Sashe 57
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Usman yace, “Yaya ba iya hak’urin yake so ba har bikon aure ya yake yi a karo na biyu.” Yaya ta girgiza kai cikin mamaki tace, “bikon auren ta kuma Yusuf? Yanzu tsakani da Allah kana da idanun da zaka sake kallon Ameena kace zaka aure ta a karo na biyu? To wanne kalamai zaka yi amfani dasu da zai saka ta amince da abinda zaka ce mata?.” Yayi shiru baice komai ba tace, “Kar ka manta yar mahaifinta ka yiwa alqawarin rik’e ta amma ka kasa, kazo nan kace min daga wannan ranar baza’a sake jin kanku da Ameena ba ka kasa sai abinda yayi gaba, yanzu kuma kana ganin Yaya Adam zaka yiwa alqawarin rik’e Ameena?” Tayi rmurmushi tace, “Yusuf Tsakani da Allah kayi wasa da damar ka, sake samun wannan damar abu ne mai wahala gaskiya, zancen da nake maka ma Ameena tana gab da yin aure shine wanda Amira take cewa Ameena ta Al’ameen ce. Hak’uri dai zaka iya zuwa ka bawa Yaya zai saurarre ka haka itama amma zancen mayar da auren ka da ita ka ajjiye shi gefe ko Yaya Adam baya raye Ameenan da ka sani a baya ba itace a yanzu ba, sai dai hak’urin zata hak’ura kodan Zaytun da take tsakanin ka da ita amma zancen aure Yusuf ka goge shi daga zuciyar ka, ba Yaya Adam ba ko ni bazan bari ta koma gidan jiya ba.” Yanzu rayuwar ta tayi kyau tayi k’iba ya dawo hankalin ta bazan sake mayar da ita inda zata sha wahala ba.”
Yusuf kansa yana k’asa hawayen da baya so su zuba a wannan lokacin ne suka fara sauka daga idanun sa Yaya tana kallon saukar su a shaddar jikin sa sai gaban ta ya fad’i ta sake kallon sa ta tabbatar kuka yake yi Usman ya kalli Yusuf ya kalle ta yace, “yayi kuskure nima na fad’a masa, yayi sake ya kuma yi wasa da damar sa wacce ta kubce masa a yanzu.” Yusuf ya d’ago ya kalle ta yace, “wallahil azim wancan Yusuf din da wannan Yusuf din da banbanci Yaya, a sake bani dama ta biyu wallahi bazan yi wasa da Ameena ba, bazan sake aikata duk abubuwan dana aikata a baya ba. Na gane kuskurena zan kuma gyara nayi alqawarin Ameena baza ta dake zubar da hawaye akan zama dani ba, ki taimaka min Yaya ki shige min gaba zuwa wajan Yaya bani fa k’arfin guiwar tunkarar sa zuciya ta tayi rauni sosai, ki taimaka min wallahi na rasa na Ameena a wannan lokacin zan iya rayuwata gabad’aya.”
Yaya ta kalle shi tace, “ikon Allah Yusuf bani da damar da zan sake baka Ameena a karo na biyu, sai dai kaje wajan Yaya ta inda aka hau ta nan ake sauka ai. Shine yaje har gida ya dawo da ita shine kuma zai mayar da ita in yaso, amma wannan magiiyar da kake min ka daina babu abinda zan iya.”
“Ban san ta wacce hanya zan tunkare shi da maganar ba, ki taimaka min dan Allah wallahi nayi alqawari abinda ya faru a baya bazai sake faruwa ba wallahi,.” Yaya ta rasa abinda zata ce ga shi a gaban ta yana kuka duk sai ta damu kukan ne bata so sai tace, “Yusuf in nace maka zanyi wani abun a akai k’arya nake wallahi, kawai kaje kayi abinda kake ganin zaka iya amma ni bani da abinda zan maka gaskiya.”
Usman yace, “gaskiya ne Yaya, iya sauraron mu da kika yi ma Mun gode sosai wallahi.” ya kalli Yusuf yace, “wajan Yaya Adam ya kamata kaje ba nan ba, abinda take fad’a gaskiya ne can ya kamata kaje ba nan ba dan a can Ameena take.” Ya kalli Usamsn zaiyi magana yace, “Hakan za’a yi Yusuf.” Usman ya kalli Yaya yace, “Yaya zamu wuce yanzu.”
“Da wuri haka? Kun k’in cin abinci.”
“Babu komai wallahi mun gode.” Yusuf ya kalle ta bayan ya goge idanun sa yace, “Wallahi a wannan lokacin babu damuwa a zamana dani, duk inda kuskurena yake na gano shi kuka wallahi zan gyara.”
Yaya tayi murmushi tace, “Allah ya baka iko, kaje ka same shi shida ita su zaka sanar da haka bani ba Yusuf.” Tashi sukayi tsaye sukayi Yusuf yana goge idanun sa susman ya d’auko kudi ya ajjiye yace, “Gashi Yaya a bawa yara.” Yaya tace, “dan Allah d’auke Mun gode basai ka bamu komai ba.” Usman yace, “ni na bayar ai ba Yusuf ba Yaya, dan Allah ki karb’a.” Murmushi tace, “To na gode.” Daga nan suka yi sallama suka tafi ta bisu da kallo.
Yana fita Yaya ta girgiza kai tace, “Yusuf da kuka akan Ameena? Ikon Allah.” Sai kuma tayi dariya tace, “zuwa wajan sa ma ka kasa ina ga tunkarar sa da wannan maganar Yusuf? Lallai kana tare da wahala dan abinda kake nema baza ka samu ba” ta fad’a tana shiga wajan Amira dan ya ja mata kunne akan abinda tayi.
Sai da suka yi sallah Usman yaci abinci dan shi dai Yusuf bai iya cin abinci ba yana zaune har Usman ya gama ci suka shiga mota suka d’auki hanyar kano Yusuf ya kasa magana sai tunani.
A haka suka shiga kano kamar kurame kafin lokacin Zazzabi ya gama rufe Yusuf amma bai ma fad’awa Usman ba yana sauke shi gida ya shiga shi kuma ya wuce yana tausayin sa dan yasan abinda yake so bazai samu ba. Yana shiga falon Ammah ya tarar da ita a zaune ta kalle shi tace, “kai kuma ina ka shiga yau ban ganka ba?.” Yusuf yace, “naje wani waje ne, bana jin dad’i zan shiga na kwanta” ya fad’a yana wucewa ta bishi da kallo kafin ta cigaba da abinda take yi.
Rukayya tana zaune bayan sallar magriba tana so ya shigo tayi masa maganar Amir dan ta daure zata yi masa a wannan a lokacin, tana so tayi masa amma sai ta kasa saboda bata son b’ata masa rai akan maganar amma yau kam tayi alwashin fad’a. tana zaune ya shigo da leda a hannun sa ya k’araso ya ajjiye a kusa da ita yace, “Nama ne in zaki dafa yanzu zo in kuma sai gobe sai ki saka a fridge.” Ya zauna tace, “To an gode. Sannu da zuwa.”
“Yauwa, nayi sallah ne shiyasa sai yanzu na shigo.”
“Naga alama ai” ta fad’a tana tashi ta d’auki ledar ta bud’e ta saka a fridge ta shiga kitchen din ya d’auko abinci ya kawo ya ajjiye ya kawo ruwa ma ta ajjiye ta zauna yace, “ina Amir?.”
“Tunda yaci abinci yayi sallah sai yayi bacci tun d’azu.” Ta zuba masa abincin ya fara ci tace, “D’azu Yaya Hadiza tazo, ta kawo mana awara gata can ma a fridge sai gobe sai mu soya.”
“An gode.” Ya fad’a a takaice yana cin abincin. Sai da ta bari ya gama ya sha ruwa ya tashi ya shiga d’aki. Tashi tayi itama ta shiga nata dskin tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta bacci ta saka hula a kanta ta fito taga duk ya kashe komai na falon da alama bacci zaiyi ta shiga d’akin ta same shi a zaune a gefen gado.
Zama tayi tace, “yaushe ne tafiyar tamu?.” Ya kalle ta yace, “ranar asabar ne da safe.” Tayi murmushi tace, “Allah ya nuna mana, Allah yayi dai dsni za’a ce umrah nan.” Murmushi yayi kad’an kawai baice mata komai ba tace, “jiya naje gidan su Fiddausi da naje gida.” Ya d’ago ya kalle ta ta k’asan ido yace, “kin kyauta.”
“Khalil daman wata magana nake so muyi ko nace alfarma zan nema a wajan ka.” Ba tare da ya kalle ya ba yace, “ina ji.”
“Tunda Alalh ya rubuta da ni za’a je Umrah nan an ina zamu bar Amir?.” Ya kalle ta da mamaki yace, “Kamar ya an ina zamu bar Amir?.”
Tace, “ina nufin inda zamu barshi.”
“Bani da y’an uwa? Kuma wajan Umma fa?.”
Rukayya tace, “Daman cewa zanyi dan Allah ka bawa mahaifiyar shi kafin mu dawo, wallahi ta damu da lamarin sa sosai tana son ganin sa a kusa da ita saboda….” Dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu yace, “kai k’arshen maganar ki kawai.”
“Na fad’a ai Khalil, dan Allah a bata shi na kwana sati biyun kafin mu dawo, zata ji dad’i sosai.” Ya juyo ya kalle ta kamar zai magana sai kuma kawai ya fasa ya d’auke kansa tace, “in abinda nace ya bata maka rai kayi hak’uri, mahaifiyar sace itace ta d’auki cikin sa ta raine shi ta sha wahalar haihuwar sa akwai soyayyar sa mai tarin yawa a zuciyar ta. Dole tayi kewar sa gashi shi kad’ai take dashi shi kawai Allah ya bata a yanzu. A ganina tunda ka manta da shafin rayuwar baya bai kamata maganar ta dinga b’ata maka rai ba, Tunda kace min baka santa ba muje a baka santa din ba kaga maganar babu amfanin ta b’ata maka rai da zatayi. Kayi hak’uri” ta fad’a a sanyaye tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba.