Sashe 91
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana tsaye bata motsa ba ya wuce ya shiga band’aki tana tsaye ya fito ya canja kaya ya d’auki magani zai sha sai ya fasa sboda ba’a sha ba’aci abinci ba ya zauna ya dafe kansa dan ciwo yake masa, indai zai sha wahala ko zai shiga damuwa to tabbas kai zaiyi ciwo. Jikin tane yayi sanyi kuma haka ne fa itama bata tambaye shi meyasa baya cin abincin ba, ta k’araso ta zauna tace, “kayi hak’uri, bazan sake ba in sha Allah. Kuma wallahi ni ban san ina maka fad’a ba, d’auka nake magana ta normal nake yi amma bazan saka ba in sha Allah. Duk yadda akayi cikin nan ne yake saka ni haka amma ba da niya nake yi ba.”
Shiru bai amsa ba ta kalle shi tace, “kayi hak’uri dan Allah, bazan sake ba wallahi nasan nayi kuskure kayi hak’uri. Nayi bak’i ne jiya har Yaya Al’Ameen yazo shiyasa ban samu nayi girki ba.” Sai a lokacin ya kalle ya yace, “to meye na fushi dan kince zakiyi nace ki barshi? Ba dan wani abun na fad’a bafa sai dan tausayin ki duba da yanayin ki bake kad’ai bace amma sai kika yi fushi, Wato da safe ma sai na Nemo abinda zanci.”
“Kayi hak’uri.”
“Nayi Ameena, amma kar ki sake nan gaba bazan yi hakurin ba.” Ta girgiza kai tace, “bazan ma sake ba in sha Allah.” Ya d’aga kai kawai tace, “to me kaci yau din?.”
“Nidai nasan na sha fruits nida Usman then na sha fura da nono bayan nan ban kuma cin komai ba.”
“Baka ci wajan Ammah ba?.”
“Bana so nace zanci abinci a gidan, naci jiya yau ma naje sai taga kamar akwai wani abun.”
Ameena tace, “dole kanka yayi ciwo ai, bara na dafa maka koda indomie ce.” Baice komai ba ta tashi ta fita ya bita da kallo har yanzu akwai ragowar abinda ya faru a zuciyar ta, yasan daman bazai goge ba wani abun da anyi sai taga kamar za’a maimaita baya ne sai ta kama kanta bata san ko haukacewa yayi bazai sake aikata abinda yayi a baya ba. Yayi hankali ya kuma gane mahimmacin da yake dashi soyayyar ta kuma kullum sake yawa take a zuciyar sa.
Ba jimawa ta dawo da indomie a bowl ta zauna akan bedside drawer ta tace, “ga indomie.” Ya bud’e idanun sa yace, “sai dai in da kan ki zaki bani.”
“A guje ma.” Ya tashi zaune ta zauna kusa dashi tace, “Akwai zafi amma fa” ta fad’a tana d’auka ta kai bakin sa ya bud’e ya karb’a ya haddiye yace, “ Tayi dadi,” Tayi murmushi zata sake bashi ya juyar da fock din zuwa bakin ta yace, “kema ki ci.” Baki ta bud’e taci ta sake bashi ya sake bata a haka suka cinye indomie din ta ajjiye bowl din tace, “Yanzu sai ka sha magani” ta fad’a tana d’aukar maganin ta bashi yasha ta tashi ta shiga band’aki sai gata towel ta jiqa shi ta d’ora masa a goshin sa tace, “Allah ya yaye maka wannan ciwon kan.”
Ya amsa da amin ya lumshe idanun sa yana kallon ta ta sunkuye sosai yana jin khamshin jikin ta mai dadi nan take Asiya ya fad’o masa a rai sai ya runtse ido tsigar jikin da ta tashi yaja dogon tsakin da ya saka ta kalle shi tace, “lafiya?.” Ya bud’e ido ya kalle ya yace, “babu komai.”
“Wannan tsakin kace babu komai?.”
“Na tuna wani abun ne.”
“Oh!” Ta fad’a akwai tana zama bata ce komai ba.
Ya kalle ya yace, “baza ki kwanta ba?.”
“Zanje nayi wanka sannan na duba Zaytun.”
“Kije ki duba ta ki dawo wankan sai Kiyi a nan.” Ta amsa da to ta tashi a fita ya bita da kallo Kansa na sarawa sosai yana jin zuciyar da na bugawa a ko wanne minti.
Ba jimawa ta dawo tayi wankan ta fito ta shirya duk yana kallon ta taje ta zauna kusa dashi tace, “Beb na tambaye ka?.” Ya kalle ta yace, “ina ji.”
“Beb wai ina Asiya?.” Gaban ss ya fad’i ya kalle yta itama shi take kallo ya sauke kansa k’asa ya sake kallon ta yaga dai shi take kallo yace, “zamu iya barin zancen nan?.”
“Meyasa zamu bari? Tambaya nayi kawai ka bani amsa.” Ya kalle ta yace, “Dan Allah kashe mana hasken nan kizo.” Murmushi tayi ga lura bazai bata amsa ba bai san tasan komai a bakin Humaira ba ta tashi tayi abinda yace ta dawo ta kwanta kamar yadda ya kwanta yace, “Dan Allah zan iya neman alfarma a wajan ki?.”
“Eh mana.”
“Dan Allah a bar zancen wata ko wani da suke wuce a rayuwar baya, indai babu su a rayuwar mu ta yanzu dan Allah kar Kiyi min maganar su.” Ameena tace, “to babu komai in sha Allah baza’a sake ba.” Ya kulle ido ya bud’e yana kallon ta sai yaga tayi murmushi yace, “meye a ranki?.” Ta lumshe ido ta bud’e tace, “wani abun na tuna.”
“Meye?.”
“Kai da kace min ka tuna ai ban tambayi meye ba ko?.”
“Nidai ko me kika tuna ina sonki, da kuma son ki zan mutu dashi zan tashi har ranar alqiyama.” Tayi murmushi ta kwanta a jikin sa bata ce komai ba.
Yace, “har yanzu alfarmar Ammah da Zaytun nake ci? Kince min daman bakya sona kin tsane ni har yanzu haka ne a zuciyar ki?.” Ta sauke numfashin da yaji shigar wucin sa jikin sa tace, “zamu iya barin maganar nan?.” Ya girgiza kai yace, “baza mu bari ba Beb, ina so na sani kullum da tunanin hakan nake kwana nake tashi.” Tayi shiru bata ce komai ba yayi murmushi yace, “na fahimta, Allah ya canja miki abinda kike ji a ranki Beb, ya dasa miki sabuwar soyayya ta a zuciyar ki” ya fad’a yana shafa cikin ta yace, “Allah ya fito mana da babyn mu lafiya.”
Da amin ta amsa yace, “Amin din ta addu’ar farko ce ko ta biyu?.” Tayi murmushi mai sauti tace, “Addu’a ta biyu.”
“Ta farko bata cancanci ace amin ba?. Bakya jin zaki sake son Yusuf?.”
“A’a, daman bance bana son Yusuf ba.”
“Wallahi kince, kuma idanun ki sun nuna hakan har yanzu babu soyayyar Yusuf a zuciyar kina zaune zaman Zaytun da Ammah da kuma rabon da Allah yayi sai a same shi a cikin ki.”
Ta sauke numfashi yace, “kar kice komai ina nan ina addu’a Allah ya dawo da soyayyata zuciyar ki ko bata Kai ta baya ba dan ba’a b’ari a kwashe duka.”
“Bana fata ma ta kai ta baya.”
“Kenan da gaske babu soyayyar?.” Ta kalle shi suka had’a ido duk da babu haske tayi shiru bata ce komai ba yace, “gaskiyar ki kika fad’a nima ina son hakan Beb, Allah ya dawo da soyayyata a zuciyar ki kafin barina duniya.”
“Ni bance bana son ka ba fa.” Yusuf yace, “har mai sona ma kince bakya so Ameena.” Ta kwanta a jikin sa sosai ya rik’e ta yace, “Allah ya sani, yasan zuciyata, yana san abinda yake Raina, yasan abinda ya dasa a tsakanin haqarqarina wallahi ina sonki. Kuma na canja bazan sake maimaita abinda nayi ba amma kin kasa amincewa dani har yanzu kina kokwanto a kaina da halyayata Ameena.”
Ameena tace, “Bana kokwanto kawai in wani abun ya faru ina tuni kwatankwacin sa da ya faru a baya, kasan kuma wannan bazan iya mantawa ba dole na tuna.” Ya girgiza kai yace, “Haka ne, Nima ina tunawa sosai jikina yana yin sanyi ina tabbatar da cewa tabbas ba dan halina kike a zaune a gidsn nan ba, inda dan halina ne baza ki sake kallona ba. Wallahi dana rasa ki ciwon nan zai iya tab’a kwakwalwata na haukace Ameena.” Kafin tayi magana yace, “in na tuna lokacin da nake shan giya nake dukan ki Ameena ina ji kamar na yanki jijiyoyin jikina saboda yadda nake jin bak’in ciki a zuciyata, me ya shiga kaina ne har na kai kaina ga shan abinda Allah ya haramta?. Ina zubar da hawaye a duk lokacin da na tuna hakan.”
Ameena tace, “Shan giyar nan yafi komai d’aga min hankali, yafi komai tsaya min a rai, shine kan gaba wajan cewa bazan dawo gare ka ba.”
“Na daina Ameena, daga ranar da su Ammah suka samu labari kamar anyi ruwa an d’auke.” Ta sauke numfashi bata amsa ba ya sake cewa, “in na tuna na tsallake ki na share ki na daina kula da lamarin ki na tsahon wasu watanni, Allah kad’ai yasan me nake ji a zuciyata, babu lallai ki amince amma ina dana sanin aikata hakan. Nidai nasan farko farkon faruwar hakan ina sane Ameena, Ina yi ne dan kiji haushi tabbas, amma daga baya bazan ce ni ne ko ba ni bane.” Ta sauke numfashi tace, “to ka bar tuna wannan maganar jikin ka har yayi zafi, baka da lafiya ka kuma san tuna hakan yana baka damuwa.”
Shiru yayi na wani lokaci babu Wanda yake magana a cikin su kafin yace, “Kiyi hak’uri dan Allah, ki daina kallona da abubuwan baya. Na amince na yarda ban cancanci ki dawo saboda dani ba sai dan saboda Ammah din, amma ki yafe min ki sake bani gurbi a zuciyar ki.” Ameena tace, “ya isa haka dan Allah, ni aka yiwa nace na manta to meye na damuwa?.”
“Baki manta ba wallahi, kina sane kina kallona da abin shiyasa wani lokacin kike misbehaving saboda kina tuna abinda ya wuce ni kuma ni bana ganin laifin ki, kin yi daidai ko dukana zakiyi kin aikata daidai Ameena.”