← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 93

Sashe 45

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Asiya ta d’auke kanta gefe kawai bata ce komai ba ya kalli Adam yace, “To Soja an gama hankali ya kwanta ko?.” Mubakar yace, “Tasan abinda zata dinga satowa zaka ce ba canje ba.” Ta kalli Mubakar da sauri yace, “k’arya aka yi miki? Ba satowar kika yi ba? Yau kika fara?. Garin sace-sacen ki na banza da wofi zaki kai mijin ki gidan yarı ba dan Allah ya kiyaye ba, kina can gıda kina bacci baki damu ba saboda ba ke aka kama ba” ya mik’e tsaye yace, “me ake da mata b’arauniya?.” Abbah ya kalle shi yace, “Mubakar ya isa haka, ku tashi mu tafi bana son wata magana.” Tayi shiru bata tanka ba suka tashi suka yi masa sallama suka tafi aka wuce da Yusuf Asibiti dan sake duba Lafiyar sa. Babu Wanda ya sake magana akan Asiya kowa yayi shiru domin duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa yake duka.

#Mai daki
#Nana Haleema
#Book3
#Paid

Book3
025

Ameena na zaune a falo tana karatu Anti Aisha ta fito ta zauna kusa da ita tace, "y'an boko, ana tayi." Ta kalle ta tayi dariya tace, "wallahi Anti, Bauchi nake so naje gidan Yaya amma wannan karatun bazai barni ba."  Asiha tace, "kuma yana da kyau kije ba tunda ga aure ki nan yana tunkaro ki." Ta rufe littafin ta kalli Anti tace, "nifa ba yanzu zanyi aure ba ku barni na sake hutawa sannan batun aure ya shigo."

Tayi dariya tace, "sai kiyi hutun a gidan mijin ki." Sai tayi dariya tace, "kin San meye Anti? Yaya Al'ameen dariya yake bani yana saka zuciyata nishadi in naji ya dage shi a lallai soyayya yake yi, sai naji ina nishad'i  wallahi dan darıya abin yake bani. Da girman sa wai yace yana sona, dan Allah meye nawa bai sani ba lokacin ina yarinya? Komai da tare suke yi da Yaya amma yace wai ni yake so" ta sake fad'a tana dariya a bayyyane.  Anti ma dariyar tayi tace, "ita soyayya ina ruwan ta da babba da yaro? Kuma wai kwata-kwata nawa yake da kike zancen wai babba?, sa'an Yayan ki ne da kike gani  ko babar y'ar yayan ki bata yi shekara takwas ba har yanzu." Ameena tayi dariya tace, "to ki duba su Yaya mana duk k'annen sa ne kuma ko wacce ta kusa da aurar da y'a, ga Yaya Sumayya nan har an sa  ranar Ummi, ga Yayan Bauchi ma Amira ta kusa aure, kawai shi dan namiji ne."

Anti ta sake yin dariya yace, "naga alama lamarin Al'ameen kin mayar dashi comedy, to shi wanda ya ganki a bikin su Yusuf din fa?." Ameena ta yatsine fuska tace, "shi kuma yayi yaro." Ganin kallon da Yaya take mata sai tayi dariya sosai Anti tace, "kyayi dariya mana kema kin san kin d'auko sabon iskanci ne ai. Wannan yayi girma wannan kuma yayi yaro."
"Allah Anti ni maganar auren nan ma dariya take bani, ba yanzu zanyi ba sai na gama Digree in sha Allah."
"Ai wallahi baki isa ba, yadda mazan auren suke wahala ke kin samu kice baza kiyi wasa ba."

Ameena tayi dariya tace, "za dai mu gani." Sallamar Yaya Adam ya saka suka katse hirar suka kalle shi yace, "Ameena tun daga waje ake jin dariyar ki, me ya baki dariya haka?." Ta sake yin dariyar sai Anti tace, "Wai lamarin Al'ameen ne yake bata dariya wallahi, in yana magana nishadi yake bata, Kaji sabon iskanci dan Allah sai kace tana tare da mai wasan kwaikwayo." Yaya Adam  yayi dariyar shima yace, "Ameena ina ganin ki shiru-shiru ashe kema shak'iya ce." Tayi dariya tace, "babu ruwana Yaya."

Yace, "Yanzu aka sake damuna akan Ana son auren ki." Ta kalli Anti itama ta kalle ta tace, "Kya kalle ni ai, wallahi cikin ukun nan da aka samu dole ki d'auki daya sai ki gama karatun a gidan ki."  Yaya Adam yayi dariya yace, "ina wani gida na farkon layin nan wanda yafi ko wanne girma a layin nan?." Anti tace, "na gane shi, gidan Alhaji Mu'az naji Ana cewa ko?."
"Yauwa nan kuwa, ni na d'auka mai gidan da babba ne wallahi dan yanayin gidan na d'auka na babban mutum ne haka ya ajjiye mata hudu ashe mai gidan ba babba bane bai fi ni ba." Ameena ta kalli Yaya tace, "au kai yanzu ba babba bane ba Yaya?."

Aisha ta dake ta tace, "ya fa ishe ki wallahi." Yayi dariya Ameenan ma dariya take yace, "ki tambayi Al'ameen." Ya sake cewa, "shine yazo yanzu nan dashi muka gama magana na shigo, yana son Ameena yana ganin ta in zata je makaranta ko ta dawo ya tambaya aka nuna amsa nan gidan akace a nan take k'anwar a ce. Yace yana sonki kuma matan sa biyu itace ta uku, dan Allah yana so na bashi dama su tattauna nace ya bani lambar sa ranar dana shirya ya ganta zan kira shi yayi godiya sosai ya tafi."

Anti tayi dariya tace, "Allah Sarki, amma dai ga wanda basu da aure baza mu bawa mai aure ba."  Yaya yace, "to kika sani ko shi zata ji tana so?, abinda na sani kawai zan yi bincike iyakar iyawata har akan Al'ameen din duk wanda ta zab'a cikin su zan bincike shi sosai in sha Allah." Ameena tace, "to Yaya kace sa'an kane kuma yana da mata biyu har zaiyi ta uku, to meyasa kai kake da guda d'aya har yanzu?. Baka ganin sa'anin ka na k'ok'arin yin ya uku?."
"Innalillahi! Wai Ameena kakar ki ce ni?" Anti ta fad'a tana kallon ta tare da tafa hannu sai kuwa ta sake yin dariya sosai harda rik'e ciki dan nishadi take ji dashi a wannan lokacin.

Yaya Adam yayi dariya sosai shima yace, "kuma fa Ameena wannan shawara ce mai kyau, ya kamata a san abinda za'ayi."  Anti dai murmushi itama take yi kafin Yaya yace, "Ameena a bar batun wasa, ina jin fa zaki auren ne in yaso sai ki gama karatun a gidan ki, bana son wannan yazo wannan yazo din nan in aka gama magana guda d'aya duk wanda yazo zance an bada ke kinga yafi. A haka ma akwai wanda in suka zo fuskar magana ce basa samu a wajena dan ni ko shigar kace bata yi min ba baza kayi min wata magana ba. Kinga mai gidan nan na bayan mu? Haka yazo shima wai sonki yake yi matan da uku yaran sa ina jin sunyi hamsin, a tunanin sa dan yana da kud'i zanyi gaggawa nace gaki nan ya d'auka nan take na taka amsa burki har gobe baya iya  had'a ido dani ko a masallaci. Dan haka zan bawa shi Mu'az din dama yazo ku gaisa daga baya sai a d'auki d'aya a tsayar da magana an huta wannan da yazo wannan yazo."

Anti tace, "hakan yayi sosai, in ba haka ba na banza ma wallahi zuwa zasu yi. A haka ma dan suna tsoron kane shiyasa ba'a iya zuwa amma babu damar auren yarinya ya mutu ko wanne banza sai kiga yazo wai yana sonta a ganin su ai bazawara ce nan da nan zata amince." Yaya yace, "Ameena kina ji baki ce komai ba, kina ganin hakan yayi ya cigaba da karatun a gidan ki tunda naga yanzu har kin shiga level two ko?." Ameena tace, "level 3 dai, ka manta direct level two din na samu?."

Yaya yace, "ma sha Allah karatun naki ai yana gudu sosai, kinga end of level three din sai kiyi  auren ki ki huta ko?." Tayi murmushi tace, "duk abinda kace Yaya shi zanyi." Yayi murmushi yace, "to na gode. Ina Zaytun?."
"Tana makaranta."
"İn ta dawo anjima ki shirya ta zamu je asibiti ta duba baban ta bashi da lafiya." Ameena ba tare da yanayin ta ya canja ba tace, "To." Ya kalle ta yace, "ko kema zaki je?." Ta wara ido bata ce komai ba yayi dariya itama haka kafin ta tashi ta shiga cikin d'aki.

              Labari ya baza unguwa Fiddausi ta dawo gida labari ne ya jewa Zakiyya bayan sallar magriba ta shiga gidan nasu ta samu Mama tana wanke zogale. Mama ta kalle ta tace, "A'a Zakiyya kece tafe?."
"Eh Mama, ina wuni?."
"Lafiya lau, kawar taki ta dawo ki shiga tana ciki." Da to ta amss ta shiga cikin d'akin ta hango Fiddausi a zaune akan sallaya tayi tagumi da hannu biyu yana kuka.

Da sauri ta k'arasa kusa da ita tace, "Fidy." Jin muryar Zakiyya ya saka ta d'ago ta kalle ta sai ta sake fashewa da kuka Zakiyya ta zauna kusa da ita tace, "Fidy kece kika koma haka?." Bata ce komai ba sai kuka ta rik'e hannu Zakiyya tana juya kai tace, "Nice Zakiyya, Fiddausi da kika sani ce tayi wannan lalacewar."

Zakiyya tace, "da gaske kenan maganar da nake ji garkuwa akayi dake?." Bata iya bata amsa ba Zakiyya tace, "in badan haka ba a kullum sai na kira ki sau goma amma ban tab'a samun ki ba, komai ya tsaya cak Fiddausi meye faru?."
"Meye ma bai faru ba Zakiyya?, naga isha naga rayuwa, na tabbatar kud'i ba komai bane indai babu kwanciyar hankali." Zakiyya ta sauke Ajiyar zuciya tace, "Nima na fahimci wannan zancen Fiddausi, bani labarin abinda ya faru."
Chapter 45 · 0% Book details