← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 93

Sashe 42

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbah sai da ya kira Abie da Yaya Abubakar da Usman abokin Yusuf suka tafi can, koda suka je a inda suka ga Yusuf sai da zuciyar su tayi rawa ya basu tausayi fiye da tunani, yayi bak’i daga jiya zuwa yau saboda babu ci babu sha babu kwanciya sai dai zama suka kalle shi babu Wanda yayi magana Abie yaje wajan ma’aikacin yace, “Dan Allah da wa zamuyi magana akan Yusuf?.” Wanda yake yiwa magana yace, “oga ne kuma bai zo ba, zaku iya zama.”

Zama sukayi suna kallon Yusuf idanun sa na lumshe kamar mara lafiya jiriii yana d’aukar sa daga inda yake, Abbah ya girgiza kai yana kallon sa zuciyar sa ta karyar kamar yayi kuka haka yake ji dan in ka kalle shi ka sake kallon sa dakyar baka ji idanun ka sun taru da hawaye ba. Suna nan a zaune har sha biyu tayi Abbah ya kalli Agogo ya dafe kai yace, “ina da flight yanzu na manta ma.” Abie yace, “Kaje Abba zamuyi komai.”
“A’a dai mu zauna kawai na tafi zuwa dare.” Suna wajan har akayi azahar suka tashi sukayi sallah Usman ya sake tambayar su aka ce Oga bai zo ba.

Suna wajan akace Oga yazo ya shiga ya baya zaman jiran a basu dama suyi magana da Oga har la’asar ta kusa, Yaya Abubakar ne yayi tashi dan shi baya jurewa ya ya same su yace, “Ya ana yi muku magana kunce yazo tun d’azu shaya mutane? Kun San waye mahaifin mu da zaku wulak’anta mu haka? Ai ko dajarar girman sa kwa duba ayi wani abun ya bar wajan nan Kasancewar ba saba zama akayi a waje irin wannan ba.” Wanda yake yiwa magana yace, “Kaga a man aikin mu muke ka bamu waje.”
“Ank’i a baku waje din, wannan wanne irin wulakanci ne tun d’azu ake magana d’aya har yanzu taki k’arewa, in baza mu ganshi ba kuce baza mu ganshi bama sai kin bata mana lokaci.”

Abie ya taso ya janye shi ya kalli ma’akkacin yace, “in Zaku bamu dama ku bamu, in baza ku bamu ba mu tafi.” Abbah da yake kallon sai a lokacin ma ya tuna da yayi waya mana ya d’auki waya ya fita waje yana kiran wanda ya sani a sama dan a shiga maganar. Yana shigowa Oga ya fito suna hira shida wani da ya juya baya sannan suka gaisa ya juyo suka had’a ido da Abbah.

Yaya Adam yace, “A’a Alhaji.” Ya fad’a yana k’araso wa wajan har k’asa ya gaishe da Abbah yace, “Alhaji me kuke yi a nan haka?.” Abie yace, “a Yusuf aka kama wallahi, har yanzu anki fad’a mana laifin ma me yayi tun kafin azahar muke a nan har Abbah.” Adam yace, “Subahanallahi, Yusuf dai” ya fad’a yana juyawa ya hango Yusuf a kwance kamar ma baya cikin hayyacin sa.

Adam yace, “kai a fito dashi kamar ma bashi da lafiya.” Oga ya kalle su yace, “a fito dashi yanzun nan.” Da sauri aka fito da Yusuf dan sai janyo shi akayi dan a sume yake aka kwantar dashi a wajan. Adam ya kalli abokin sa kuma shugaba a wajan yacc “Meyasa yaran nan naku suke ke yin haka ne? Kalli bashi da lafiya amma sun k’i bari ayi magana ma balle a san abinda ya faru. Harda mahaifin a wajan nan ace tun safe har yanzu an kasa magana balle ma san wanne laifi ya aikata?.”

Oga ya kalli Abbah yace, “Alhaji kayi hak’uri dan Allah ba san abinda ya faru ba kenan” ya fad’a yana d’aukar wayar sa yayi gefe ganin mai masa waya. Bai jima yana wayar na ya juyo yace, “kayi hak’uri alhaji yanzu ma wayar da akayi min akan maganar ne.” Adam yaja tsaki yace, “wannan ai rashin sanin aiki ne wallahi.”

Ya kalli Oga yace, “yanzu ya za’ayi dashi emergency ne kana kallon sa unconsciously.” Ogan yace, “case ne Babab soja, kama cocaine akayi a motar sa.”
“K’aryar banz ce wallahi baya shan cocaine kuma baya siyar da ita, ajjiye masa akayi na tabbata bazai aikata ba.”
“Ka San shi ne?.”
“K’anina ne fa, kai a banza nake wannan tayar da jijiyoyin wuyar.”

Ogan ya kalle su yace, “Waye case din yake hannun sa?.” Ya taso da sauri ya kalle shi yace, “Meyasa baka fad’a min tun d’azu ba?.” Adam yace, “ba aikin ka zan ko ya maka ba Mujahid amma wannan ba aiki bane, ya mutum yana kwace a sume kana wani tambayar banza da wofi. Kaga ni ka bani Yusuf din na kai shi asibiti in ya gudu ka kamo ni kawai, snake dashi yanzu su kayi magana dasu.”

Ya kalli Adam yace, “bazai yu bane hakan har yanzu ana zargin sa da abin bazai yu ba dole sai munyi magana tukunna.”
“A kai shi emergency na k’arkashin ku mana, wannan wanne irin bincike ne?.” Ogan ya kalli Adam yace, “Dan Allah ka nutsu Adam za’a yi komai yadda ya kamata, matsala ta dakai hargagi. Kai ku d’auke shi a kai shi emergency” ya kalli su Abba yace, “Abbah mu je.”
Adam yace, “ni zamu je dashi asibitin.” Mubarak da ya yake wajan yace, “A’a Yaya Adam ni zan bisu ka zauna a nan.” Ya kalli Mubakar yace, “Yauwa dan Allah ka bisu.” Aka d’auki Yusuf aka fita dashi su kuma suka shiga office din Muhajid.

Cocaine din da aka kama a motar ya ajjiye akan table yace, “Alhaji Kaga abinda aka kama a motar sa a safiyar jiya.” Adam yace, “au tun jiya ma yake a hannun ku amma ba’ayi yi waya ba sai d’azu? Wannan wanne irin abu ne wai haka? Baku da tabbas akan tasa ce ko ba tasa bace a ajjiye mutum ba ci babu sha sama da awa ashirin da hudu? Yanzu in ya mutu a hannun ku fa?.” Ya kalli Adam yace, “da zahiri muke aiki Adam, kasan doka ya take ai ka ajjiye wannan hargagin naki dan Allah.”

Alhaji yace, “Abinda na sani Ysusuf baya harkar k’waya gaskiya sai dai in saka masa akayi a motar.” Yace, “to bamu da tabbas tunda dai babu shi a wajan nan yanzu, kaya dai tunda a motar da aka gani nasa ne in kuma ba nasa bane a dokar mu sai ya kawo mana mai kayan sannan zamu sake shi.” Adam zaiyi magana ya katse shi yace, “NDLEA ne nan fa Adam ba police station ba, Muna da ka’ida kan aikin mu, amma saboda wayar da akayi da kai za’a san abinda za’ayi amma dole Yusuf ya kasance a karkashin kulawar mu har sai munji magana daga bakin sa.”

Adam yace, “In saka masa akayi a motar fa?.”
“Wannan bai dame mu ba, mu dai a motar sa muka ga kaya dan haka na sane” ya kalli Abbah yace, “Alhaji ku kwantar da hankalin ku in sha Allah babu matsala za’a san abinda za’ayi amma dole sai ya farfad’o gaskiya.” Alhaji yace, “Babu damuwa mu gode. Amma zamu iya zuwa mu duba shi?.”
“Za’a iya amma dai dole akwai masu kula dashi ma’aikatan mu in ya farfad’o akayi magana za’a iya bada belin sa tunda anyi magana daga sama ga kuma Adam.”

Abbah yace, “babu damuwa in gode sosai, bara na kira Mubakar muji abinda suke.” Ogan yace, “ Alhaji in sha Allah a gida Yusuf zai kwana gobe.”
“Har sai gobe? Kenan yau ma a wancan wajan zai kwana?.” Ya kalli Adam yace, “yanzu ai yana asibiti ko? A can zai kwana da safe sai ayi magana a wuce wajan.”

Adam yayi tsaki ya tashi ya fita yayi murmushi ya kalli Abbah yace, “Adam dan rigima kenan, Alhaji wannan d’an naka kana fama dashi bashi juriya ko kad’an komai ayi a gama kawai. Baya son b’ata lokaci gashi bai iya fushi ba, mantawa yake da waye shi in ran ya b’aci Abbah yayi murmushi yace, “sojojin kenan.”
“Tare muka fara aikin dashi na fad’i a wani training sai na dawo nan, abokin a ne sosai yana da kirki akwai zumunci baya yarda ya sani ko waye shi.” Abbah yayi murmushi kafin yayi magana yace, “Kar ka damu Alhaji walalhi ko ba’a yi waya daga sama ba saboda Adam za’a san abinda za’ayi, so nake muji daga bakin sa sannan sai mu yanke hukunci.”
Abbah yace, “na fahimce ka, babu damuwa mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi.”
Aka amsa da amin suka fito tare sukayi alwala akayi sallah sannan suka wuce inda aka kai Yusuf dan su ganshi.

Book3
24

Lokacin da suka je asibitin an kwantar da Yusuf ana k’ara masa ruwa da yake da Mubarak private aka je d’akin shi kad’ai sai mai tsaron sa a k’ofa a tsaye shi kuma yana kwance yana bacci. Kallon sa suke yi dukkan su dan ya rame sosai yayi bak’i kayan jikin sa sunyi daud’a sai ga nurse t shigo Abbah yace, “Dan Allah me yake damun sa?.” Ta kalle shi tace, “muje waje ayi muku bayani.”

Tare suke fito ta kalli Abbah tace, “damuwa da yunwa sune suke damun sa, jinin sa ya d’an hau ta dalilin damuwar ko kuma ya jima baiyi bacci mai yawa ba duk shine suka had’u suka saka ya suma lokaci d’aya. amma yanzu Alhamdulillah komai zai dawo daidai da ya tashi.” Abbah yace, “to mun gode sosai.” Bayan ta bar wajan Abbah ya kalli Adam yace, “Soja na gode sosai fa Allah ya bar zumunci.” Adam yayi murmushi yace, “Babu komai Alhaji, zan koma yanzu zan san abinda za’ayi bazai koma wajan nan ba in sha Allah. So nake ya tashi muji ya akayi ta shiga motar sa ya bawa motar kafin ya hau an ina kuma ya ajjiye motar.” Abbah yace, “Gaskiya ne wannan, Allah ya taimaka mana baki d’aya.” Ya amsa da amin yayi musu sallama ya wuce.
Chapter 42 · 0% Book details