← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 93

Sashe 65

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tace, “ya zama dole na samo kud’in nan kafin gobe in ba haka ba Sakina zata wulakanta ni.” Baba ne ya shigo duk yana jin abinda suke cewa ya kalle su gabad’aya su in badan darajar yaran ba da yanzu ya jima da rabuwa da Umma amma yaran yake dubawa shiyasa yake d’aga mata k’afa. Wuce su zaiyi yaga Asiya a zaune tana kuka tana cewa, “yace min ya sake ni saki uku, na shiga uku a taimaka min kafin na mutu, bazan iya zaman gidan nan ba wallahi. Saki uku yace yayi min, na lalace ni Asiya.” Baba ya kalle ta yace, “dole ki zauna kuwa in ba haka ba sai ki kama gaban ki. Lalacewa kuma indai baku gyara halin da Uwar ku ta d’ora ku a kai ba yanzu kuka fara” ya fad’a yana shigewa ciki ya barsu.

Umma tace, “saki uku naji kina cewa fa?.” Tace, “gidan su naje Umma, yace min ya sake ni saki uku, shikenan yanzu na daina zama a falo ina kallo, Nidai an cuce ni da aka raba ni da mijina wallahi.” Umma tayi shiru cikin jimami sai tace, “Tunda ya riga ya datse auren shikenan babu yadda zamuyi, gobe aje a kwaso kujerun falon d’aya na gidan aje a siyar sai a biya ta kudin.” Sai Asiya ga mik’e kamar a itace take kuka ba tace, “kujerun wa? Babu wanda zai tab’a min kayana ajjiye su zanyi in ya mayar dani na cigaba da amfani da kayana. Babu kayan da za’a kwaso min wallahi dan ba’a isa ba.”

“Asiya wai kike yiwa wannan abubuwa akan abin duniya? Uwar ki ce ni fa?.”
“Umma kece kika saka ya sake ni da yanzu ina gidana, meyasa kika saka ya sake ni dan Allah?.” Umma tayi shiru ta kalli Baba da yake kallon su taga yayi murmushi kawai ya fita. Itama wuce ta tayi kawai ta koma d’aki zuciyar ta a cushe sosai wai Asiya ce take mata wannan abun akan kud’i, kud’in da itace silar tara su badan ta sha wahala anyi auren ba da yanzu ba haka ba.

Haka suka kwana Asiya kwana tayi kuka da danasanin abinda tayi gashi an raba ta da mijin ta tana ji tana gani ta zama bazawara. Washe gari da safe Umma Sakina ta sauka a gidan Baba ya fita lokacin Umma na tsakar gida tana tunanin kud’in Sakina sai kuwa gata harda y’an sanda. Suna shigowa tace, “Yauwa gata nan, bashi nake binta ta hana ni kud’ina muje da ita ko ta bani kudina ko a kulle ta.” Umma tsoro ya cika mata zuciya ganin y’an sanda tace, “Sakina ni zaki yiwa wannan wulakancin akan kud’i? Nice fa Atika k’awar ki kuma aminiyar ki.”
“Ban sanki ba, ban kuma tab’a ganin ki ba, ki bani kudina ko kuma a tafi dake yanzu.”
“Bani dasu, amma ki bani lokaci zan kawo miki.”
“La la la! Wallahi bazan yarda ba, officer kama min ita.”

Jami’iar tayi wajan Umma tace, “ki bamu hadin kai kawai muje in munje za’a iya sasanta ku in hukuma ta shiga maganar.” Umma tace, “Dan Allah ki bari mu sasanta a nan da mutuncina a ganni a wajan y’an sanda da sunan an kama ni babu dadi ai.” A lokacin Baba ya shigo ganin abinda yake faruwa yayi kamar bai gani ba Umma tace, “Malam ka saka baki kana ganin za’a tafi dani.” Baba ya kalle su baiyi magana ba ya shige daki.

Su Maimuna suna kallo aka tafi da Umma Fauziyya tabi bayan ta duk da babu abinda zata iya. Asiya dai tana tsaye sai da aka tafi da Umman taji babu dadi a zuciyar ta jikin ta yayi sanyi tana dana sanin abinda tayi gashi bata da kud’in duk suna cikin account d’inta, amma zata san abinda zatayi dan karb’o Umman ta daga hannun hukuma.

#Mai room
#Book3
#paid
#500
#Nana haleema.

Book3
034

Asiya ta kalli Maimuna cikin sanyi jiki, dan sai bayan an tafi da Umma taji jikin ta yayi sanyi sosai tace, “shikenan zanje yanzu na d’auko wani abu a gidana sai naje na siyar na kai a karb’o Umma.” Maimuna tace, “da ke akwai wani abun kika bari aka tafi da Umma a gaban ki?, ina yake naje da kaina ke ba Lafiya gare ki ba.” Asiya tace, “A’a barni naje yanzu zan dawo” ta fad’a tana jan mayafi ta har zata fita sai ta koma ciki ta shiga d’aki ba jimawa ta fito ta fita ita ta manta ma wai tana wani abu idda ne a lokacin.

Kai tsaye gidan ta ta wuce ta dinga buga gate din mai gadin yana can yana bacci kamar zata b’alla gidan haka take buga shi ya tawo ya bud’e ganin itace yace, “sannu da zuwa.” Ta kalle shi tace, “tun d’azu ana bugu baza’a bud’e ba dan an raina mutane?” ta fad’a shigewa cikin gidan kai tsaye b’angaren ta ta wuce. K’ofar na kulle kamar yadda ta barta ta saka key din ta bud’e ta shiga falon ta hau saman da sauri.

D’akin ta shiga duk wani kayan ta na kadara da ta tara ta tattaro su ta zuba a jaka ta fito ta sauka tana kallon falon sai akwai ta fara kuka tace, “shikenan yanzu na bar kwana a gidan nan? Shikenan yanzu na daina zama a wannan kujerar?. Na shiga uku ni Asiya na cuci kaina, k’arya ta kaini ta baro ni Allah ya isa an cuce ni.” Motsi taji alamun ana shigowa falon gaban ta ya fad’i ta d’auka Yusuf ne sai taga Mubakar ya da mai gadi a bayan sa ya kalle ta yace, “ke zo ki fice kafin na kifar dake a wajan nan.”

Shiru tayi bata yi magana ba ta sai kallon sa da take yi ta wuce shi tace, “na sake ganin k’afar ki a gidan nan wallahi sai na sab’a miki kammani, barauniyar banza da wofi. Uban me kika zuba a jakar?” Ya fad’a yana yin kanta zai ta kwasa a guje ya fita tsabar dariya sai ya kasa binta yace, “gayyatar tsiya” ya kalli mai gadin yace, “Yauwa baba, duk wanda ta sake zuwa gidan nan ka sanar dani.” Baba yace, “an gama.”

Asiya a guje ta fita daga gidan tana waige sai ga mai adaidaita sahu a kusa da ita ta fad’a tace ya kaita kasuwar rimi ya kaita ta sauka ta bashi kud’i tana maqale da jakar hammata hannu a maqale ta shiga cikin kasuwa. Kai tsaye kantin Maryam Jumare mai saida gold da azurfa da saka haqorin makka ta nufa, dan ta ganshi babba sosai baza’a cuce ta ba tana shiga ta zauna mai kantin da yaran sa a zaune yace, “Barka da zuwa.” Tace, “barka dai.”
“Siya ko siyarwa?.” Asiya tace, “siyarwa.” Ya d’aga kai yace, “mu gani.” Ba musu ta sakko da jakar ta fito da sark’ar ta ajjiye masa.

Kallon sark’ar yayi sannan ya kalle ta ganin ta wata tagaja-tagaja ya d’auki sark’ar ya auna gram din ta ya sake kallon Asiyan sannan yace, “ina y’an kunnen?.” Asiya tace, “a haka take, kyautar ta akayi min.” Ya girgiza kai yace, “to ina receipt din?.” Asiya ya dan yi jimm kafin tace, “ya kone a gobara da nayi da ita akwai na tsira, a wajan gudu gobarar ne ma na karye a hannu ka gani.”

Yayi murmushi yace, “Allah sarki, to nawa zaki siyar?.” Ta kalle shi dan bata san ya ake yin abin ba sai tace, “nawa zaka siya?.”
“Ke zaki fara yi mata kudi, in naga zan siya a haka na siya in zan rage sai na rage.”
“Ka kawo miliyan biyu.” Kallon sark’ar yayi ya kalle ta ya girgiza kai yace, “Haba hajiya na bada dai miliyan d’aya a bani.” Ta kalle shi tace, “Gaskiya bazan siyar haka ba.” Yace, “shikenan da dari biyar Allah ya saka musu albarka.” Asiya ta sauke numfashi yace, “to kawo.”

Ya fita daga da inda yake yace, “ina zuwa” ya fad’a yana fita ya barta a zaune da yaran sa da suke ta aiki a wajan. Jim kad’an sai gashi ya dawo ya nuna Asiya yace, “barauniya ce.” Asiya gaban ta ya fad’i ta tashi tsaye tace, “Kamar ya barauniya, nice barauniya?.” Ya nuna musu sark’ar yace, “kunga sark’ar da ta siyar a baira miliyan d’aya da dari biyar.” Mutanen suka kalli sarkar suka kalle ta wani yace, “ahh wannan ko a b’arayin ma bagidajiya ce, wannan sarkar da zata haura miliyan goma a yanzu saboda tsadar dala shine ta siyar haka?."

Asiya tace, “ni ba b’arauniya bace, wallahi ba b’arauniya bace ba ni.”
“Karya kike wallahi, yau a cell zaki kwana, badan da hankalina ba da kin jawo min bala’i a garin nan. Wannan sarkar kana gani kasan k’era ta akayi ta wata matar Alhajin ce watakila ita kad’ai ce mai irin ta duniya a yanzu shine zaki d’auko kika zo kika kawo min ko? Yau a station zaki kwana.” Asiya na kuka aka tasa keyar ta aka tafi da ita wajan yan sanda.

Washe gari ranar asabar jirgin su Rukayya zai tashi da karfe sha biyu na rana tun safe suka fita daga gidan suka wuce gidan su Rukayyan tare dan ya yiwa su Umma sallama. Da sallama Rukayya ta taga Amir yana ganin ta ya taso yana mata oyoyo ta zauna suka gaisa da Umma Umma tace, “tun d’azu yake maganar ki sai gaku, k’arfe nawa zaku tashi?.”

“Zuwa sha biyu akace.” Umma tace, “Allah ya kai ku Lafiya ya dawo daku Lafiya.” Ta amsa da amin sai ga Ibrahim ya shigo shima suka gaisa Umma ta dinga yi masa godiyar da bai San dalilin ta ba har yaji nauyin hakan shi kawai murmushi yake yana amsa addu’ar da take yi masa. Baba ne ya shigo nan ma aka sake sabuwar gaisuwa Ibrahim ya fita har zai shiga mota sai yaji ana masa magana, yana juyowa yaga mahaifin Fiddausi sai ya fad’ad’a murmushin sa ya k’araso ya duk’a har kasa ya gaishe shi Abba yace, “Ibrahim yanzu ake fad’a min abin alkhairi, kai naji dadi Allah ya sanya alkhairi ya kai ku Lafiya ya dawo daku Lafiya, Allah ya amsa ibada.”
Chapter 65 · 0% Book details