← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 93

Sashe 55

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukayya tace, "babu neman alfarma Fidy Amir zai zo ma in sha Allah." Tayi dariya tace, "Allah ya kawo shi, na gode sosai Rukkya. Daman nasan indai Amir yana tare dake bazai yi kukan rashin  na ba sai dai yayi kuka in na dawo rage shi." Rukayya bata ce komai ba tayi murmushi kawai kafin Fidy tace, "cikin ki ya fito sosai, awo kika je?." Rukayya tace, "eh naje asibiti na biyo gida na gaida Umma, sai na shigo nan,"
"Kin kyauta wallahi naji dadi sosai kin d'auke min kewa. Cikin wata nawa?." Rukayya ta dan kawar da kai tace "ke ni ban rik'e lokacin ba." Tayi dariya tace, "karya kike wallahi kin rik'e." Tayi dariya itama suka dan yi hira kad'an kafin Rukayya tayi mata sallama ta tafi ta bar Fiddausi da sabuwar damuwa da dana sani a zuciyar ta.

Yaya Adam yana dariya yana shiga d'aki Aisha ta kalle shi tace, "to Lafiya dai?." Ya zauna yace, "Al'ameen yana nan zan zauna lafiya ne? Wai bawan Allah nan tashi yayi yaje har wajan k'anin mahaifin sa yaje yace masa ya samu matar aure kuma kanwata ce amma ina so na hana." Tayi dariya  tace, "kai Al'ameen da gaske yake fa." Ya girgiza kai yace, "da shi k'anin mahaifin nasa muka gama waya yanzu yana ta dariya shima yana cewa yasan halin Al'ameen baya son jira ya kasa hak'uri har sai da yaje ya same shi. Al'ameen hmmm" ya fad'a yana girgiza kai.

Tace, "shi gani yake kaine ka hana bai San ta mayar da lamarin sa tamkar comedy ba."
"Iskancin tane da itama tana sane wallahi, a kaf wanda na basu damar ganin ta babu wanda naga tana sakewa dashi kamar Al'ameen din."
"Sakewa daban ai so daban, in ka duba zata sake dashi mana saboda tana ganin sa koda yaushe tare da kai zata ji a ranta kamar kaine tasan bazai cutar da ita ba." Ya girgiza kai alamun haka ne kafin yace, "kafin ya cigaba da tara min jama'a zan same ta muyi maganar hankalin kar kuma ta dinga min wannan dariyar, in ta amince haka nake so in bata amince ba shikenan."

Aisha tace, "Anya zata amince kuwa? Wallahi ta mayar dashi kamar abokin ta."
"Shi yaga zai iya daman ai, ina shi ina Ameena dan Allah?."
"Kaji ka, yana sonta tun ba yau ba akwai aibu dan ya aure ta?." Ya tab'e baki yace, "gashi nan ai tun yanzu ta mayar dashi Kakan ta." Tayi dariya tace, "ba komai duk cikin so ne." Yayi dariya baice komai ba sai daga baya yace, "zan so ayi auren ma kawai kafin tafiya ta dan in lokacin tafiyar yayi tana nan sai dai ku zauna tare naje na dawo bazai yu a barta ita kad'ai a nan ba." Aisha tace, "kai da naji dadi wallahi." Tashi yayi ya fita baice komai ba.

Yusuf ana idar da sallar la'asar yaje gidan Usman a lokacin dawowar sa kenan ya same shi yana cin abinci Yusuf ya zauna yace, "Dan Allah ka gama muje bana son b'ata lokaci." Usman yace, "ka barni da aiki a can a nan kuma kazo kana takura min? Wallahi baka isa ba." Yusuf yayi tsaki ya cigaba da cin abinci ya kalli Yusuf din yace, "baza kaci ba?." Ya girgiza kai alamun bazai ci ba ya zauna yana kallon sama cikin tunani.

Har Usman ya gama ya tashi ya shiga ciki ya fito ya kalle shi yace, "Yusuf muje." Sai kuwa ya zabura ya mik'e Usman ya girgiza kai suka fita Usman yaja motar suka nufi gidan Yaya Adam.

Tunda suka nufi gidan kuma sai guiwar sa tayi sanyi gaban sa ya tsananta fad'uwa daidai lokacin da suke hango gidan Usman ya kalle shi yace, "ya naga ka karaya ne?." Yusuf yace, "bazan iya zuwa ba Usmsn bani da wannan  k'arfin guiwar." Usman yace, "kai kace zaka iya ai ko?."
"Bazan iya ba wallahi."
"Amma kasan haka ka d'auko ni ko hutawa banyi ba muka tawo?, yanzu hakan daidai ne?." Yusuf yayi shiru baice komai ba.

Kallon gidan sukayi a tare sai ga Ameena ta fito daga mota ta shiga cikin gidan da alama daga makaranta take. Yusuf ya kalli Usmsn shima ya kalle shi yaga ya kulle idanun sa sai ya bashi tausayi amma bai nuna ba dan shi ya jawowa kansa ba wani ba. Usman yace, "watakila ma yanzu ta kusa aure, Allah Sarki Ameana na jima ma ban ganta ba sai yanzu."

Yusuf ya bud'e ido da sauri yace, "mai kace dan Allah?." Usman yace, "cewa nayi watakila ta kusa aure, ko baza tayi auren bane ba kake min wani kallo?, kai ba'a yin auren kayi?." Yusuf ya fara girgiza kai yace, "Usman yanzu a gabana kake fad'ar haka?."
"A gaban naka mana, waye d'in ta da bazan fad'a ba?."
"Kasan Adadin abinda nake ji a zuciyata kuwa? Kasan ne nake ji da ka fad'i wannan maganar Usman?."
"Ko fashewa zuciyar zata yi bazai hana ni fadar gaskiya ba, zata yi aure, na fad'a watakila ma ta kusa aure sai me?."

Baya yayi ya kwanta a jikin kujerar yayi shiru zuciyar sa na bugawa sosai hankalin da ya tashi gabad'aya tunanin da bai zo kan Ameena zatayi aure ba sai yanzu da Usmsn ya fad'a, yanzu in Ameena tayi aure ya zaiyi Kenan? In Ameena ta auri wani wanne hali zai shiga kenan?. Usman yaja tsaki yace, "Soyayyar banza da wofi wacce bata yi amfani ba sai yanzu, Kaga malam ni ina da  abin yi tunda baza ka iya shiga gidsn ba sai mu juya" ya fad'a yana kunna motar tare da juya kanta suka bawa gidan baya ya bar cikin unguwar.

Har Akaje k'ofar gidan Usman Yusuf bai d'ago ba sai da Usman yace, "na kai ka gida ko zaka d'auki motar ka?." Yusuf ya d'ago suka had'a ido ganin yadda idanun sa suka ja da fuskar sa sai da yaji tsoro sosai ya bishi da kallo kamar zai magana sai ya fasa yace, "kaini gidan Ammah dan Allah." Usman baice komai ba yayi gaba suka cigaba da tafiya baice komai ba har suka je gidan Ammah Yusuf ya bud'e motar ya fita baice komai ba Usman ya bishi da kallo yace, "kayi hak'uri Yusuf domin kuwa kayi babbar asara a rayuwar ka, sake samun Ameena a karo na biyu ba abu bane na wasa ba. Ka dai bsta hak'urin amma batun dawowar ta ka daina shi ma."

Yusuf yana shiga gidan babu kowa a falon kai tsaye ruwa ya d'auka yana sha a lokacin Ammah ta fito tana kallon shi tace, "lafiya dai ko?." Ya girgiza kai alamun babu komai ya fita ya bishi da kallo tace, "ikon Allah yaron nan gabad'aya ya firgice." A k'asa ya je gidan sa tun bayan da Asiya ta tafi bai sake zuwa gidan ba ya shiga wajan Ameena ya zauna yana sake k'arewa falon kallo.
"Ya zanyi? A ina zan ganta? Me zance mata? Da wanne ido zan kalle ta?." Ya dafe kai yace, "nayi mata abubuwa da yawa, na b'ata mata rai, na saka ta kuka, na dake ta, na zage ta, na cutar da ita. Da wanne baki zan iya cewa tayi hak'uri?."

"Ameena wallahi Ina sonki nasan kin san ina sonki, ki bani dama guda d'aya na baki hak'uri na nemi afuwar ki, Ameena ki bani dama dan Allah Ina so na ganki amma bani da wannan karfin guiwar."
A bayyane yake maganar kuma da k'arfi kamar wanda bashi da hankali, ya tashi tsaye yana zagaye yana so ya samo mafita amma ya kasa ya dunkule hannu ya daki kujera sai kuma ya tsaya cak a a bayyane yace, "Bauchi zanje, dole naje Bauchi wajan Yayar ta ko zata taimaka min wajan bata hak'uri." Yana fad'a ya fita daga falon da sauri ya fita daga gidan a k'asa ya sake komawa gidan Ammah.

D'akin da yake kwana ya shiga y d'auki waya ya kira Usman yana d'auka yace, "zaka raka ni Bauchi gobe?."
"Muyi me?."
"Zaka raka ni ko baza ka raka ni ba?."
"Badan halin ka ba zanje."
"Gobe da safe zamu tafi in Alalh ya kaimu" yana fad'a ya datse wayar ya cillar a kan gado yace, "Ya Allah ka kawo min mafita kafin zuciyata ta k'arasa kumbura ta fashe, kaine kawai zaka kawo min sassauci a cikin lamarina ya Allah. Ya rabbi ka taimaka min ka shiga lamarin nan kar ka barni da kaina ka dafa min ka hana ni zubar da hawaye" ya fad'a hawaye suna fara sakko masa kamar yadda ya zamar masa aboki a wannan lokacin.

#Mai daki
#Book3
#Paid
#500
#Nana Haleema.

Book3
030

Ameena tana shiga gida ta tarar da Yaya yana zaune a falo ta zauna tace, “Yaya yau na gaji” sai kuma ta tashi tace, “yunwa nake ji, bara na zuba abinci na baka labari” ta fad’a tana shiga kitchen yayi murmushi kawai sai gata ta dawo da plate na abinci ta zauna Zaytun ta tawo ta zauna kusa da ita tace, “Yaya kasan a wannan semester ma ban samu carry over ko d’aya ba?.” Yaya Adam yayi murmushi yace, “Gaskiya wannan abun farin ciki ne, kin yi k’ok’ari.”

Tayi dariya tace, “na gode Yaya.” Yayi murmushi baice komai ba har ya gama cin abincin ta sha ruwa sannan tace, “yanzu na dawo hankalina” ta fad’a zata tashi yace, “Ameena zauna.” Ta dawo ta zauna ya kalle ta yace, “meye ra’ayin ki akan Al’ameen? Yana ta karad’e dangi yana cewa ai na k’i bashi ke, meye ra’ayin ki a kansa?.” Tayi murmushi tace, “Ban San me zance ba Yaya.”
“Kin sani Ameena ki fad’a min kawai bana son wasa da hankali ke kin sani.” Ameena tayi Ajiyar zuciya tace, “Yaya ka bani lokaci dan Allah.”
“Shikenan na baki, amma kar lokacin ya jima. Ina so nasan abin da za’a yi ne na gaji da wannan yazo wannan yazo gwara ayi a gama kawai.” Ta d’aga kai ta tashi ta shiga cikin gidan.
Chapter 55 · 0% Book details