← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 93

Sashe 34

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbah yana zaune a dashi da yaran sa kaf harda jikoki ana ta lissafin wanda ba’a kaiwa katin d’aurin auren Humaira ba, Abbah yace, “ku dai tuna dan Alalh bana son korafin ban bada kati ba. Gwara a tuna Wanda ba’a kaiwa ba a kai dan Allah.” Mubakar yace, “nidai wanda na sani duk na rubuta an kuma kai musu kati, sai dai ka kira Yusuf akwai wanda ya sani wanda ni ban san su ba.”

Abbah yace, “Gaskiya ne, ban san ma inda ya tsaya ba mun yi dashi zai zo nan din yace min yaje store shiri bai k’araso ba” ya fad’a yana d’aukar waya da niyar kiran sa.” Wani kiran ne ya shigo wayar Abbah yace, “to DPO kuma?.” D’aukar wayar yayi ya saka a kunne yace, “Dpo barka da rana.” Daga can b’angaren yace, “Barka dai Alhaji, ya shirye-shiryen biki? An kawo iv ai nace ashe abun har yazo.”
“Wallahi yazo yanzu haka maganar katinan nake yi.”
“Allah ya kaimu ya sanya alkhairi.”
“Amin.”

Yace, “Alhaji Yusuf aka kai station na bompai babar matar sa tana k’arar sa akan ya daki y’arta har d’an da yake cikin ta ya mutu, yanzu akayi min waya daga can aka fad’a min dan yace ya sanni tunda ba station dina aka aji da case din ba.” Abbah yace, “Subahanallahi, yaushe akayi hakan?.”
“Yanzun nan ne, ba shiri muke da DPO din can ba shiyasa ban neme shi bama na Kira ka na sanar dakai nasan baza ka rasa sanin sa ba, aje ayi magana dashi dan babar matar tace ita kotu take so a kai case din tsaf kuma zai aika kotu din.”

Abbah yace, “to na gode sosai yanzu zan tura Sulaiman yaje a San abinda za’ayi.”
“Yauwa ayi hanzari aje kafin wani abun ya faru.” Sallama sukayi Abbah ya kashe wayar ya kalli kowa da yake kallon da yace, “Wai Yusuf aka kama yana station na bompai.” Yaya Sulaiman yace, “Wanne Yusuf din?.”
“Akwai Yusuf din da ya wuce wanda yake gidan nan?.”

Ammah tace, “Akan me aka kama shi?.”
“Wai Babar matar sace tayi k’arar sa ya daki y’ar ta dukan da yayi silar mutuwar abinda yake cikin ta, ita kotu take so kai maganar kai tsaye.” Ammah tace, “shi kuwa yana da hankali? Dukan mace mai ciki har d’a ya mutu?. Wanne irin duka yayi mata haka?.” Abbah yayi karamin tsaki kawai yace, “Hankali ne dashi? Waye ya fad’a masa Ana dukan mace ma? Matar ka ka dinga dukan ta dan hauka da rashin hankali?. Babana dakai da Mubarak ku tashi kuje can sai ayi abinda za’a yi sai ku had’a ni da shi Dpo din a waya.”

Yayan Abuja tayi tsaki tace, “Wai Yusuf aka kama, ji wani abun haushi dan girman Allah. Gabad’aya ya zubar da dajarar sa tunds ya auro yarinyar nan mai halin b’eraye shikenan ya zama gashi nan dai kawai, yau ana nan gobe Ana can.” Babu Wanda yace komai Abie da Muabakar suka tafi dan jin yadda abun zai kasance a can amma kowa zuciyar sa babu dad’i dan wannan ba mutuncin dangin su bane.

Lokacin da suka je a cell suka tarar da Yusuf Abie ya kalle shi sai kawai yayi tsaki ya wuce zuwa wajan Dpo din ya jima kafin azo a fitar da Yusuf a shiga dashi office din. A nan ya samu Umman su Asiya a zaune ita da Fauziyya ya zauna Dpo din ya kalli Umma yace, “Hajiya Gashi ya fito, abinda nake so a bar maganar nan akwai duba da shi din sirikin kine tozarta shi tamkar tozarta yar ki ne. Babu riba in kin Kai shi kotu ko babu komai za’a ce sirikin ta ne kuma ta kai shi kotu.”

“Saboda su masu kudi ne ko? To bazan iya hak’uri ba kotu nake so aje sai an karbarwa y’ata hakkin ta na abinda yayi mata. Ai ya san tana da ciki yake dukan ta, yanzu abinda yake cikin ta ya mutu watakila shine kawai jinin ta da zata gani a duniya amma yayi silar mutuwar sa. Tana can a a kwance asibiti ba lafiya sboda dukan da yayi mata ace kuma a bar maganar? Bazai yu ba ai ba ni nace yasha giya ba da zai dinga jibgar ta kamar jaka ba.”

Ya kalli Umma yace, “Hajiya a gaban hukuma kike ya kamata ki saita harshen ki ki san kalaman da zasu dinga fitowa daga bakin ki.” Ya kalli Yusuf yace, “Yusuf da ilimin ka da hankalin ka me ya kai ka dukan mace mai ciki kuma matar ka?.” Yusuf yayi shiru baice komai ba sai Dpo ya sake cewa, “Yanzu dai sulhu za’ayi wannan hayaniyar bata kamaci dangi kamar ku ba, mata da miji ace kuma babar mata na k’arar mijin y’ar ta abun ai sam baiyi dad’i ba.”

Ya kalli Umma yace, “Hajiya ki yi hak’uri an san anyi ba daidai ba amma ki janye batun zuwa kotu akan maganar nan, ayi maganar iya nan wajan a rufe ta kowa ya tashi tunda dai matar sace shima kuma mijin tane, duk yadda akayi wani b’acin ran ne ya jawo yayi mata haka ai a akwai sab’ani tsakanin ma’aurata ko?.”

“Ranka ya dade sab’ani ai ba hauka bane da zai mata dukan da sai da abinda yake cikin ta ya mutu, yanzu in da itama ta mutu haka za’a ce nayi hak’uri kenan?.” Dpo yace, “ai bata mutu din ba Allah ya kare, a bar maganar nan tunda dmaan ta gıda ce ba ta hukuma ba.”
“Za’a bar maganar nan amma ai ya biya diyar ran dan da ya mutu.”
Yayi dariya ya kalle ta dan yaga alama tana da son kud’i ba kuma mutunci ne da ita ba yace, “kin san nawa ne diyar rai da kike cewa a biya?.” Umma tace, “Yana da daraja kenan tunda har ka tabbatar da yana da tsada diyar sa dan haka ko a biya ko naje kotu.”

Dpo yace, “Hajiya babu batun zuwa kotu magana za’a gama a rufe ta anan tunda mijin tane in kin kai shi k’ara babu riba.” Umma tayi shiru kafin ta tausasa murya tace, “fisabinillahi ace yarinya mai ciki mijin ta ya dake ta har abinda yake ciki ya mutu wannan darajar miji ce? Ba yau ya saba dukan ta ba amma tunda tana da ciki kamata yayi ya anada dukan nasa ya bari ta haihu sai y d’ora daga inda ya tsaya. Haka kwanaki ma ya dake ta aka tabbatar mana da cikin ya kusa fita nayi hak’uri na bar maganar yanzu kuma ya sake, wannan daidai ne?.”

Dpo yace, “Gaskiya bai kyauta ba.” Umma tayi shiru bata ce komai ba ganin hakan ya saka yace, “Yanzu dai ki yi hak’uri tunda mijin tane komai ya wuce Allah da ya basu cikin zai sake basu nan gaba, magani da komai daman a wuyan da yake dan haka kiyi hak’uri a bar maganar nan haka.” Ya kalli Yusuf yace, “ka bata hak’uri dan baka kyauta ba.” Yusuf yayi shiru bai ce komai ba bai ma kalli Umman Umma tace, “ka gani bazai bada hak’uri ba, da nasan haka za’a yi fa bazan kawo case din nan wajan nan ba wallahi. Wani wajan zanje daban inda nasan za’a yi min abinda nake so.” Abie ya kalli Yusuf suka had”a ido sai Yusuf yace, “Kiyi hak’uri.” Ta zabga masa garar tace, “haka kazo har gida kace baza’a sake ba sai gashi a sake abun yayi gaba ma fiye da baya. Ranka ya dad’e ina so ayi rubutu kowa ya saka hannu indai ya sake dukar min yarinya wallahi sai maganar nan taje gaba.”

Shi dai mamaki ma yake yi a ina suka samo wannan sirika masifaffiya wacce bata girmama masu matsayin sirikai? Sai a lokaci ya tuna ya Santa a kwanaki yayi case da ita kuma itace tayi nasara shiyasa ta kawo abun gaban sa amma baice komai akayi rubutu kamar yadda tace aka bar copy d’aya a hannun dpo d’aya a hannun ta tace, “Gashi nan ya saka hannu in ya amince.” Dpo yace, “Yusuf ka saka hannu.” Babu yadda ya iya haka ya saka hannu akan rubutun bazai sake dukan Asiya ba sannan aka sallami case din. Umma na fita daga office din Dpo kalli Abie yace, “A ina kika samo wasa nan matsayin sirikai? Na San matar bata da mutunci daga ita har y’ay’an ta bata ganin darajar kowa , Yusuf ne ya kai ka hada zuri’a da wad’annan dan Allah?.”

Abie yace, “Sakyya ce da rashin jin magana.” Dpo yace, “yanzu badan kazo ba inda wani wajan takai case din nan sai yayi prison fa dan ba abu bane na wasa, dukan mace mai ciki har d’an ya mutu in badan Nigeria ba Wallahi duk da mijin tane wannan ba abu bane da za’a barshi. kaima bai kamata ka daki mace mai ciki ba wannan ba dabi’a mai kyau bace ba Yusuf. Yanzu gashi da mutuncin ka dana ahlin ku an d’auko ka an kawo ka nan da sunan ana k’arar ka. Ina dad’i a wannan lamarin dan Allah?.” Abie yace, “bari kawai, Allah ya kyauta kawai za’a ce” ya fad’a yana tashi tsaye suka gaisa tare da yin sallama suka fito.

A lokacin sallah ake sai da suka yi azahar sannan suka wuce zuwa gida. Suna shiga falon Ammah ce da Yayan Abuja ganin harda Yusuf ya shigo suka kalle shi Yaya tace, “An Sako shi kenan.” Mubarak ya tab’e baki yace, “Allah ya raba mu da sirikan banza wanda zasu tozarta ka a idanun jama’a, wai sirika ce zata kai k’arar sirikin ta saboda lalacewa” yana fad’a ya wuce Yusuf baice komai ba yana tsaye har lokacin sai kuma ya waje ya zauna a kusa da k’afar Ammah kawai ya kwantar da kansa a k’afar ta amma baice komai ba.
Chapter 34 · 0% Book details