← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 93

Sashe 16

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aliya ta koma kusa da ita sosai ta rik’e ta tace, “sai dai ki yi hak’uri fa dan zaki ji zafi sosai a hankali zaki dawowa daidai, baza ki iya zama a yanzu ba ki daure ki kwanta zaki samu Lafiya zuwa wani lokaci.” Kuka take yi sosai mai tsuma zuciya Aliya ta rungume ta tana kuka itama dan rayuwar da suke ciki sai dai kawai Allah ya fitar dasu. “Aliya bazan zauna ba, bazan zauna ba Aliya gidan mu zan tafi, bazan iya zama a gidan nan ba walalhi gida zanje. Mutuwa zanyi in na zauna a nan zuciyata zata buga, na hak’ura da komai zan tafi gida.”

Aliya bata ce komai ba domin taga wanda ya shigo yana kallon su duka biyun ganin suna kuka ya saka shi ya tsaya a gefe yana kallon Aliya yace, “ki fad’a mata ta cire ran komawa gida yanzu” ya fad’a yana k’araso inda suke yana kallon su. Aliya tace, “Ka sani Allah sai ya saka mana sai kayi mutuwar wulakanci, sai Allah ya nuna maka sakamakon ka tun a duniya.” Yayi k’aramar dariya yace, “Dani daku za’a ga wanda yake ganin sakamako ai. Ku tun a yanzu kuke ganin naku sakamakon gashi nan duk Kun firgice Kun kasa tsayar da hankalin ku waje d’aya.”

Fiddausi tana kuka ta kalle shi tace, “Allah ya isa ban yafe maka ba wallahi sai ya saka min abinda kayi min. Mugu, azzalumi, d’an neman maza.”
“Ohh! Kin farfad’o daga suman kenan, yayi kyau” ya fad’a yana kallon ta yana wani irin murmushin rainin hankali. Aliya ya kalla itama shi take kallo yace, “ki fad’a mata irin wannan addu’ar kun saba yi min ita tun lokacin baya kafin tazo, ke tun kafin ku akwai wanda suka yi min irin ta babu adadi amma babu abinda ya same ni. Itama ki fad’a mata babu abinda fatan ta zaiyi min sai dai ya k’ara min k’arfi da kuzari.”

Fiddausi tace, “mugu, kaci amanar yardar da nayi maka, ka cuce ni ka yaudare ni, ka lalata min rayuwa ka saka na sab’awa Allah. Ban tab’a tunanin aikata abinda ka aikata dani ba ko a tunani bai tab’a zuwar min ba, Allah ya isa bazan yafe maka ba.” Yayi dariya mai sauti yace, “ke ai amfanin ki bai k’are a wajena ba, dan kaf matan da nake mu’amala dasu banji wacce naji dadin ta kamar ke ba, dan haka zan iya ce miki yanzu aka fara gwara ma ki kwantar da hankalin ki zaki fi samun duk abinda kike so” ya fad’a yana rik’e fuskar ta.

Kwace fuskar tayi fuskar ta duk hawaye taji sosai tace, “kuma wallahi nafi k’arfin ka, baza ka sake sab’on Allah dani ba sai dai kayi duk abinda zaka yi min, in kashe ni ma zaka yi sai ka kashe ni amma wallahi bazan bari ka sake ba. Allah ya isa nan yafe ba kuma sai na bar gidan nan ko baka sake ni ba.”
“Hajiya Fiddausi Kenan, ai daga yanzu har lokacin amfanin ki ya k’are a gidan nan baza ki sake koda waya da kowa naki ba har sai lokacin dana ga damar hakan, amma daga yanzu babu ke babu waya, duk kuma wayar wanda zaki karb’a da niyar sanar da wani babu wanda zaki samu” ya fad’a yana nuna mata wayar ta a hannun sa yayi murmushi yace, “nasan kin haddace lambar mutane da yawa zaki iya Karb’ar wayar wani kice zaki kira su, ina tabbatar miki da duk wayar wanda zaki karb’a baza ki tab’a samun wani naki ba, koda wannan k’awar taki ce baza ki same ta ba har sai lokacin da naga dama sannan hakan zata kasance.”

“Wallahi sai na gudu na bar gidan nan, bazan zauna dakai ba, na tsane ka, bana sonka, bana son mai sonka” Fiddausi ta fad’a tana kuka sosai tana kallon sa. Yayi dariya yace, “nima ba sonki nake ba sannan ba kaunar ki nake ba, dalilin da ya saka na aure ki shi na aiwatar miki jiya kuma shi zan cigaba da aiwatar miki a duk sanda amfanin hakan ya tashi. A banza na saka kika kashe auren ki an fad’a miki? An fad’a miki soyayyar gaskiya ce zata saka na nace ki kashe auren ki Fiddausi?” Yayi dariya tare da tafa hannu yace, “duk kashe kud’in da kashe na yi shi ne akan abinda nayi miki jiya, ban auro ki dan ina sonki ba sai dan ina da manufa a kanki kuma ita nake cimmawa a yanzu.”

“Ke kuma kin aure ni saboda kud’i, mota, babban gida, fita kasar waje. Duk kin samu kuma ko yanzu kika ce min kina son zuwa wata k’asar Fiddausi you’re free to go, zan barki ki je ko ina amma banda Saudia. Duk inda kike so a fad’in Abuja zaki je amma baki isa ki tsallaka titin Abuja ba tare da ikona ba. Duk wani motsin ki ina gani ko ina kika je na sani dan haka taku d’aya baki isa ki yi ba sai ni naso. Abinda kika aure ni dan shi ai kin samu meye kuma kike fatan na sake ki kuma Fiddausi?. Kince kudi shine komai a duniya gashi kina cikin kudi to meye na kuka kuma? . A ganina farin ciki zakiyi domin in kika amince da abinda nake so wallahi ba kud’i ba kud’ad’e zan baki ba.”

Kasa magana tayi sai kuka kawai da take yi tunawa da abubuwan da tace a baya sai zuciyar ta ta karye kuka babu full stop. Ganin hakan ya saka shi yin murmushi yace, “In kuna da ra’ayi a yau din nan zan siya muku ticket ku tafi England, kuna so?.”
“Bama so, ko bango duniya zaka kaimu so, kaje ka k’arata da k’udin haram mu bama so. Allah ya isa bamu yafe ba” Aliya ta fad’a tana kuka sosai.

Yayi dariya ya yace, “Kedai bakya so, amma nasan Fidy tana so ko My Baby?.” Kuka take sosai ta kasa magana balle ta tanka masa yayi dariya kawai ya fita ya barta ba tare da yace komai ba Aliya ta kalle ya tace, “Kinyi kuskuren kashe auren ki kika shigo wannan gidan Fiddausi, Kinyi kuskuren zab’ar kud’i a matsayin farin ciki. Daga shigowa ki wannan gida gashi kin fara tabbatar da kud’i ba shine farin ciki ba, gamu a kud’in a zaune amma ko wanda suke hannun kidnappers baza su sha irin wahalar da muke sha ba” tana fad’a ta tashi ta bar Fiddausi wajan tana kuka kamar ranta zai fita. Dana sani take ji tana mamaye mata zuciyar ta hakan ya saka kukan tak’i tsayawa sai zuba yake kamar an kunna fanfo.

Tunda suka samu sab’ani da Asiya ya fita sabgar ta ko wajan ta baya zuwa sai yaje d’aukar wani abun , a b’angaren Ameena yake zaman sa a d’akin sa ko ta kanta baya bi dan gabad’aya ta fita masa daga rai amma kuma ya kasa yin komai a kanta. Hukunci yake so yayi mata ya d’auki mataki a kanta amma da sun had’a ido sai ya kasa yin komai ya rasa a inda Matsalar take.
A Daren Umma Sakina tazo gidan Asiya a lokacin tana zaune a falo tana kallo daga ita sai d’aurin kirji kai ko dakwali babu ga kitson ya gama tsofewa ba’a gyara ba.

Umma Sakina tana yin sallama ita da Maimuna suka toshe hanci saboda k’arnin falon yake ganin su ya saka ta taso a guje ta rik’e Umma Sakina tana cewa, “Umma Sakina Sannu da zuwa.” Janye ta tayi daga jikin tana k’are mata kallo tace, “Asiya ashe daman duk fad’an da nake miki akan wannan kazantar baki daina ba? Ke kinji yadda kike wari kuwa ga hammatarki kamar kan jariri?.”

Asiya ta zauna tace, “Umma Sakina Ina k’ok’ari ai wallahi, kin San ina da ciki ne shiyasa ba komai nake iyawa ba.” Maimuna tace, “ina y’an aikin naki?.”
“Suna nan, suna gyara gidan.”
“Amma yake wannan k’arnin kamar an zubar da Kwai? K’arnin ma na rasa wanne iri yake yi.” Asiya tace, “kinji Yaya meye yake k’arni a nan dan Allah?” Sai ta tsaya da maganar ta d’aga filon kujera ta tofa yawu ta kalli Umma Sakina tace, “Cikin nan ne baya bari na yin komai wallahi.”

Umma Sakina ta yamutsa fuska tace, “Ai gashi nan na gani.” Asiya ta mik’e tace, “bara na kawo muku ruwa da abinci.” Umma tayi saurin cewa, “A’a nidsi bazan ci ba, ki barshi kawai ba sai kin kawo komai ba.” Asiya ta koma ta zauna tace, “Yauwa Umma daman ina so muyi magana dake, tun fad’an nan da nace miki munyi yau kwana biyu kenan ko shigowa nan baya yi yana b’angaren matar sa, ni abun ya dame ni nayi fushin naga bai zo yana rarrashi na ba.”

Maimuna tace, “A haka zai rarrashe ki kina fama da wari da d’aurin kirjin?.”
“Kinga Yaya babu ruwan ki dani, in ma bana wanka ai jikina ne” ta fad’a ta murgud’a baki. Umma Sakina tace, "Shugabar marasa kunya ta Nigeria, To ya rarrsshe ki yace ya rarrashi wa kenan? matar sa ko kuma k’azama?." zata yi magana ta dakatar da ita tace, "Indai a haka zaki cigaba da zama ba rarrashi ba sake kallon ki ma bazai yi ba. Shiyasa aikin mu baya tafiya mana ashe kece kike daqile komai saboda wannan shegiyar k’azantar taki, ai ko wanne aiki sai da gyara sannan za’a samu abinda ake so.”

Asiya tace, “To ni ya zanyi? Ina iya k’ok’arinw ai.”
“Sai ki yi ai amma ina so ki sani a haka babu maganin da zaiyi miki aiki, domin kuwa baki da wani abun da zai yi marmarin sa, kin lalata komai kin bar komai ya tsofe kamar ba sabon aure ba. Daman nazo miki da wani wanda in zaku kwanta zaki shafa to naga babu amfani dan ko ni bazan iya zaman minti d’aya a a kusa dake ba balle kuma shi da zai jima jikin ku a had’e.”
Chapter 16 · 0% Book details