Sashe 44
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa yayi shiru a falon babu maganar wanda yake magana kowa jikin sa yayi sanyi sosai kikan ta kawai ake ji tace, “duk abinda kace na aikata Abba, amma wallahi nayi badana nayi dana sani domin na banbance tsakanin kud’i da kwanciyar hankali Abba. In na koma kashe ni zaiyi bak’in ciki zai iya silar bari na duniya.”
“Ai sai kin koma, baki gama ladaftuwa ba har yanzu Fiddausi dole ki koma kije ki cigaba da rayuwar jin dad’i mu ki bar mu muyi rayuwar wahala da talauci a nan.” Ta rud’e ta gigice tayi wajan Mama tace, “Mama ki bashi hak’uri, Yaya, Kawu ku taya ni bashi hak’uri nayi kuskure amma dan Allah kar yace sai na koma, in na koma da gawata za’a dawo gidan nan.”
Abba yace, “sai me in an dawo da gawar taki? Ai bake kad’ai na haifa ba ina dasu da yawa dan na rasa ki bazan ji komai ba. Baki da d’a ko y’ar da zan tausayawa in akace babu ke a duniya. Babban abinda yake bani takaici dake bai wuce karyar da kika shirya kika fad’a mana akan mijin ki ba, ashe plan kika shirya duk akan burin ki kashe auren ki ki tafi gidan masu kud’i. Tashi ki koma baza ki zauna a gidan nan ba, bazan zauna da matar dan luwadi a gidana ba, ko da yake kema kin zama shi ai bazan zauna dake ba ki tashi ki koma can ki yi rayuwar ki mu ma muyi tamu.”
Kawu yace, “Haba Yaya, dan Allah ka daina wannan maganar tayi laifi kuma ta tuba in da wanda za’a yiwa hukunci nine ba ita ba. Hannun ka bazai rube’e ka yanke ka yar ba.” Abba yace, “sai dai in bai dame ka da ciwo ba, in ya dame ka lokacin da zaka yanke ka cire ka y’ar ma baka sani ba. Na fad’a mata ta bar gidan nan kafin na dawo kar na same ki a nan” yana fad’a ya fita Mama ta tashi tabi bayan sa ta same shi a d’aki tace, “Alhaji nasan ka tausayawa Fiddausi dan Alalh ka yafe mata. Wannan fad’an da kake mata zai iya jawo mata wani sabon ciwo, kasan ance jinin ta ya hau in aka mata irin haka wallahi sai zuciyar ta ta buga.”
Ya juyo ya kalli Mama yace, “in na tuna abinda ta aikata ina bak’in ciki, ina bak’in cikin abubuwan da tayi a baya kawai saboda wani buri nata na banza da wofi. Haushi nake ji in na tuna yanzu tsohon mijin ta yayi mata nisan da baza ta tarar dashi ba, duk uban da ya samu siriki kamar sa farin ciki yake yi baya so yaga yarinyar sa ta fita daga gidan sa amma ita ta k’arfi da yaji ta fita banda rashin kunyar da ta dinga yi har iyayen sa bata kyale ba. To me zata zauna tayi a nan? Ta koma can take ta cigaba da rayuwar jin dadin da ta zaba matsayin farin ciki.”
Mama tace, “na sanabinda kake ji Alhaji, amma kayi hak’uri akwai hakan da kake fad’a kuma akwai k’addara dole hakan sai ya faru.”
“Wannan ba k’addara bace ganganci ne, yanzu kika sani ko ya saka mata wani ciwon.”
“Kayi hak’uri dai ka yafe mata dan Allah.” Yayi shiru baiyi magana ba tace, “ka daina cewa ta koma ka yafe mata dan Allah mu barta a nan.”
“Da aure a kanta har yanzu shi muyi ya dashi?.”
“Za’a San abinda za’a yi ko zuwa gaba in sha Alalh. Amma dan Allah ka yafe mata.” Yayi ‘karamin tsaki baice komai ba ya fita Mama ta bishi da kallo ita kanta zuciyar ta tayi rawa sosai.
Lokacin da ta koma Fiddausi take basu labarin komai da ya faru har kama ta din da akayi a New York sai da ta fad’a, su kansu y’an uwan ta kuka suke dan sun tausayawa mata sosai. bayan ta gama basu labari tace, “nayi dana sani kuma na tuba na gane kwanciyar hankali daban kudi daban, na gwammace gidan da babu ci ko sha nake a zaune indai hankalina zai kwanta. Kwanciyar hankali ke kawo jin dad’i ba kudi ba na yarda.”
Mama tace, “daman a gaske akwai masu irin wannan rayuwar?.” Wacce take bin Fiddausi tace, “ko an american film ban tab’a jin wannan kazantar ba, lallai addu’ar da aka saka ana yi miki daga nan Allah ya amsa kika gudo da ba’a San a inda abun zai tsaya ba. Watakila ma ya bada jinin ki ayi tsafi dashi.” Shiru kawai bata ce komai ba amma zuciyar ta zafi take yi. Danasani, nadama, ina ma banyi ba, sun taru sun yi mata yawa a zuciyar ta, ta rasa me zatayi taji daidai a zuciyar ta da jikin ta, ta rasa farin ciki gabad’aya a ko wanne bangare na rayuwar ta.
Yusuf yana zaune akan kujera ya dafe kansa an office din su Abbah dasu Abie su Adam duk suna zaune a wajan Oga yace, “Yusuf akayi aka samu cocaine a motar ka?.” Yusuf da yake cikin rashin lafiya yace, “ban sani ba, yadda aka ganta nima haka na ganta amma ban San taya ta shiga ba.”
“Wa ka bawa motar taka ya hau kafin kai?.” Yusuf ya dan yi shiru aka sake cewa, “an ina ka ajjiye motar?.”
“a gida.”
“Baka ajjiye ta a ko ina ba? Ka tuna wa ka bawa motar sannan a ina ka ajjiye?.”
Yusuf yace, “direban gidana Sani ya fita da matata a cikin motar, dan ko da naje gida ba a ita nake ba ban hau ba sai da safiyar.” Oga Muhajid ya kira waya ya bada umarnin aje a kawo Sani. Adam yace, “ba iya Sanin ba har matar ai tana cikin motar.” Yayi dariya Abba ma dariya yayi yace, “banda abin Adam ina mace ina wannan harka.”
Oga yace, “suna yi alhaji wallahi suna yi, sai kaga mace da ciki ka d’auka d’a ne a ciki ashe cikin kwaya akayi mata ciki dan a b’atar da hankalin mutane daga kanta.” Abbah yace, “kai amma lamari ya b’aci.” Ya kalli Yusuf tace, “wa kake zargin zai ajjiye maka a cikin motar ka?.” Ya girgiza kai yace, “Gaskiya babu.” Ya girgiza kai yace, “za’a san abinda za’a yi in sha Allah.”
Sani aka shigo dashi aka zaunar dashi ya kalle shi yace, “Malam Sani kaine direban gidan Yusuf?.” Ya daga Kai yace, “kwarai nine.”
“Kwana biyu da suka wuce ka d’auki matar sa Kun fita da ita a motar ina kika je?.”
“Wajan biki na kai ta.”
“Sai ka bar motar an ina?.”
“Ina ciki babu inda naje.”
“Babu wanda suka tsaya a motar aka dan yi hatsaniya ko wani abun?.”
Sani yace, “eh to, gaskiya anyi.” Yace, “Meya faru?.” Ya kalli Yusuf ya kalli wanda yake masa tambayar yace, “Hajiya ce ta fito da sauri tana cemin na kunna motar ta shiga da gaggawa kafin mu tafi wasu mata da wani namiji sun zo wajan kamar zasu daki motar ana cewa a kamo ta ta had’a harda kayan ta sace ni kuma a lokacin ina motar muka tafi. Muna tafiya ta bud’e abinda ta fito dashi sai naji tayi tsaki ta cillar da jakar ta window tana juya wata Leda a hannun ta sai kuma ta ajjiye tace, aikin banza babu komai sai hoda daga nan tayi shiru muka cigaba da tafiya.”
Ya girgiza kai yace, “in na fahimce ka ina its Hajiyan ce ta sato jakar da hodar take ciki, da ta duba taga babu kud’i ko wani abun a ciki sai ta yar a motar.” Yace, “haka aka yi, bayan wannan ba’ayi komai ba gaskiya ban kuma tsaya ko na fita daga motar ba.”
Ya kalli Yusuf yace, “matar ka muna son ganin ta a wajan nan.” Baice komai ba Abbah yace, “a tura a d’auko ta.” Nan take aka yi waya aka gida mace da na miji du tawo da Asiya. Suna zaune babu wanda sake magana sai Ogan da ya fita ya dawo ba jima wa sosai sai ga Asiya a shigo da ita.
Zama tayi ya kalle ta yace, “Kin San wannan?.” Ya fad’a yana nuna mata Yusuf. Ta daga kai tace, “na San shi.”
“Wannan fa?”. Ya nuna mata Sani ta kalle shi tace, “shima na San shi.”
“Kwana biyu da suka wuce ya kai ki biki a motar mijin ki hana ne?.”
“Eh haka ne.”
“Kin d’auki wasu kaya har mutane suka biyo ki da kika duba a motar kika ga ba abinda kike so bane a ciki sai kika cillar anyi haka?.” Asiya tace, “eh, amma ni ba d’aukar kayan nayi ba kuskure ne nayi da jakar na d’auka tawa ce.”
“Me kika gani a ciki kika yar?.”
“Wata hoda ce fara a cikin Leda sai na yar kawai.”
“Kin San meye a ciki?.”
“A’a.”
“Kin San cocaine?.” Ta zaro waje tace, “na dai ji ana fad’a amma ban sani ba.” Ya girgiza kai yace, “to itace kika yar a cikin motar.”
Kafin tayi magana yace, “zaki gane masu jakar da kuka yi canjen?.”
“A’a bazan gane ba” ta fad’a tana kawar da kai gefe. Ya girgiza kai yace, “Alhaji zaku iya tafiya gabad’aya ku amma dan Allah a kula in za’a shiga mota a dinga duba ko ina dan kana tare da makiyin ka naka sani ba wani zai iya ajjiye maka dan ya tozarta ka.” Abbah ya girgiza kai yace, “Gaskiya ne.” Ya kalli Asiya yace, “ki san abinda zaki dinga d’auka ko da yake ki san irin jakar da zaki canje da ita, a dinga kula in ba haka ba wata ran zaki kai kanki kurkuku.”