Sashe 2
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameena tace, "wai daman saboda haka Fidy ta rabu da Ibrahim?." Rukayya tace, "hmm bakin su d'aya da Zakiyya fa, duk abinda ya faru da saka hannun Zakiyya itace take zuga ta." Zakiyya tace, "k'aramar yarinya ce da zan zuga ta? Babu wata zugata da nayi akwai ni na taya ta cika burin ta ne kawai kuma burin ya cika." Ameena ta kalli Zakiyya tace, "zugar kenan ai."
Zakiyya tace, "wannan ya wuce Ameena, muyi magana akan abinda yake gaban mu a yanzu. Bara na kira Fiddausin na tabbata abinda na fad'a shi zata maimaita, duk hankalin Rukayya ya tashi Akan wannan gwara tasan ba wani abun bane ba" ta fad'a tana d'auko waya ta shiga kiran Fiddausi ta katse bata d'auka ba ta sake kira a lokacin ga dauka ta saka a speaker daga can tace, "Kiyya yane? Kin kira ina wanka ina fitowa kiran ki ya sake zuwa."
"Amaryar Alhaji Bello, ko ne mana ma bakya yi" Ameena ta fad'a daga gefe." Fiddausi tace, "Muryar wa nake ji kamar ta uwar gidan Yusufa?."
"Nice."
"Wallahi Ameena baki da kirki, message nawa na yi miki ta WhatsApp bakya bud'ewa?." Ameena tayi murmushi tace, "wallahi ni na manta ma rabon da na shiga WhatsApp, tuba nake amarya."
Fiddausi tayi dariya tace, "wallahi nayi kewar ku sosai, ina amaryar Ibrahim kuma?" Ta fad'a tana dariya sosai. Kallon juna sukayi Zakiyya tace, "daman kin san maganar ne?." Fiddausi tace, "na sani mana, jiya ake bani labari a gidan mu Baba yaje ya samu Abba da maganar shi kuma ya fad'awa Mama, Mama tace sai farin ciki Abba yake yi dan wai Ibrahim yana son Rukayya kamar wani gwamna ne yake sonta. Kar dai su Abba suyi mata dad'in baki ta yarda ta kai kanta gidan talauci wallahi."
Zakiyya tace, "Maganar muke yanzu da da Ruky kin ganta a zaune duk tayi tsuru-tsuru wai ita ji take kamar ma zuwa da yayi yace yana sonta kamar taci amanar ki ne."
"Amanar wa? Ni Fiddausin Abba?, Rukayya ko lokacin da nake gidan sane yace zai d'auko ki meye zai dame ni balle bana gidan?. Nifa sai yanzu nasan meye aure nasan meye ma kishin miji, wallahi da bana kishin wani Ibrahim balle naji haushi da zaiyi aure, kina ji Ruky in zuciyar ki ta amince da Ibrahim bismillah ki shiga babu abinda zai damu Fiddausi, kuma in na dawo har gidan zan zo wajan ki mu gaisa dashi matsayin mijin ki naci shinkafa da wake in akwai kunu na kora dashi babu abinda ya shafe ni. Ai na rufe chapter wannan talakan a rayuwata wallahi. Kawai dai kema ki yiwa kanki fad'a kowa gidan jin dad'i yake zuwa ke zaki tafi gidan wahala."
Zakiyya tace, "Kamar a gaban ki haka nace mata yanzu nan, dan ma fa hankalin ta ya kwanta ne ya saka na kira ki, duk da basu zauna shida ita ba ya samu Baba da maganar ne kawai shine hankalin ta ya tashi haka wai mutanen unguwa sai suce daman tun can baya tana son sa ita ta kashe auren ku dan ta aure shi." Fiddausi tayi dariya son ranta harda su tafa hannu kafin tace, "to su fad'a mana, in zata biyewa mutane ai baza ta yi komai a rayuwar ta ba. Ni kaina dana biye mata ai da yanzu bana inda nake, ni wallahi in da zata aure shin ma farin ciki zanyi saboda nasan Amir dina ya samu uwar da zata kula dashi fiye dani."
Sai a sannan Rukayya tayi magana tace, "balle ma babu abinda zai kai ni Allah ya had'a kowa da rabon sa." Fiddausi tace, "gwara dai ki yiwa kanki fad'a ki samu mai kud'i ba irin su Ibrahim ba. Sai yanzu nasan da zaman cutuwa kawai nayi wallahi." Murmushi kawai Rukayya tayi Zakiyya tace, "Wai yaushe zaki dawo ne?."
"Ke nima ban sani ba wallahi, Ina nan ina Shan soyayya me zai dawo dani Nigeria?. Wai kuna gidan Ameena ne na jiku tare?."
Zakiyya tace, "eh Muna can, kin San da yake...." Ameena ce ta tab'a ta tare da girgiza mata kai alamun kar ta fad'a mata Zakiyya ta fasa fad'at abinda zata ce tace, "sai dai kin dawo akwai labari, amma ina jin bakya nan za'a yi bikin Ruky."
"Maganar tayi karfi kenan?."
"Eh akwai wani ai da yake sonta da gaske kuma bana jin auren zai d'auki lokaci."
"Mai kud'i ne?."
Zakiyya tayi dariya tace, "Mai kudi ne, sai dai yana da mata." Fiddausi tace, "in ma mataye ne dashi ba mata ba kawai ta shiga, Allah ya sanya alkhairi. Kai amma naji dadi wallahi Rukyya zata shiga daga ciki itama."
Dariya sukayi dukkan su kafin suyi Zakiyya tace, "kar ki kwashe min katin ma k'arasa a whatspp" ta fad'a tana kashe wayar ta kalli Ruky tace, "kin ji ahında na fad'a miki ko?. Rukayya kar ki yi gaggawar korar Ibrahim kice masa ke bakya son sa, ki tsaya ki yi addu'a kawai wanda ya kasance alkhairi Allah ya zab'a miki a cikin guda biyun, in dukkan su babu alkhairi Allah ya kawo miki wasu. Ke zuciyar ki ba irin tamu bane ta son mai kud'i ba, dan haka Ibrahim daidai da ke ne."
Ameena tace, "shine akwai abin yi." Rukayya ta girgiza kai zuciyar ta na yin sanyi da kalaman Fiddausi da kuma nasu Zakiyya domin sai taje jin tsoron da take ji game da Ibrahim gabad'aya ya kau, zuciyar ta sai take bata k'arfin guiwar zata iya sauraren sa koda bazata aure shi ba.
Ameena taji dad'in zaman su sosai sun jima suna hira ta sake ana dariya da ita har bayan la'asar sannan suka tafi.
Rukayya tana komawa gida shigar ta soron gidan su kenan suka had'u da Baba yana niyar fitowa ya kalle ta yace, "ina kika je ne ina ta neman ki?." Rukayya tace, "munje wajan Ameena ne nida Zakiyya."
Baba yace, "maza kije ki shirya kina da bak'o yana jiran ki." Gaban Rukayya ya fad'i ta d'aga kai Baba ya fita ita kuma ta shiga wajan Umma. Da Zuhra suka had'u a tsakar gida tayo wajan ta tana fadin, "Aunty kin san waye yazo wajan ki? Ibrahim fa mijin Fiddausin ki." Rukayya tace, "Shine bak'on da Baba yake fad'a?." Ta d'aga kai tace, "Shine, kije kar baba yayi miki fada tun d'azu yake neman ki wayar ki bata shiga."
Falon Umma ta shiga Umma na ganin ta tace, "tun d'azu ake kiran wayar ki bata zuwa, kin shiga wajan bak'on?." Ta girgiza kai alamun A'a tace, "Umma anya hakan ya dace kuwa?, mijin Fiddausi ne mahaifin yaron ta fa." Umma tace, "Jeki dai kiji mai zai ce ki dawo sai muyi maganar daga baya" da to kawai ta amsa ta juya ta fita ba tare da ta canja komai ba ta nufi d'akin da Baba yace mata gaban ta yana mugun fad'uwa bata san dalilin hakan ba a haka ta tunkari d'akin zuciyar ta na bugawa sosai.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
Book3
002
Sai da ta tsaya a bakin k’ofa ta daidaita nutsuwar ta sannan ta shiga da sallama kanta yana k’asa. Daga ciki taji ya amsa ta k’arasa ta zauna a kan carpet ta d’an yi shiru bata ce komai ba kafin ta d’ago ta kalle shi tace, “Barka da yamma.” Kyankyawan murmushi yayi mata wanda ya saka ta saurin mayar da kai ‘kasa yace, “Barka dai Malama Rukayya, ina fatan n same ku lafiya.”
Rukayya kanta yana kasa tace, “Lafiya lau, ya su Hajiya?.”
“Alhamdulillah, tanas gaishe ki.” Bata iya amsa ba domin zuciyar ta bugawa take yi sosai ya lura da rud’anin da take ciki sai ya tausasa murya yace, “Rukayya nazo wajan mahaifin ki akan ina so na shiga sahun masu neman auren ki, shine ya bani dama yace nazo yau na ganki kuma gashi nazo, sai dai ke naga kamar bakya son ganina ni kuwa ganin naki nake so.”
Kai ta girgiza kawai bata ce komai ba ya sake cewa, “ilimin ki, nutsuwar ki da kuma shaidar da kika samu daga bakin mutane itace ta jawo hankalina zuwa ga auren ki. Kamar yadda Baba ya sanar dake sunana Ibrahim na tab’a aure amma bana tare da matar, ina da yaro guda d’aya mai sunan mahaifina wanda nake kira da Amir. Ina aiki a masana’antar sarrafa siminti.” D’ago ido tayi ta kalle shi cike mamakin sa jin yana fad’a mata abinda ta riga ta sani hakan kamar ma ya raina mata hankali ne.
Ganin tana kallon sa sai yayi murmushi dan ya fahimci dalilin kallon kafin yayi magana tace, “Duka nasan komai a kanka kamar ka sani a kaina, amma ka manta wacece ni a wajan….” Saurin dakatar da ita yayi yace, “Baki sanni ba ban sanki ba, yau kika fara ganina nima yau na fara magana dake, ban zo nan da a tuna wata magana da ta wuce ba, ban zo nan da a tuna wani ko wata ba, haka ban zo nan dan a bani labarin wata alaqa ba. Shi aure yana faruwa ne in Allah ya qulla babu ruwan Allah da alaqa ko wani ko wata, kuma ita k’addara takan zo a kan abinda baka yi tunanin ba, domin wani lokacin sai wani abun ya faru sannan k’ofar alkhairi zata bud’e maka ba tare da ka fahimci hakan ba, kafin faruwar hakan baza ka kawo ba amma in ya faru in ka zauna zakayi tunani ashe daman saboda kaddarar da Allah ya rubuta min aka yi kaza da kaza.”
Shiru tayi tana jin sa kalaman Fidy suna fad’o mata musamman in tana cewa akwai kalamai a bakin Ibrahim ta kuma yadda domin yadda yake magana dole ba su shiga zuciyar ka, yace, “Rukayya ki saka a ranki baki sanni ba, nima zan saka a raina ban sanki ba sai da nazo neman auren ki, in kika ce zaki tuna baya babu abinda zaka ciki cimma a rayuwar ki domin kuwa duk abinda ya wuce ana so ka barshi a ya wuce ka kalli abinda zai zo kuma. Ki d’auke ni matsayin mai sonki har abada baza kiyi dana sani ba, kamar yadda na nake so na d’auke ki mai sona dan nasan bazan yi dana sani ba nima.”