaifin tane kai fa.”
“Kun bani mahimmacina ne a lokacin auren? Ba aurar da ita kuka yi ba kuka kaita ai ta samu gidan mai kudi. Bara na fad’a miki abinda baki sani ba Fiddausi da kanta ta kashe auren ta, wannan wanda ku ka bata auren sa ya jima suna tare dashi shine ya zuga ta ta kashe auren ta da Ibrahim ai talaka ne zata auri mai kudi.”

Mama tace, “Haba Alhaji taya zata aikata haka da ilimin ta fa?.” Zaiyi magana Kenan Zakiyya tayi sallama ta shigo ta durk’usa har kasa ta gaishe su bata d’ago ba tace, “Mama dan Allah ana samun Fiddausi a waya kuwa?.” Alhaji ya kalli Mama yace, “ki bata amsa ba’a samun ta a waya baku san ta wacce hanya zaku nema ta ba, ba dai ta d’ora rayuwar ta akan motar kwad’ayi da hange ba? Wallahi a tashar wulakanci zata ajjiye ta” ya fad’a yana saka hular da ya fita Mama ta bishi da kallo kamar zatayi kuka.

Mama ta kalli Zakiyya da ta mik’e tsaye tace, “Zakiyya jikina yana bani wani abun ga samu kawar ki.” Ta fashe da kuka Zakiyya tace, “in sha Alalh babu abinda ya faru mama, Kawu bai San dangin sa ba?.”
Mama tace, “Zakiyya duk waliyan da ya kawo na karya ne, sunan sa dai shine amma komai da yayi amfani dashi na k’arya ne. Ban san a wanne hali Fiddausi take ciki.” Zakiyya tace, “in sha Allah tana cikin kwanciyar hankali, zan saka a bincika in da hali ma zanje har Abuja gidan da aka kaita na dubo na gani.” Mama tace, “anje har gidan, yayar su taje ita da mijin ta har gidan an tabbatar musu da babu mutane a cikin gidan, hankalina ya tashi sosai ban San abinda yake faruwa da ita.”
Chapter 27 · 0% Book details