Sashe 85
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusuf yace, “kuma haka ne, banyi tunsninzuwa bama sai yanzu. Daman visa ta England ta kusa k’arewa sai muyi amfani da ita mu shiga Saudia.” Ammah tace, “hakan ya kamata, wannan zaman ba zai amfane ka ba ai tunda lalura ce Allah ya d’ora maka.” Ya sauke numfashi baice komai ba Mubakar yace, “ni sai nake gani kamar ma baka farin ciki bayan ga wacce kake Shan kukan a kanta tana tare da kai. Soyayya bala’i ce, ban tab’a ganin kana kuka bafa tunda nake a duniya sai Akan Ameena.” Ya kalli Mubakar sai yayi murmushi kawai Humaifa tace, “kai kasan wani farin cikin baya bayyanuwa ko Yaya?.” Shi dai baiyi magana ba ya tab’e baki kawai sukayi dariya.
Humaira ta kalli Ameena tace, “Sis zo muje kiji wata magana.” Ameena bata ce komai ba ta tashi ta bita dan tasan wata gulmar zata isar mata.
Suna gidan har akayi sallar magriba sai a lokacin ne ya shiga d’akin Ammah ya same ta a zaune suna Shan kayan marmari ta da Ammah da Humaira yace, “ke wai baza ki tafi gida bane?.” Humaira ta kalle shi tace, “sai anyi sallar i’sha.” Ya girgiza Kai ya kalli Ameena yace, “muje?.” Ammah ta kalle shi tace, “taje ina? Baka ga abinda take yi ba? Ka jira ta gama mana ko ka bari ayi i’sha kwa tafi kuma. Ta nesa ma gata a zaune balle ku maqota?.” Yusuf ya kalli Ammah da take magana tace, “to Ammah.” Abinda yace kenan ya fita Ameena ta kalle shi kafin ta kalli ammah sai suka had’a ido Ammah tace, “ke ban hana ki bin sa bafa, tashi kije naga kina kallona ta k’asan idanu.”
Ameena tayi dariya mai sauti Huamira tace, “kema dai Ammah kece da wata magana, wai sai anjima gashi nan ta nuna miki bin sa zatayi.” Ameena ta kalli Huanira tace, “banda sharri.” Ammah tayi dariya tace, “gashi naga zahiri, tashi kije maza ni ban hana ki ba.” Ameena bata tashi ba tace, “basai naje ba Ammah.”
“Baki isa ba tashi ki tafi sai da safe.” Ameena ta tashi tsaye ta kalli Zaytun da ta shigo ta kalli Ameena tace, “ Mummy Mun tafi unguwa da Uncle Mubakar.” Humaira tace, “sai kin dawo.” Zaytun ta fita Ameena ma ta yiwa Ammah sallama ta fita ta same shi a zaune ganin ta ya saka ya tashi suka fita tare.
Suna fita ana kiran sallah ya kalle ta yace, “zan shiga masallaci kije gani nan.” Ta amsa ta wuce sai da yaga ta shiga gidan sannan ya wuce masallaci. Ita kuma tana shiga sama ta hau tayi wanka ta canja kaya tayi sallah tana tsaye a falo saman sai gashi ya shigo tace, “Yaushe zamu je wancan gidan ne? Akwai abinda nake so zan d’auka.” Ya girgiza kai yace, “ai Mun barshi kenan baza mu saka amfani da komai na cikin sa ba.” Ameena da mamaki tace, “Meyasa to?.”
“Babu wani abu na rayuwar baya da zamu yi amfani dashi yanzu, mu din ma Mun canja dole komai ya canja.”
Tayi murmushi tace, “to ka sha magani tunda Kaci abinci.”
“Zan sha, amma zo kiji” ya fad’a yana zama ta zauna a kusa dashi ya saka hannu ya zagayo da hannun sa a jikin ta ya kwantar da kansa a kafadar ta yace, “yaushe zaku yi hutu?.” Ameena tace, “mun je hutun mix semester ma yanzu haka.”
“Yauwa, gobe nake so zamu tafi Saudia ko jibi muje asibitin nan ayi abinda za’a yi sannan kuma mu gode Allah a can.” Ameena tace, “Allah ya kaimu lafiya.”
“Amin. Passport din ki dana Zaytun suna wajena, zan saka Mubakar ya duba mans ticket indai zai yu gobe nake so mu tafi.”
Ameena tace, “Allah ya nuna mana goben.” Ya amsa da amin yayi shiru yana jikin ta har lokacin itama bata ce komai ba sai daga baya tace,”baka sha magani ba naji jikin ka da zafi.”
“Magani na yana tare dake ai Beb.”
“To indai yana tare dani ai ya kamata ace yanzu ka warke, Tunda gani gaka.” Ya d’ago ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa tayi murmushi tace, “kai ka ce a bar komai ya wuce meyasa wani abun yazo ranka yanzu?.” Ya kalle ta yace, “kunyar ki nake ji.”
Ta kwanta a jikin sa tana murmushi bata ce komai ba yace, “tunda mun manta da baya mun kalli gaba, muje daga ciki?” Ya fad’a yana kallon fuskar ta suka had’a ido tace, “baka da lafiya.” Kamar mai rad’a yace, “na warke.” Tayi murmushi shima Murmushin yayi yana kallon ta cikin so da qaunar ta a zuciyar da tace, “naji, amma kasha maganin ka.”
“Kar ciwon kan ya tashi ya hana wani abun?.” Ta kalle shi jin abinda yace sai tace, “zauna to basai ka sha ba.” Yayi dariya mai sauti yace, “ina sonki Ameena, dashi Allah ya halicce ni dashi zan mutu.”
Ta d’ago tana kallon sa shima ita ake kallo yace, “baki yarda ba?.” Ta girgiza kai alamun A’a ya sake yin murmushi ya tashi tsaye ya rik’e hannun ta yace, “zo ki tabbatar.” Ta tashi tana kallon sa tace, “a yanzu ma na tabbatar ai.” Ya girgiza kai yace, “gani ya kori ji, muje ki tabbatar babu b’ata lokaci.” Ta girgiza kai tace, “A’a basai na tabbatar bama na yarda.”
“Ai baki isa ba, Tunda kina kokwanto ya kamata ki amince.” Murmushi tayi yaja hannun ta zuwa d’aki tana fatan zaman su ya d’ore haka har abada.
Suna shiga d’akin ta kalle shi tace, “Gashi Mun zo, me zan tabbatar?.” Ya matso da ifta jikin sa yace, “son da nake miki.” Ta kwanta a kirjin sa tace, “ai na fad’a maka na tabbatar.” Yayi murmushi yace, “so nake na daina cin alfarmar Ammah na zauna daram babu wanda zai kare ni a zuciyar ki.” Bata ce komai ba ya d’ago ta daga jikin sa yace, “bani da k’arfin guiwar kasancewa dake, zuciyata na so amma in na tuna adadin kwanakin da aka d’auka a wancan lokacin sai naga kamar in ka nemi wani abun a wajan ki bani da hankali. Kiyi hak’uri Ameena, ki yafe min duk sabodake nake shiga wannan Matsalar gashi ana tunanin na samu tab’in kwakwalwa.”
Ameena tace, “babu wani Matsalar kwakwalwa da ka samu, ana so a gano inda ciwon yake ne amma ba dan ka samu matsala ba. Kai kace na d’auka komai ya wuce meyasa kake dawo da abinda ya wuce din bayan ni ban dawo dashi ba?.”
“Kunyar ki nake ji” ya fad’a voice din sa na shaking ya rik’e ta sosai a jikin sa tace, “ka zama rabo yanzu komai kuka, ko kunyar kukan ma a gabana baka yi, mai arhar hawaye zan dinga ce maka.” Yayi murmushi hawayen suna sauka yace, “na cutar dake Ameena, na zalumce ki, da wani abun ya same ki da ya zanyi da hakkın ki?.”
Bata ce komai ba yace, “zan gyara kuskuren, zan goge wancan zan rubuta sabon zaman lafiya a tsakanin mu a farin littafi. Kin bani dama Ameena?.” Ya fad’a yana raba jikin sa da bata yana kallon ta ta daga masa kai alamun eh tace, “amma kar ka cutar Dani, ko yaushe ka zama mai tausayina. Ka daina min fad’a Akan komai, koda an fad’i abu a kaina ka tsaya kayi bincike a kai kafin ka yanke min hukunci.”Ya girgiza kai yace, “har abada, har a tashi duniya ni mai tausayin ki ne. Babu ma wani wanda zai sake fad’a min wata magana a kanki balle na kasa tsayawa na bincika in sha Allah.” Murmushi tayi masa ganin hakan ya saka zuciyar sa farin ciki sosai ya sake mayar da ita jikin da ya rik’e ta gam gam.
Ameena tace, “zaka b’alla min k’ashin baya.” Ya sassauta rik’on da yayi mata yana murmushi itama Murmushin tayi yace, “amarya ce ke kin yarda?.”
“Zan yarda in ka amince kai ango ne.” Yayi dariya mai sauti yace, “a guje ma.” Dariyar itama tayi zuciyar ta ba sake amsar chanjin sa tana ki a jikin ta baza’a sake maimaita abinda akayi a baya ba.
Washe gari tana tashi kafin ta tashi zaune suka had’a ido dashi yayi murmushi itama haka ta rasa meyasa tun jiya yake kallon ta yana murmushi, ta tashi daga kan gadon tace, “wannan Murmushin na rasa na meye shi tun jiya nake ganin sa.” Ya tashi shima yana kallon ta yace, “na farin ciki ne.”
“Da gaske?.”
“Eh mana.”
“To a daina kallona ana yi.” Yayi dariya yace, “Yanzu aka fara.” Murmushi tayi itama tace, “.ya kamata naje na had’a breakfast ko?.”
“Yunwa kike ji?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “saboda kai ai kaci abinci ka sha magani amma ni yanzu ai na kai sha biyu ma banci komai ba.” Ya jawo ta jikin sa yace, “to nima haka.” Ta kalle shi tace, “A’a ya kamata Kaci.” Ya girgiza Kai yace, “A’a bazan ci ba., kawai ki dawo ki zauna.”
“To nayi ne in na zauna? Ba gwara baje na gyara gidan ba.” Ya ja hannun ta suka zauna yace, “Akwai masu aikin da zasu zo daga gidan Ammah zasu gyara miki ko Ina, nan akwai abinda zaki yi, baki san kewar ki da nake ji ba wallahi bama so kije ko ina.”
Ameena tayi dariya tace, “to gani ai, Muna tare a gidan nan ko?.”
“So nake mu zauna a nan abincin ma a kawo mana daga gidan Ammah.” Ameena tace, “mu zauna a d’aki kuma babu inda zamu je?.” Ya d’aga kai yace, “haka nake so, indai zan samu hakan ina so.” Ameena tace, “to gani.”
“Dana ana saka mutum a zuciyar mutum da naje an bud’e zuciyata an saka ki kawai na huta, kinga dai yanzu gani gaki na rik’e ki ko? Amma wallahi kewar ki nake ji a zuciyata da gangar jikina Ameena. Hakan bai gamsar dani sosai ba, ban san wacce irin soyayya Allah ya dora min a kan ki ba.”