Sashe 86
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta shiga jikin sa sosai ta rike shi tace, “to ka saka ayi maka aiki a saka ni a ciki mana.” Yayi murmushi yace, “dama ana yin hakan. Duk da Yaya Adam bazai bari ba.” Tayi dariya ya kalli fuskar ta yace, “Tunda baa’a saka mutum a zuciya amma ana iya yin kusancin da yafi wannan ko?.” Ta gane abinda yake nufi tace, “baka gaji ba? Baka da lafiya fa.”
“A bar zancen rashin lafiya, ni ban gaji ba ko kusa ko alama.”
“Ni kuma na gaji.”
“Zan saka ki d’aure.” Murmushi kawai tayi b’ata ce komai ba yace, “na gode Allah da nine dai Ameena har yanzu itace ni, Allah da wani ya shigar min gona ta Ameena da gaske zan iya haukacewa, a yanzu ma gashi kina ji Ana zancen hoton kwakwalwa ina ga wani ya kusance ki?.” Tayi murmushi tace, “Ameena dai itace kai, Amma kai ba kaine Ameena ba. Kar ka manta kayi aure fa.” Yayi shiru na wani lokacin bai ce komai ba ya kalle ta sai suka had’a ido yace, “ba gode Allah da ya bani ke matsayin Uwar gida a gare ni.”
“Akwai wata amaryar kenan?.” Jin abinda tace sai yayi dariya tace, “har abada.” Ta tab’e baki tace, “Ban yarda ba sai naga abinda gaba zatayi, Nidai koda nan gaba an samu a sanar Dani zan shige gaba wajan sanar da Ammah in sha Allah.”
Yusuf ya kalle ta yace, “ki daina wannan maganar dan Allah, a yanzu Yusuf naki ne ke kad’ai har abada.” Ta girgiza kai tace, “bazan yarda ba kawai kayi hak’uri, fatana dai a sanar dani da wuri.” Ya sauke numfashi dan ya kawar da zancen yace, “an bani dama na sake komawa inda zuciyata take marari?.” Tayi murmushi shima shi yayi yace, “ke daban ce ko a cikin mata Ameena, ni zan tabbatar miki da hakan a yanzu.” Nan ma batayi magana ba dan ta tabbatar da gaske yake babu yadda tayi haka ta zauna ranar a sama babu inda taje, Karb’ar abinci ne da aka kawo daga wajan Ammah ya saka ta sauka shima dan ya fita yaje masallaci ne.
Ranar tayi musu dadi sosai farin ciki ya ninku a zuciyar su sun manta da baya suna kokarin gina gaba farin ciki kawai suke yi da kuma da kula da junan su cikin soyayya da kewar juna.
Bayan kwana biyu.
Zaman Yusuf da Ameena sai dai ace Alhamdulillah farin ciki da kwanciyar hankali da walwala ta same shi a cikin zaman da suka yi dashi. Duk da farkon auren ne ba zata banbance ba zaman baiyi nisa ba amma kuma Ameena ta amince ta yarda koda gaba baza ta samu matsalar da ta samu a baya ba dan a yanzu yafi sonta akan baya.
Yusuf yayi k’iba ya mayar da jikin sa duk da har lokacin bai daina ciwon kan ba amma tunda suka je Saudia abin yayi sauki sosai sai dai yana tashi lokaci zuwa lokaci musamman in ya kasance ya wahala sosai.
Tana zaune akan kujera tana juya takarda a hannun ta ya shigo da sallama ta kalle shi bayan ta amsa yace, “yan boko, karatun ne ya chaja miki kai?.” Ta sauke numfashi tace, “ba karatu bane ba, bama takardar makaranta bace.” Ya zauna kusa da ifa yace, “yo ta meye?.”
“Wai asibiti naje shine suka ce min wai ciki ne dani” ta fad’a tana mik’a masa takardar bai karb’a ba ya bita da kallo cikin tsantsar farin ciki ya wara ido yace, “ciki fa Beb, na kwana nawa?.”
Tayi dariya kad’an tana rufe ido tace, “komai daidai.”
“Kice wallahi?.” Sai tayi dariya tace, “naga shi nan ka karanta.”
“Ni daga bakin ki nake so naji, kina so kice wai a ranar Allah ya k’addara samun unborn?.” Ta rufe idanun ta tace, “ka cika maimaita magana wallahi, ni kunya kake bani wallahi.” Yayi dariya ya rik’e ta yana shafa cikin yace, “Allah baki ji farin cikin da nake ji ba kamar babu Zaytun. Yanzu da gaske dai a ranar Allah yayi an samu ciki? Koda yake ranar fa babu inda muka je abu d’aya kawai aka saka a gaba.” Tayi dariya ta kifa fuskar ta a kirjin sa tace, “baka da kunya.” Yayi dariya yana jin farin ciki a zuciyar sa.
Kamar zatayi kuka tace, “ni kuma yar jaririyar y’ata nake ji. Nawa take ma da za’a yi mata k’ani?.” Ya harare ta yace, “yarinyar da tana zuwa makarnaya itace jaririya?.” Ta kalle shi tace, “Abin yazo da sauri ne ban yi tunanin hakan ba.”
“Rabon kenan” ya fad’a yana mata kiss a kumatu tayi murmushi tace, “fita fa zanyi.”
“Makaranta?.”
“Wa yake ta makaranta, jiya Ruky ta haihu yanzu gidan ta zanje.”
“Allah Sarki, me ta haifa?.” Ameena tace, “mace ta haifa.”
“Allah ya raya.” Ameena ta amsa da amin tace, “ya kamata muje kayi mata barka kaima ko?.” Yace, “eh hakan ya kamata, yanzu muje na sauke ki in zan dawo na d’auke ki sai na shiga mu gaisa ko?.” Ameena tace, “nida kaina zan tafi.”
“ai in baki wasa ba kin daina driving kenan
Sai kuka kin haihu.” Ameena tace, “Kar ma kace haka dan Allah.” Ya tashi tsaye yace, “ai na ma ce, taso muje.” Ta tashi ta saka mayafi tana kallon sa yace, “harare ni da kyau kin daina.” Tayi dariya suka sakko tare ta shiga motar yana suka tafi gidan Rukayya.
A k’ofar gidan Rukayya ya tsaya ta kalle shi tace, “to sai ka dawo?.” Ya zuba mata ido ya jingina da kujera yana kallon ta yace, “a kula min da unborn.” Ta kalle shi alamun ta gaji da maganar yayi dariya ya tashi zaune sosai yace, “Allah sai na hana ki fita na juya.” Tayi dariya tace, “Allah ya baka hak’uri, mai kasan yadda na shiryawa yau din nan kuwa? Su Fidy duk suna ciki bi kawai ake jira.” Yayi murmushi yace, “to jeki, sai munyi waya.” Ta bud’e motar ta fita shi kuma ya juya ya tafi.
Tunda suka hango ta ta window suke ihuu ta toshe kunne ta shiga tace, “ku a gidan mutane muke fa, naga alama mai gidan yana nan kuke mana ihu” ta fad’a tana kallon Zakiyya dan itace karfin yi Fiddausi dai na zaune tana murmushi Ameena tace, “Fiddausi! Kan bala’i haka kika koma?.” dariya tayi tana kallon Ameena tace, “ke bance kinga yadda kuka koma ba sai ni?.”
Ya kalli Zakiyya tace, “ku tsaya, ina Rukayya wai take ma?.” Zakiyya tace, “tana wanka bata fito ba.” Ameena ta zauna ta karb’i babyn a hannun Fiddausi Tana kallon ta tace, “kai ma sha Allah! Wannan baby tabarakallah akwai hanci.” Zakiyya tace, “kamar Rukayya yarinyar mai kyau wallahi kamar na sace” ta fad’a da nata babyn a hannu wanda ya dan yi watanni.
Fiddausi dai na zaune tayi shiru bata wani motsin kirki ana haka sai ga Rukayya ta fito Ameena ta bita da kallo tace, “Allah Sarki mar’atussaliha, k’araso ki zauna.” Sai Ameena ta bata dariya gashi bata son yin dariyar saboda an mata d’inki ta k’araso ta zauna Ameena tace, “Sannu Rukayya, Allah ya raya abinda aka samu.”
Tayi murmushi murya a hankali tace, “Amin Ameena. Kinga yadda kika yi kyau? Lallai Ana Shan amarci.” Ameena tayi dariya kad’an ta kalli Fiddausi da tayi shiru bata magana tace, “Wai Lafiya kike?.”
Fiddausi tayi murmushi kawai Zakiyya tace, “Wai kunyar zuwa gidan nan take yi har yanzu, gashi bata had’u da mai gidan ba tana son bashi hak’uri har yanzu abu ya gagara.” Rukayya ta kalle ta tace, “Yanzu kuwa zai fito nasan zai fita” sai ta kalli Window tace, “ga motsin sa can, kije ki same shi.” Ta kalli Rukayya tace, “kin bada damar Hakan?.” Rukayya tayi tsaki ta kawar da kai kawai hakan ya saka Fiddausi riko hannun Ameena tace, “zo ki raka ni.”
Tare suka fita da Ameena a daidai lokacin yana niyar bud’e mota Fiddausi tace, “Assalamu alaikum.” Ya juyo yace, “Wa’alaiki salam.” Ga mamakin su sai suka ga yayi murmushi Ameena tace, “ina kwana.” Yace, “Lafiya lau, ya gida?.”
“Lafiya lau walalhi, an samu karuwa Allah ya raya abinda aka haifa yayi mata albarka.”
Ibrahim yace, “amin na gode.” Fiddausi ta kasa magana ganin hakan sai Ameena ta tab’a ta sai ta kalli Ameena din alamun baza ta iya magana ba ganin hakan sai Ibrshim yayi murmushi yace, “Fiddausi baki ga Amir din ba?.” Gaban ta ya fad’i damm ta d’ago ta kalle shi sai yayi murmushi yace, “yak’i zuwa makaranta yau yace an yi masa k’anwa bazai je.”
Ameena tace, “da gaskiya sa.” Yayi murmushi kawai zai shiga mota tace, “Ibrahim ka yafe min abubuwan da suka faru a baya dan Allah, na kasa tunkarar ka nayi magana amma yau na samu dama saboda fuskar da na gani a wajan ka da matar ka. Ka yafe min kar ka rik’e ni a zuciyar ka.” Ya juyo ya kalle ta yace, “kar ki damu, ki d’auka komai bai faru ba kar komai ya dame ki komai ya wuce. Ni ban rik’e ki a zuciya ba na manta da abinda ya faru.”
“Baka ce ka yafe min din ba.”
“Na yafe miki, dmaan ba laifi kika yi min ba.” Sai tayi murmushi tace, “na gode.” Baice komai ba ya shiga mota ya fita da baya su kuma suka koma ciki jikin Fiddausi a sanyaye.
Rukayya ganin su sai tace, “na fad’a miki shi komai ya wuce kawai kin kasa yarda ne yanzu ai kin yarda.” Ta zauna tace, “yanzu nake jin na dawo sabuwa dal saboda yace ya yace min, hakkin sa nake ji da yake kaina amma yanzu Alhamdulillah. Na gode Ruky.” Tayi dariya Fiddausi ta kalli Ameena tace, “Ameena kinga yadda kika yi kyau kuwa? Anya baki da ciki?.” Tayi murmushi tace, “wata biyu.” Sukayi dariya gabad’aya banda Rukayya da take murmushi kawai Zakiyya tace, “kinji rabon ko? Ke ko wannan rabon abinda aka samu ba dole ma ki komawa Yusuf ba.”