← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 93

Sashe 46

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaf ta kashe labarin ta fad'awa Zakiyya tashin hankali da ta shiga sai dan cikin ta ya motsa kuka itama take yi kamar ranta zai fita, cikin kukan  tace, "lallai Fiddausi kin auna arzuki da Allah ya kub'utar dake daga hannun mugu azzalumi. Kai Innalillahi wa'inna ilahir raji'un mu kam mun sakawa zuciyar buri shiyasa gashi nan muna ta wahala." Fiddausi tace, "Hakkin Ibrahim ne yake bina, na cutar dashi, nayi masa rashin mutunci, nayi masa..." sai ta dafe kai kawai ta kasa cewa komai dan in ta tuna kamar ta dawo da abin haka take ji. Fiddausi tana kuka cewa, "duk wani abu da nayi masa sai da ya faru a kaina, ma zubar da cikin sa an zubar da nawa, na hana shi kaina a lokacin da yake bukatar hakan  anyi amfani dani ta k'arfi kuma ta hanya ba daidai ba, babu abinda na iya dole na hak'ura, na saka an saka shi a cell nima na shiga cell. Zakiyya ya ko wanne b'angaren wallahi hakkin Ibrahim ne da kuma son zuciya irin nawa."

Zakiyya tace, "ni kaina hakkin Ibrahim ya shafe ni balle ke, domin kuwa in b'era da sata daddawa da warin ta, nice umul'abamisin auren ki da Bello, Bawai dan cutar dake nayi hakan ba sai dan akwai ki samu abinda kike so. Amma yanzu na wayi  gari cikin fargaba da tashin hankalin had'uwa ta da mijina, ya tabbatar min da in na sake na raini cikin nan har na haife shi sai ya sake ni Fiddausi. Ke kin aan ya gidan mu yake in na baro gıdana na dawo gidan mu an ina zan zauna?, me zanci bayan nice nake taimaka musu?. Ina cikin gidsn komai yi min ake yi amma wallahil azim bana cikin farin ciki ko kad'an, kalli yadda na koma ni kaina. Nayi dana sani wallahi nima." Kuka suke tayi har anyi i'sha basu sani ba sai da Mama ta shigo tace, "kukan ya isa Kuyi sallah an idar tun d'azu" ta fad'a tana juyawa ta fita.

Zakiyya tace, "Ameena da Rukayya da suke saka kyskykyawan burina zuciyar su ke in kika ga Ameena da Rukayya yanzu sai kin so ki sake kallon su, amma kalle ni kalle ki yadda muka koma bayan da su muke yiwa dariya muna ganin basu San dadin kudi ba."

Fiddausi tace, "Ameena da Ruky ba irin fad'an da basa yi mana amma muka toshe kunnen mu, banji haushin ki ba Zakiyya bazan ce ke kika zuga ni ba son zuciyata ce itace ta Kaini ta baro, inda ban biye miki ba da hakan bata faru ba. Rukayya da Ameena su da yake babu son zuciyar a tare dasu ai basu tab'a yarda da kalaman ki ba. Kalli yadda kika koma kalli yadda na koma, duk mun lalace har gwara ke a kaina, ni luwadi akayi dani" sai ta sake fashewa da kuka Zakiyya tace, "ki daina kuka ya wuce na tabbatar yanzu yana can yana girbar abinda ya shuka."

Fiddausi ta goge idon ta tace, "Anyi bikin Ruky ko? Wa ta aura?." Kallon Fiddausi Zakiyya tayi sai tayi murmushi tace, "Zamu je gidan wanda ta aure baki San shi ba."
"Bata auri Ibrahim din ba?."
"Eh, wannan  sunan sa Mu'azzam ba Ibrahim din ki ba." Fiddausi tayi murmushi tace, "daina cewa Ibrahim dina na wata ne dan nasan yayi aure yanzu shima, Allah Sarki Ibrahim ya bani rayuwa mai kyau a gidan sa, ya kyautata min ko kad'an baya so yaga raina ya baci, hana hak'uri dani yana sona in nayi laifi sau goma sau d'aya zai min hukunci, bai tab'a bari na kwana da yunwa ba, bai tab'a bari nayi kwadayin wani abun ba kafin na ayyana ya kawo min. Duk da bashi da kudi amma yayi kokarin kiyaye min duk wani hakkina da yake wuyan sa. Ya bani tarbiyya a zamana dashi, yadda nayi k'iba a zama na dashi ko Ameena da take  gidan Yusuf batayi ta ba, amma na bijire bana ganin duk abinda yake min, na wulakanta shi nayi kokawa dashi na saka aka kama shi" ta d'aga kai sama tace, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Zakiyya na tafka babban kuskure hakkin sane yake bibiya ya a yanzu, na tabbatar a tafka asarar da bazan tab'a mayar da kamar ta ba."

Zakiyya tace, "Mun yi kuskure dukkan mu, na zab'i kudi matsayin farin ciki amma tunda an samu cikin nan kud'in suka zama basu da amfani a wajena saboda babu farin ciki, Kullum fargabata kar ya dawo ya tarar ban zubar d cikin nan ba, na rame Kullum a fad'uwar gaba nake.  yanzu in yazo ya sake ni ya zanyi? Ina zanyi rayuwa a gidan mu? A ina zan zauna? Da ace ban zuga ki kin zubar da ciki ba da yanzu watakila bana cikin wannan tashin hankalin, hakkin dan cikin ki da muka zubar ne ya biniye ni."

Fiddausi tace, "sakayya muke gani wallahi, sakayya da gaggawa Allah ya nuna mana ita. Kinga ranar da kuka gama wayar nan daku akan Ibrahim yana son Rukayya a washe gari farin ciki ya kaurace min, Kullum cikin kuka da tashin hankali nake, Allah Mun tuba ka yafe mana" ta fad'a tana rufe fuskar ta tana sake fashewa da kuka.

Sun jima a haka kafin ta goge idon ta tace, "A haka ma nayi kyaun gani ai Zakiyya. Yaushe zamu je gidan Rukyn?." Zakiyya tace, "keda baki da lafiya? Ki bari na sanar dasu sai su zo ko?."
"A'a ni nake so naje."
"muje gobe in zaki iya sai mu fara zuwa wajan Ameena daga nan sai muje gidan Rukayya tare da ita." Kai ta d'aga kafin Zakiyya tace, "mu tashi muyi sallah kar kamu k'arawa kan mu zunubi." Sallah sukayi a d'akin suka cigaba da tattaunawa har dare yayi sosai kafin Zakiyya ta koma gıda.

             Kamar yadda Yaya ya cewa Ameena a shirya Zaytun bayan sallar isha suka tafi, a cikin d'akin da yake suka samu yan gidan su harda Abbah da Ammah duk suna nan shima ya tashi yana zaune ana Shan tea. A guje Zaytun tayi wajan Ammah ta d'auke tana dariya tace, "takwara kullum k'ara girma kike me mummy take baki?."

"Abinci." Ta fad'a Ammah tayi dariya tace, "lallai naga alama." Mubakar ne yace, "Zaytun ba magana?." Sai ya sauka daga jikin Ammah ta tafi wajan sa ya d'auke ta yana yi mata wasa kafin ta tafi wajan Yusuf. Adam ya kalli Yusuf yace, "ya jikin naka?." Yusuf ya kasa had'a ido dashi kai a k'asa yace, "Da sauki."
"Alalh ya kara Lafiya." Ya amsa da amin.

Sallama akayi aka shigo ganin wands  ya shigo ya saka Yusuf yin murmushi yace, "A'a Taha k'araso ciki." K'arasa yayi ya gaishe da kowa ya zauna skan kujera yace, "ashe baka da lafiya, Mubakar na kira yake sanar."
"Wallahi ina kwance."
"Ina wayar ka?." Yusuf yace, "ai tana gıda wallahi."
"Haba koda naji." Yusuf yace, "lafiya dai?."

Taha yace, "kudi ake cirewa daga account din ka a kalla yanzu an cire kudi yayi miliyan biyar ko sama da haka, in aka cire yanzu to sha biyun dare za'a sake cirewa. Shiyasa na kira ka naji anya wayar na hannun ka dan nasan ba haka aka saba da kai ba, kuma ta application ake cire kudin transfer ake zuwa wani account guda biyu."

Asiya da take tsaye ta fara zare ido Yusuf ya kalli Taha yace, "Wanne Account ake turawa?."
"Wani ne  something Asiya da kuma wani Maimuna, but tunda naga haka nace sace wayar akayi kuma kananun b'atayi ne basu san kan bank ba da baza'a zo haka ba. Amma zasu ci uban su na nemo address din su gobe zan saka aje a kamo su a duk inda suke, cire kud'i suke na gidadawa wanda satar ma basu iya ta ba. Amma zasu yi dana sani, but yanzu nayi blocking account din naka baza su kuma iya tura kudi ba tunda naga satar tasu ta kananun b'arayi ce. Abinda ya sa ma na lura sata ce yawan cirewar, da kad'an-kad'an suke cirewa kuma Kullum sai an cire sau biyu, shiyasa na san sata ce kuma satar ma ta k'ananun b'arayi. Amma zasu ci uban su."

Yusuf yayi murmushi ya kalli Asiya da take tsaye yaga sai zare ido take yi ya mayar da kai k'asa ya sunkuyar, Ammah da kowa da yake ji akayi shiru babu Wanda yace wani abun dan an San wacce take aikin nan sai Abie da yace, "Ai Taha ka bar zancen binciken ma tunda kayi blocking shikenan kawai, amma wanna satar ta gıda ce kuma mata ce ta d'auki kayan mijin ta a ganina babu komai akwai ka bar maganar nan." Taha da mamaki yace, "ban gane ba, kenan duk wanda yaci kudin yaci banza?."
"Baka ji ne bace bane? Mata ce ta saci kayan mijin ta shine kawai."
"Kana nufin matar sace take cire kudin?."
"Kwarai itace, babbar b'arauniya ce a kaf unguwar su itace shugaba, kawai ka bar maganar." Taha ya girgiza kai yace, "kuma yake zaune da ita? Matar ka ace tana sata meye amfanin zama da ita?, yanzu da ba kudin sa bane da haka za'a kama shi ita taci bulus?."

Mubakar yace, "ai kawai ka bar zancen Taha, duk wanda ya siyi rariya ai yasan zata zubar da ruwa, dan matar da ake so ta d'auki kudi ai ba komai bane ba." Taha ya girgiza kai kawai baice komai ba ya kalli Yusuf yana bai ma d'ago kansa ba balle yayi magana.

Yaya Adam ne ya katse shirun yace, "Zaytun muje ko, mu zamu koma dare yayi."
"A wajan Ammah zan zauna." Ammah tayi dariya tace, "ba wajan Daddy ba?." Ta kalli inda yake taga Asiya tace, "tsoron ta nake ji" ta fad'a tana nuna Asiya. Adam yace, "Zaytun kin manta kin fara zuwa makaranta?." Ganin zatayi kuka ya saka yace, "Zauna wajan Ammah, sai da safen ku" duk suka amsa ya fita yana mamakin hali irin na matar Yusuf ko yaushe cikin sata.
Chapter 46 · 0% Book details