← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 93

Sashe 76

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameena tace, “matsalar sa daban taki daban Fidy.”
“Ya tab’a zagin iyayen ki? Ya tab’a zuwa gida gaban Yaya Adam yace baya sonki baya kaunar ki ya gaji da zama dake in aka matsa masa zama dake zai kashe ki?, shi namiji ne dan ya kula wata macen kuna tare ba wani abun bane amma ya tab’a chakumar wuyan rigar ki yace baya sonki sai ya sake ki Ameena?. Duka bai aikata ba, to ki juya laifukan baibai ki mayar dashi mace ya tab’a aikata duk abinda na aikata?.” Ameena tayi shiru bata amsa ba tace, “ki koma Ameena indai kin yarda nayi kuskure kuma na gyara yanzu shima ya gyara, ko dan mahaifiyar sa da yake son ki, ko dan yarinyar da yake tsakanin ku Ameena, ni dai ina bayan ki koma amma abinda kika ga shine daidai shi zaki d’auka.”

Ameena tace, “hmmmm, Rukayya sun dawo kuwa? Bana samun wayar ta” ta fad’a dan ta kawar da waccan maganar. Fidy tace, “ban sani ba walalhi, amma munyi waya ina jin shekaran jiya tace min ko jibi zasu dawo dai na manta.” 
“Zakiyya fa?.”
“Zakiyya ai tunda manya suka shiga maganar Allah ya taimake ta ya hak’ura akan batun cikin, kamar ba cikin halak ba wai sai ta zubar. Amma fa ya dindaya mata sharad’i babu ciki sai nan da shekara ko goma tace min ne ko sha biyu” ta fad’a yana yar darıya kafin tace, “kamar shine mai rayuwa a hannun sa, Allah sarki Kiyya da yake son zaman take tace min na amince Fiddausi.” Ameena tace, “Ko wacce mace dai akwai kaddarar da take fuskanta a gidan mijin ta. Dole akwai ta inda take hak’uri dashi.”

Fiddausi tace, “to hakan zaki saka a ranki ki koma wajan mijin ki Ameena, yana sonki yana son sake zama dake a karo na biyu. Son da yake miki a yanzu wallahi bai yi miki shi a da ba nasan kema kin fahimci hakan. Wani lokacin sai abu ya kubce maka kake gane mahimmacin sa a rayuwar ka. Kamar dai ji d’in, na nayi hak’uri da nice a gidsn ibrahim har yanzu, to ban yi ba ga yadda na samu kaina a ciki.” Ameena tace, “to bacci nake ji sai da safe.” Fiddausi tayi dariya tace, “kiyi ta addu’a kawai.” Ta amsa kawai ta kashe wayar ta ajjiye a gefe tana tunani.

         Washe gari Ameena bata shirya ma zuwa makaranta ba tana zaune a gida bayan Zaytun ta tafi Anty Aysha ta shigo ta same ta tace, “baza ki fito ki ci abinci bane ba?.” Ameena ta kalle ta tace, “yanzu daman zan fito, Yaya ya fita?” Ta fad’a tana tashi suka fito tare tace, “Bai fita ba yana nan.” Suna fitowa yana fitowa shima ya kalle ta yace, “Amaryar Al’ameen.” Tayi dariya kad’an ta gaishe shi ya amsa a yace, “banga kina shirin biki ba fa.” Ameena ta  zauna tace,”ina yi Yaya.”
“K’arya kike babu abinda kike yi banga alama ba.” Tayi murmushi kawai b’ata ce komai ba ta zuba abinci tana ci. Shiru babu wanda yake magana suna cin abinci dukkan su  wayar sa tayi kara ya duba yaga Al’ameen ne sai ya share ya cigaba da cin abincin ka.

Sai da ya gama sannan ya fita ya samu Al’ameen din a gidan sa yace, “sai waya ka ke min Lafiya?.” Al’ameen yace, “baka k’arasa fad’a min abinda ya faru jiya ba, shi nake so na sani.” 
“Wai daman akan haka kake ta kira na na d’auka wani abun ne mai mahimmaci?.”
“Mai mahimmaci ne mana Adam, ita Ameena bata amince da komawa gidan sa ba?.” Yaya Adam yace, “a jiya dai tace  masa yayi hak’uri baza ta koma ba amma daga jiyan yanayin ta ya canja, tana tausayin sa kamar yadda yanzu ni kaina tausayi yake bani. Amma fa ban sani ba ba ita tace min ba kawai ni nace tana tausayin sa.

Al’ameen yace, “nima haka wallahi, bana so ace ta silar hakan ya samu wani babban ciwon ko ace ya rasa ransa ma gabad’aya wallahi. Yanzu na tabbata ba Lafiya yake ba.” Adam yace, “ko meye dai shine ya jawo badan haka ba da yanzu tana gidan sa ai. Kuma shi ba ta silar sa ta samu ciwon ba? Dan ya samu ba komai bane anyi kunnen doki.”
“K’addarar kenan ai, da kuma silar canjawar tasa gabad’aya.” Yaya Adam yace, “Tunda tace bata yi zancen sa ba namu bane, muyi abinda yake gaban mu.” Al’ameen yace, “Nidai inda zata amince da ta koma din, wani zaman jin dadin baya zuwa sai an samu kuskure, kuma ba ko wacce mace bace take komawa gidan mijin da ta bari ta sake tarar da abinda ta bari ba, musamman yadda yanzu yake wahala akan Ameena bazai sake aikata abinda yayi ba na tabbatar maka.”

Adam ya girgiza kai yace, “nima na yarda wallahi, baka ga na zubar da makaman yaqina ba?, har azumin kaffara nayi akan lamarin Yusuf.” Al’ameen yace, “amma tunda muna addu’a gabad’ayan mu Allah zai zab’a mata mata mafi alkhairi.” 
“Wai kai daman baka son Ameena din ne?.” Al’ameen yayi murmushi yace, “ni kuwa nake sonta, amma son da nake mata bazai hana ni fad’ar gaskiya sannan na kuma sanar da farin ciki a rayuwar ta ba, sannan bai hana ni fad’ar abinda yake daidai ba. In Kaga ban aure ta ba daman Allah baiyi ni mijin bane shiyasa take ta kubce min.”

Adam ya girgiza kai yace, “Salon kaje ka cigaba da yad’a ni kace na sake hana ka Ameena a karo na biyu ko?.” Al’ameen yayi dariya yace, “indai hakan ta tabbata Allah ne ya hana ni Ameena ba kai ba wallahi.” Adam ma yayi dariya yace, “to zamu dai ga abinda Allah zaiyi. Mun bar masa zab’i ya zab’ar mata inda zatayi farin ciki.”
Al’ameen ya harare shi yace, “Kai ko Allah bai zab’e ni matsayin mijinta ba ba hakan yana nufin baza tayi farin ciki a wajena bafa, Yauwa ka canja kalaman ka kasan abinda zaka ce.” Adam yayi dariya shima haka yace, “ai gaskiya ne.” Tare suka fito Al’ameen ya hau mota ya fita shi kuma ya koma gıda.

       Ameena ya samu da hijjab a jikin ta ya kalle ta yace, “sai ina kuma?.” Tace, “Class mate din muce bata da lafiya yau kwana uku anje duba ta ban je ba, kuma tare muke komai har karatu nida ita. Tunda yau bazan fita ba sai nace bara ka shigo na tambaya sai naje.”
“Sai kin dawo.”
“Na gode. Nayi driving?.” Ya kalle ta sai yace, “ki dawo da wuri.” Ta masa ta fita da murna dan har kewar jan mota take yi.

       Asibitin taje ta duba y’ar ajin nasu ai kuwa taji dadin zuwan ta sosai itama Ameenan yaji dad’i ta fito daga d’akin sai ta hango Mubakar a tsaye ya juya baya ga Ammah a zaune ita da wata mata suna magana duk sun juya baya. Murmushi yayi yace, “Da rabon zamu gaisa da Hajiya Ammah” ta fad’a tana k’ara sauri dan yaje inda suke.

Magana Amma suke yi da matar  tana cewa, “Haka Yusuf ya koma shine baki fad’a min ba? Ki kalle shi fa dan Allah kamar ba shi ba.” Ammah tayi dariya tace, “ciwon nasa ne yaje ya dawo, a kwanakin nan ina jin kwanciyar sa a asibiti na hud’u kenan shiyasa bana fad’awa kowa wallahi.” Matar tace, “ai lalura ce, suma sauran y’an uwa suka ji baza suji dad’i ace baki fad’a musu ba. Amma ne yake damun sa haka wai?.”
“Damuwa ce wallahi, itace take saka masa wannan ciwon kan da ko haske ba’a kunnawa in ya tashi, ga zazzab’i mai zafi wani lokacin k’ank’ara ake b’arewa ana zuba masa a jikin sa.”
“Wannan wacce irin damuwa ce haka?.”
Ammah tace, “hmmm! Yusuf fa ni wallahi na fitar da rai dashi, lokaci kawai yake jira Allah ya karb’i kayan sa. Yau ciwo gobe Lafiya a haka ake rayuwa dashi, Tunda asirin wannan shegiyar Asiyan ya fita daga jikin sa shikenan kuma sai hankalin sa koma wajan matar sa ta farko. Shikenan fa ake tayi abu kamar zugi kullum babu cigaba.” Ta zaunen tace, “Ameena kenan, mai hankalin nan.”

Ammah tace, “ita kuwa. Shikenan ya koma kamar mahaukaci, Kullum a kuka yake, Kullum a tunani Kullum a ciwo yake. Ya rasa inda zai saka ransa yaji dad’i, tun bama tausayin sa har ya kai ya yanzu tausayi yake bani, tun ban yarda ya gane kuskuren sa ba ta kai ta kawo yanzu na amince wallahi, na tabbatar bazai sake kuskuren da yayi a baya ba amma sai dai lokaci ya k’are masa Murja. İn Allah ya baka dama kayı amfani da ita a lokacin, shi sai yayi wasa yanzu kuma damar ta kubce masa shine ya koma haka.”

Murna din tace, “Wai Yaya Hafsa daman akan Ameena ya koma haka?.” Ammah tace, “akan hakkin tane da kuma soyayyar ta.”
“Amma wanne irin so yake mata haka da ya mayar dashi wannan yanayin?.” Ammah bata ce komai ba ta tab’e baki Murja din tace, “to baza mu ce komai ba dan kamar yadda kika ce ta kubce masa, dan yayi asarar mata mai hankali da nutsuwa ga rik’e sirrin miji, sake samun ta a yanzu zai masa wahala sosai gaskiya, dan irin su basa jimawa ake aurewa, balle bata kyakykyawa…ina Yusuf yayi sake.” Ammah tace, “shiyasa nace miki lokaci yake jira, domin ni na tabbatar ana cewa Ameena tayi aure to Yusuf kuma sai abinda Allah yayi dan abinda yake fad’a da gaske zai iya rasa hankalin sa, in kika duba yanzu abin kamar ya tab’a masa kwakwalwa shiyasa Kullum a ciwon kai. Amma babu ruwana a maganar nan, in Ameena taga zata dawo wajan sa haka nake so a raina amma a wani b’angaren bana so dan kar ya sake abinda yayi.”
Chapter 76 · 0% Book details