← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 93

Sashe 51

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falo ya smau Ameena tana shirin wucewa yace, "Ameena." Ta tsaya tana kallon sa yace, "karb'i wannan in ji Yusuf." Ta saka hannu ta karb'a yace, "da kin sani kun gaisa ko babu komai Zaytun ta had'a ku, amma in kina ganin hakan yafi miki daidai kar ki damu." Ameena tace, "bana cikin walwala ne wallahi."
"Meya same ki?."
"Kawar mu Fiddausi ta dawo daga wani waje labarin babu dadin ji shine ya saka baba Jin dad'i ko Zaytun din ma ban so ta dawo ba takura min zatayi." Yaya Adam yace, "ga kuma Al'ameen." Sai tayi murmushi bata ce komai ba yace, "in kin warware daga damuwar zamu yi magan dake." Da to ta amsa ta wuce ciki zuciyar ta cike da mamakin meyasa Yaya Adam ya bar Yusuf yazo k'ofar gidan har yake cewa da ta sani sun gaisa dashi? Kenan ya yafe masa ko kuma wani abun ne daban?.

Da Zazzabi mai zafi Yusuf ya koma gida kai tsaye wajan Ammah ya wuce ya same ta a inda ya barta yana shiga ya zauna akan kujera baiyi magana ba tace, "har ka kai ta?." Kai ya d'aga kafin yace, "kaina ciwo yake min Ammah."
"Sannu ka sha magani."
"Ki kama min ki kama min kan dan Allah." Jin abinda yace sai ta taso ta dawo kusa dashi ta kama jijiyoyin kan nasa yadda suke harbawa zai tabbatar maka da ciwon da kan yake yi tace, "kan ka yana ciwo kam, Sannu." Addu'a ta dinga karantowa tana yi masa tana tofasa a kan nasa duk abinda yazo bakin ta yi take yi cikin ikon Allah taji harbawar ya ragu ta kalle shi taga ya lumshe ido tace, "Sannu. Jikin ka ma da zafi sosai kaje ka sha maganin ka."

Ameena yake gani a Idon sa yadda ta juyo ta kalle shi da kallon sa da tayi suka had'a ido da yadda ta juya kamar bata ganshi ba shine yake sakawa bugawar kan nasa ta k'aru sosai. Ameena shine abinda zuciyar da take fad'a amma gangaar jikin sa bata bashi wannan had'in kan yadda ya kamata. Duk da an samu canji sosai amma ba irin canjin da yake so ba, so yake ya samu karifin guiwa sosai amma ina ya rasa wannan damar da ya motsa sai ya sare guiwar sa tayi sanyi qalau. Ammah tace, "ko Mubakar yazo ya mayar da kai gida?." Ya girgiza kai alamun A'a sai ta kyale shi a wajan ta kawo masa magani da ruwa yasha sannan ta bar wajan. Kwanciya yayi a kan kujerar kamar maraya yayi shiru abubuwan da suka faru a baya suka dinga fad'o masa a rai ya lumshe ido ya tashi zaune sosai yana kallon falon kamar mai son gano wani abun a ciki sai kuma ya mik'e ya fita.

Book3 yana ja ina ja.😭😭

#Mai daki
#Book3
#Paid
#500
#Nana Haleema

Book3
028

        Kai tsaye gida ya koma bai ma kalli b'angaren Asiya ba na Ameena ya shiga yayi k'ura sosai amma haka yake jin dad'in zaman gidan, kitchen ya shiga babu sauran kayan amfanin a ciki ya fita ya hau sama har d'akin sa ya zauna a kan gado yana kallon gadon. Ameena yake gani a kwance a kan gadon tana yi masa murmushi shima sai yayi murmhsin yana kallon ta sai kuma ya tuna d'azu da ta kalle shi tayi kamar bata ganshi ba nan take yaji babu dad'i a zuciyar sa ya kwanta da baya. Bud'e k'ofar yaji anyi an shigo yasan wacece hakan ya saka bai kalli wajan ba tabi d'akin da kallo tace, "ban San me kake ji ba da kake mak'alewa a nan daki duk k'asa." K'arasowa tayi ta zauna kusa dashi tace, "wai ne nayi maka ne kake share ni? Dan na cire kud'i a kud'in ka laifi ne?."

Baice komai ba ta sake kallon sa tace, "meye dan na cire kud'i a kud'in ka ai a ganina ba wani abun bane ba, shine kake wannan b'ata dan kamar na d'auki kudin wani ba mijina ba." Lallai ma yarinyar nan bata da hankali, tayi masa satar kud'i nasu yawa kamar wannan kuma tazo tana fad'a masa maganar banza? Dan taga ya kyale ya fita daga lamarin tane kenan shiyasa take masa wannan maganar bata san haushin ta yake ji ba.

"My love, ka dawo nutsuwar ka kawai bana son wannan rashin maganar taka. Kuma gaskiya abin nan ya ishe ni ace tunda nazo gidan nan anyi Ramadan anyi babar sallah ban koma makka ba, Haba k'amawaye na duk sunje umarar azumi amma ni an barni a nan a zaune. Gaskiya na gaji ya kamata a kaini a kai Umma na itama."  Jin shirin yayi yasa sai ta d'auka bacci yake ta kalle shi taga idanun sa biyu tace, "nifa bana son wulakanci ina yi maka magana kayi min banza kamar baka ji me nace ba."

Tashi tsaye yayi ya kalle tayace, "tashi tsaye." Ta tashi yace, "fita" ya fad'a yana nuna mata k'ofa ta kalle shi tace, "bazan fita ba, d'akin mijina ne babu inda zanje.  Dan wulakanci ina yi maka magana kayi minbanza kuma ka tashi kace na fita?, bazan fita din ba."
"Asiya ki fita."
"Bazan fita ba, nafa gaji da wannan wulakancin naka da kake min, duk abinda nayi maka ai bai kai abinda kayi min ba, har kashe min dan cikina kayi amma ban d'auki mataki ba sai kai mai bakin magana zaka dinga yi min wulakanci akan kud'i? Ka share ni balle na samu wani cikin a ganin ka din wannan ba laifi bane?."

Ya runtse ido wallahi ko maganar ta baya son ji ya kalle ta yace, "Nace ki fita!."
"Bazan fita, bazan fita ba nace, kayi abinda zakayi kuma hannun ka yazo jikina wallahi sai na fasa maka kai da duk abinda yazo hannuna." Damkar hannun ta yayi ya jawo ta ta k'arfi ya cilla ta waje bai tsaya yaga wani abun ya mayar da k'ofar ya kulle ya zube a wajan ya zauna ya tank'washe k'afa a jikin k'ofar kawai ya fara hawaye.

Bai San abinda yake damun zuciyar  sa ba amma yasan yayi rashi na wani babban abu da yake sanya zuciyar sa farin ciki a ko yaushe, hawaye yake amma bai san dalilin zuwan su ba abinda ya sani zuciyar sa tana dana sanin auren Asiya yana kuma neman hanyar da zai raba kansa da ita amma bai san inda zai nemo hanyar ba. A wajan yayi bacci tun yana Jin kukan Asiya har ya daina ji.

      Wayar sace ta tashe shi daga baccin da yayi a wajan  ya mik'e zaune kayan sa duk sun b'aci da k'ura ga wuyan sa ya rik'e sosai ya tashi tsaye ya k'arasa wajan wayar yana kallon fuskar wayar ganin sunan Abbah, d'auka yayi ya saka a kunne daga can b'angaren Abbah yace, "Yusuf kazo gida Yanzun nan."
"Abba bazan iya zuwa ba bana jin dad'i" ya fad'a a sanyaye kamar zai yi kuka.
"Shikenan zan turo Mubakar ya tawo da kai." Ya amsa da to ya kashe wayar ya shiga band'aki ganin har anyi magriba da isha yana bacci.

Sallah ya fito yayi akan sallaya bayan ya idar ya zauna a yana addu'a yana hawayen da ya zamar masa jiki a yanzu, haka kawai yana zaune sai yaji yana kuka har ya saba hawayen a yanzu dan baya iya rike shi ko kad'an, komai yazo bakin sa rok'on Allah yake yi dan zuciyar sa tayi masa nauyi gab take da tarwatsewa. Yana shafa addu'ar kiran Mubakar na zuwa bai d'auka ba ya d'auko wayar ya fito ya sakko ya same shi a mota a zaune ya shiga suka tafi.

A motar Mubarak ya kalle shi yace, "duk ka rame Allah ya yaye maka wahala." Yusuf yace, "kiran na meye?."
"Matar kace da babar ya suka je, mtswww Allah ya raba mu da auren masa tarbiyya wallahi. Kaima ka samu ka saukewa kanka wannan wahalar da take d'awainiya da kai." Yusuf ya kalle shi ya samu kansa da cewa, "Amin Mubarak." Kallon sa yayi kamar zaice wani abun sai ya fasa suka shiga cikin gidan nasu.

Tun daga bakin falon yake jiyo muryar babar ta dan daman bata magana a hankali ko cikin lallami take magana sai ka d'auka fad'a take saboda ihu da harare-harare, ya shiga jiki a sanyaye ya zauna yace, "Abbah gani." Abbah yace, "Yusuf meyasa kake son jawo min magana ne a ko da yaushe?, meyasa kake son dukan matar ka ne? Yanzu meye amfanin kayi mata dukan da har hannun ta zai karye?." Ya kalli Abbah ya kalli Asiya da take zaune da maqalallanhannu ya kalli Babar ta da take aiko masa da harara yace, "Waye yace na dake ta?." Umma tace, "k'arya zatayi maka? Ba silar dukan ne ya saka ka kashe abinda yake cikin ta ba?." Ya kalli Umma yace, "ni ban dake ta ba itama ta sani. Ta shirya k'aryar da ta saba shiryawa ne."

"Wallahi karya kake ka dake ni, dan kawai nazo inda kake ka dinga dukana har ka karya min hannu" Asiya ta fad'a tana kukan gaske dan hannun ta da gaske a karye yake. Yusuf jin tana cewa k'arya ka ke a gaban iyayen sa da kowa nasa sai jikin sa ya sake yin sanyi bakin sa ya d'aure ya d'ago ya kalle ta yace, "inda ni na dake ki da yanzu bakin da zaki yi maganar ma na fasa shi wallahi, ba iya hannu zan karya miki ba dukka k'asusuwan jikin ki zan karya."  Umma tace, "Iyeee! Kuna jin abinda yake cewa ko? Wato Yusuf naga alama tashen rashin kunya kake ji da ita, to kasan da wacce kake magana dan wallahi ba'a tab'a ni ko yarana a zauna lafiya."

Yusuf ya d'ago kai kamar zai mata magana sai ya fasa kawai ya kalli wani wajan daban dan har babar ta ta yake jin haushi in ya sake kallon ta zai iya fad'a mata magana itama, kuma baya son hakan saboda iyayen sa amma gabad'aya ya tsane su.
Chapter 51 · 0% Book details