← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 93

Sashe 73

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fiddausi tace, "ashe kin je kin d'auko shi."
"Naje Fiddausi, Su Mama ne suke cemin bashi da laifin komai akan me bazan d'auko ba? Shine naje Gashi yanzu a wajena har bana son Tuna jinin Alhaji Bello ne wallahi.”
"Haka ne kama bashi da laifin komai bai kuma san komai ba. Hak’uri zaki yi ai komai zai wuce zai kuma zo k’arshe, Allah yayi shine mahaifin sa babu Wanda zai canja faruwar hakan.”

Naja'atu tace, "amma an raba auren ko?." Fiddausi tace, "d'azu muka je kotu alqali ya raba auren tunda duk zance ya baza duniya ya zama mahaukaci." Naja'atu tace, "ni zan gaya miki ya zama mahaukaci Fiddausi, nifa naje gidan, wallahi tun daga k'ofar d'akin da yake zaki dinga jiyo wari gashi yana ciki yana ihuuu babu wanda yake bud'e shi balle aje inda yake. A nan yake komai babu ruwan wani da yaci ko yasha duk sun gudu sun barshi. Ba’a San dangin da ba balle a fad’a musu, ke ko an sani ma ba kowa ne yake son nuna su Bello yace d’an uwan sa bane ba. Wato Fiddausi a duniya in baka aikata alkhairi ba wallahi kana cikin mayuwacin hali. Ki kalle mu mu kan mu sai da muka girbe abinda muka shuka balle su Alhaji Bello."

Fiddausi ta share hawaye tace, "Mun ga sakamako kuwa mu ma balle shi, shi ai shaidan ne." Naja'atu tace, "da muka samu iyayen mu suka yafe mana ma Mun gode Allah, Aliya kuwa tace min da taje bata samu mahaifin ta ba ya rasu, sai kuka take bata sani ba ko yafe mata ko kuma da bak’in cikin ta ya mutu bata sani ba." Ta girgiza kai tana kuka kamar suna ganin juna tace, "in sha Alalh ya yafe mata. Ki bani lambar ta duk da yanzu ni bani da waya har yanzu."
"Nima ta Mama ce sai na samu hankalina ya dawo jikina sai na samu wayar."
"Ki tura min a wayar Maman sai mu gaisa da ita kafin mu saka lokaci mu had’u. Nan gaba mu zamu yiwa wasu fad'a in muka ji sun zab’i irin rayuwar da muka zab'a." 

Naja’atu tace, “ai Mun ga zahiri, Mun ga sakamakon mu tun a duniya.” Fiddausi tace, “Mun gode Allah ka da abin ya tsaya mana iya nan da bamu san a wanne Hali zamu tsinci kan mu ba muma.” 
“Bari kawai Fiddausi Allah ya tarfawa garin mu nono.”
“Su Bello kuma sai ayi mutuwar wulakanci,” Tayi dariya kawai suka cigaba da hirar abinda ya shafe su kafin suyi sallama su kashe wayar.

      Yusuf ya samu sauk’i sosai har lokacin babu Wanda yake masa maganar Ameena shi kad'ai yake tunanin ta a zuciyar sa amma babu wanda yake masa zancen ta duk da a yanzu duk sun saduda sun amince ya karb'i kuskuren sa amma babu Wanda yake goyan bayan sa a zahiri.

Bayan ya koma gida a daren da ya koma Ammah taga ya fito ya kwance hannun nasa wanda aka d'aure ta kalle shi tace, "meyasa ka kwance hannun?ina zuwa kuma?." Yayi shiru baiyi magana ba tace, "ko wajan Ameena din zaka je?." Ya d'aga Kai alamun eh kamar maraya yace, "ka daina wahalar da kanka Yusuf, Ameena bazata dawo rayuwar ka ba meyasa ka kasa ganewa." Ya kalli Ammah yace, "bazan gane ba Ammah, sai ranar da aka d'aura auren ta da wani a lokacin zan gane Ameena ta barni Kenan."

"Kafin lokacin yazo ya kamata ka san zai zo yadda in ya same ka zai zo maka da sauki Yusuf." Ya girgiza kai yace, "Ammah bazan iya ba walalhi." Ta d’aga Kai tace, "shikenan, sai ka dawo." Ya kalle ta yace, "Ammah dan Allah sau d'aya kice Allah ya bani sa'a." Ta kalle shi taga ita yake kallo tayi shiru na wani lokaci kamar baza ta fad’a ba kafin tace, "Allah ya baka sa'a Yusuf."
Sai yayi murmushi yace, "Amin Ammah, na gode." Ya fad'a yana fita ta bishi da kallo tace, "iska tana wahalar da mai kayan kara Yusuf. Allah ya kawo maka mafita a abinda yake damun ka, amma dawowar Ameena ba abu bane wanda zai yu a yanzu ba.”

Kai tsaye mota ya hau ko Usman bai nema ba ya tafi gidan Yaya Adam a karo na uku cika da k’arfin guiwa. A k'ofar gidan ya tsaya ya fad'awa mai gadin gidan ya sanar dashi zuwan Yusuf ya ja ya tsaya a jikin mota. Yaya Adam a lokacin yana zaune dashi da Ameena da Yayan Bauchi da matar sa suna ta tattaunawa akan abubuwan da yake tunkaro su a yanzu shine auren Ameena.

Sallamar sa ya saka suka kalle shi ya rage tsaho yace, "Alhaji Yusuf yace a sanar da kai zuwan sa yana waje." Yaya Adam ya sauke numfashi ya dafe kansa yayi shiru na wani lokaci kafin ya kalle shi yace, "kace yazo." Ya kalli Ameena da suka had'a ido ya kalli Yayan Bauchi yace, "ban san ya zanyi da Yusuf ba wallahi, duk masufar da nake ji da ita ya fara bani tausayi ko zaryar nan da yake ma ta isa ya baka tausayi. Bana so nace bazan ganshi ba ya sake tafiya yayi accident gwara yazo a sake gwabzawa.” Babu wanda yayi magana a cikin su Ameena ta mik’e zata koma Yaya yace, "dawo ki zauna." Ta dawo ta zauna sai ga Yusuf ya shigo da sallama Yaya Adam ya amsa yana kallon sa.

Gaishe shi yayi ya gaishe da Yayan Bauchi ta amsa da murmushi ya kalli Ameena yace, "Ameena Barkan ki da dare." Sai ta kawar da fuska gefe ba tare da tace komai ba ta d'aure fuska sosai. Yaya Adam ya kalle shi yace, "ya kuma karfin jikin?." Yusuf yace, "Alhamdulillah." 
"Allah ya k’ars lafiya." Ya amsa da amin kafin Yaya ya sake cewa, "to meye yake tafe dakai Yusuf?."

Yusuf taja numfashi ya sauke yace, "akan maganar nan ne dai Yaya, na kasa jure cewa da kayi kar na sake zuwa gidan nan sai da nazo, ji nake ko zaka dinga yankar naman jikina sai nazo na same ka a karo na uku Yaya." Yaya Adam yace, "Yusuf bafa dani zaka zauna ba, ga da wacce zaka zauna nan tana zaune tana Jin ka meye nawa da zaka dinga zuwa wajena?."
"Kaine tsani a wajena, dole kai zan fara tunkara ba ita ba, kai kanka baka amince ba balle ita Yaya?." 

Yaya Adam ya kalli Ameena kafin yayi magana Yusuf yace, "duk abinda idanun ka suka gani a wancan lokacin na gyara wallahi, duk abinda kake gudun ya sake faruwar a wannan lokacin bazai sake faruwa ba. Wannan alqawari nayi da Allah bazai sake faruwa ba duk tsanani duk dad’i.” Yaya Adam kallon sa yake yi domin nadamar yake gani akan fuskar sa sosai ta bayyana abinda bai gani ba a kwanakin baya, har zuciyar sa a yau ya amince Yusuf yayi nadamar abinda yayi kuma koda wasa nan gaba bazai sake aikata hakan ba sai  dai nuna masa ba yace, "ana iya cewa na daina a baki amma kuma  a zuciya ba haka abun yake ba, da zarar Ameena ta sake komawa shine an ta zama nama, wannan sunkuyar da kan da kake kana kuka duk na banza ne, tana komawa ka tashi daga b'era ka koma zaki sai abinda kake so shi zaka yi dan kana ganin sai ka sake furta kalmar saki a kanta ai zata fita."

Ya girgiza kai yace, "A'a wallahi, na daina wallahi duk abinda nake yi bazan sake yi ba, har zuciyar ta nake fad'a maka wannan, kuma Allah kad’ai shine yasan meye a zuciyata bayan shi babu wanda zai gani, da akwak wanda zai gani da na baka dama ka gani Yaya kodan ka gasgata da gaske nake ba wasa ba."

Yaya Adam ya sauke numfashi yace, "me kake so nayi maka yanzu?."
"Dama nake so a sake bani a karo na biyu domin gyara abinda na b'ata."
"Gaka ga Ameena nan indai har ta amince zata koma gidan ka Yusuf zan dawo maka da Ameena, in kuma bata amince ba sai dai kayi hak'uri." Ya kalli Ameena da take zaune ya kalli Yaya Adam yace, "gabana fad’uwa yake ban san taya zan mata magana ba." Sai ya bawa Yaya Adam tausayi sosai  ganin kamar ba namiji ba duk ya susuce ya kalli Ameena yace, "Ameena ga Yusuf nan in kin amince zaki koma masa a karo na biyu na amince nima, in baki amince ba shikenan sai yayi hak'uri."

Yusuf ya juya yana kallon ta yace, "nasan nayi kuskure Ameena, nayi laifi ko nace nayi laifuka amma ki yi hak'uri a karo na babu adadi zan gyara bazan sake gangancin hakan ba, bazan sake barin ki kuka ba indai ba na farin ciki ba, bazan sake barin ki a damuwa ba wannan alqawari nayi miki kuma zan cika shi indai ina da numfashi da rai. Ki amince ki bani dama dan Allah, badan ni ba kuma ba dan halina ba dan Allah dan kuma iyayena dan kuma Zaytun."

Yayi shiru na wani lokaci yana kallon ta dan yaji me zata ce sai yaga tayi murmushi tace, "Ka cire batun zan koma gidan ka Yusuf a kaf cikin rayuwar ka, na amince na yafe maka na kuma yarda kayi nadama amma damar ce bazan iya sake bayarwa ba gaskiya.." ya girgiza kai yace, "Dan Allah kar kice haka Ameena, kar ki kalli baya ki kalle ni matsayin sabon  Yusuf wanda ya canja daga wancan wanda kika sani dan Allah, Ameena indai zaki koma gidana koda baza ki yi min magana ba na yarda, na yarda ki gwada ni in kin koma daga ranar har shekarun da kike so na yarda, na yarda a zarar kinga canji kice na sake ki zanyi hakan wallahi. Duk abinda kike so zanyi." Ta kalle shi tace, "na koma ka cigaba da dukana ko?." Ta zuba masa ido sosai dan so take ya fahimci abinda take nufi ba dukan take nufi ba bata son fad'a a gaban su Yaya dan bai san yana shan giya a baya ba ita kuma kodan y’ar sa zata rufa masa wannan asirin har abada.
Chapter 73 · 0% Book details