Sashe 29
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusuf yace, "yanzu ya ake ciki."
"Ga dai zobe ta fito dashi, Gasu a zaune zan basu abin su a kashe case din a nan komai ya wuce. Dana san matar kace ma da baza'a zo nan ba wallahi amma komai ya wuce ai." Ya d'auki zoben ya mik'a musu yace, "ga zoben ku." Ta taso ta karb'a yace, "an rufe wannan case din tunda ga abun ku ya fito, koda nan gaba kar a sake tayar da maganar nan."
"Shikenan ranka ya dad'e, ai da ta fito dashi tun farko da ba'a zo nan sai tak'i tana yi mana taurin kai."
"Yanzu dai komai ya k'are."
"Shikenan ranka ya dad'e."
Ya kalli Asiya yace, "ke ki basu hak'uri." Ta kalle su tace, "kiyi hak'uri." Mai zoben ta Harare ta tace, "babu komai ya wuce." Ya kalle su yace, "na sallame ku" sukayi sallama suka fita.
Bayan sun fita ya kalli Asiya yace, "koda nan gaba ki daina wannan gangancin, mijin ki babban mutum ne haka mahaifin sa hakan ba k'aramin b'ata masa suna zaiyi a duniya ba." Asiya tace, "baza'a sake ba in sha Allah."
"To ma sha Allah. Yusuf zaku iya tafiya babu komai yanzu komai ya wuce." Yusuf ya tashi tsaye suka sake gaisawa dashi sannan ya kalli Asiya ya fita itama ta tashi sum sum tabi bayan ta.
Ko a mota baice mata komai ba itama bata ce ba har suka isa gida ya faka a bakin gate yace, "ki shiga gıda." Bata ce komai ba ta bud'e ta fita shi kuma yana motar ya nufi gidan su.
Sai da ya tsaya yayi sallar magriba sannan ya shiga gidan ya samu kuwa kaf yayyen sa suna nan mazan da k'anin sa ya shiga da sallama ya zauna baice komai ba. Kallon sa dukkan su suke yi kafin Humaira tace, "Yaya Yusuf lafiya kake kuwa?." Bai ma ji abinda tace ba ganin yayi shiru bai amsa ba ta kalli Abbah sai Abbah yace, "Kai Yusuf lafiya kake kuwa?."
A sannan ya kalli Abbah yace, "Abbah mai kace?."
"Lafiya lau kake kuwa? Kaga yadda ka koma?."
"Babu komai Abbah." Ammah da take gefe face, "to ana samun lafiya a wajan mai sab'awa Allah ne? Mtsww har a tsaya tambayar Yusuf Lafiyar sa Qalau dan b'ata lokaci?."
Yusuf yayi shiru tun abinda ya faru a gidan Asiya tace yana shan giya shikenan ko murmushin Ammah ya daina gani yazo ya bata hak'uri yace ya daina amma tak'i yafe masa kuma har zuciyar sa daga wannan lokacin bai sake koda kallon abin ba, tunanin ta ma ya daina balle ya aikata hakan. Abie ya kalle ta yace, "Dan Allah Ammah ki bar batun nan haka, Yusuf ya daina wallahi ni na tabbatar da hakan ba tun yanzu ba. Tun daga wannan ranar bai sake ba." Tayi tsaki kawai bata ce komai ba.
Abbah yace, "Yacase din matar taka?." Yusuf ya kalli Abbah yace, "anga zoben an basu sun tafi." Abbah ya jinjina kai yace, "to Allah ya kiyaye gaba, sai kayi mata fad'a tasan inda zata dinga d'aukar abun magana." Ammah tace, "ga b'arauniyar dai ta bayyana, yanzu aka fara ai badai kace marainiyar Allah ba komai bace? Badai ka sab'a alqawarin da ka d'auka ba?. Hmmm ayi dai mu gani" ta fad'a murmushi tana kallon wani wajan daban.
Yusuf yayi shiru baice komai ba sai yaji zaman wajan ya ishe shi sai ya mik'e ya yiwa Abbah sallama ya fita daga gidan. Abbah ya kalli babban yyayan su yace, "Anya lamarin Yusuf babu wani abun kuwa?." Abie yace, "nima na gani Abbah, munyi magana da Umsan yace min gaskiya a dinga amsa addu'a yarinyar da yake tare da ita kamar ba haka ga barshi ba gaskiya." Ammah tace, "Qalau yake fa sakayya ce kawai take bibiyar sa, tun ba'a je ko ina ba ai gashi ya fara ji a jikin sa ina ga nan da kwana biyu?. Ga b'arauniya nan dai ya d'auko ya kawo har gidan sa."
Abbah yace, "koma meye Allah ya kawo k'arshen sa, satar da yace Ameeena tayi masa ga b'arauniya nan ta bayyana yanzu, babu abinda kuma zai iya yi mata" ya fad'a yana tashi ya fita saboda sallar I'sha.
Bayan kwana biyu.
Yau ta kama ranar Alhamis ranar ake taron saukar alkur'ani na bikin Rukayya su Ameena ne a gaba ita da Zakiyya ana ta karatu sai da aka sauke alkur'ani a gidan sannan aka ci abinci mai rai da lafiya abin rabon da Ameena tayi mata aka raba a wajan kowa ya tafi da murna a fuskar sa gwanin burgewa.
Bayan an watse Ameena ita da Zakiyya da Rukayya suna zaune suna zancen Fiddausi Ameena tace, "rashin jin Fiddausi ya fara damuna wallahi, abin yayi yawa sosai." Zakiyya tace, "bari kawai, ni kaina ya dame ni ga wata damuwar."
Rukayya tace, "meye kuma?."
"Baban Fahad mana ya tabbatar min da ko na zubar da cikin jikina ko ya sake ni." A tare suka had'a Baki suka ce, "Saki kuma?, akan ciki?." Zakiyya tace, "Saki wallahi, abin ya d'aure min kai sosai cikin halak bana shege ba amma yace zai sake ni a kai." Ameena tace, "Akan me to?."
"Wai baya son haihuwa yanzu, baiyi niyar yinta ba ban kuma isa na saka yayi ba."
Rukayya tace, "ikon Allah, yanzu ya za Kiyi?."
"Ban sani ba wallahi kaina ya kulle gabad'aya nima damuwa tayi min yawa, sabbin halaye ya samo Wanda a baya da ita ko kad'an." Ameena tace, "to Allah ya kawo mafita, amma kar ki zubar da ciki gaskiya ki bari zaku daidaita." Ta amsa da amin suka cigaba da tattaunawa akan lamarin kafin ko wacce ta tafi.
Washe gari juma'a bayan sallar juma'a aka saka Rukayya a gaba ana nasiha wannan yace wannan wannan yace wancan, dangi a taru ana biki kowa yana fad'ar albarkar bakin sa. Gıda ya cika sosai da mutane ana ci ana sha cikin wadata da farin ciki. Rukayy tun tana ganin abun kamar wasa sai da ta tabbatar gaske ne a lokacin aka kai ta gidan su İbrahim wajan iyayen sa kafin a dawo da ita gida da yamma Baba ya saka ta a mota ya tafi kaita gidan ta kansa ba tare da anyi taron kai amarya kowa yaje kafin zuwan ta.
#Book3
Book3
018
Amarya a gidan ta tayi sallar magriba tana zaune bayan ta idar tana k’arewa falon kallo madaidaici mara girma sosai kuma ba k’arami ba an saka mata kujera saiti d’aya da table a tsakiya a kan carpert din da yake tsakiya mai kyau mai gashi kamar jikin mage. Tv tana ajjiye Akan tv stand madaidaici itama tv ba babba ba sosai kuma ba k’arama bace ba.
Falon sosai ya burge ta duk kyaun da ake ce mata yayi sai taga yama fi haka san kana ganin sa kaga na amarya dole ya burge ka, da yake akwai hasken wuta ko ita yayi tarr gwanin ban sha’awa sai d’aukar ido yake yi kamar ka d’auke shi ka saka a jaka. Hawayen da take rik’ewa ne suka sakko mata ta goge da sauri dan bata son zubar da hawaye akan tunanin da yake ranta, ganin abun take kamar a mafarki wai wannan gidan ta ne komai na cikin sa nata ne, yanzu tayi aure tana zaune a gidan ta zaman gidan su sai dai taje ziyara ta dawo ta bud’e wannan tace gidan tane.
A bayyane tace, “Allah mai iko mai kuma yadda yaso.” Bata goge hawayen ba bata kuma daina kallon falon ba ta tabbatar ba mafarki take ba gidan mijin tane da Baba ya kawo ta da kansa tayi zaman aure a cikin sa.
“Asslamu alaiki” aka fad’a ana shigowa falon sai ta kalli inda taji sallama suka had’a ido da İbrahim da ya shigo yana sanye cikin shadda blue dinkin babbar Riga yayi kyau sosai fuskar sa d’auke da annuri kamar ko yaushe yana kallon ta.
“Fuskar amaryar a bud’e sannan kuma ga hawaye tana yi kuma ta kasa daina kallon angon nata” ya fad’a cikin tsokana yana kallon ta sai tayi saurin d’auke kanta ta kallo kasa amma bata rufe fuska ba sannan kuma goge idanun ta ba.
Murmushi yayi mai sauti ya shigo yana kallon ta ya dawo kusa sa ita ya zauna akan carpets kamar yadda take kansa ta yana k’asa hawayen bai kuma daina zuba ba sai ma sake yawa da hawayen yayi ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, “Yanzu wannan hawayen da yak’i tsayawa na meye Rakiya? Na farin ciki ne ko kuma na akasin sa?.”
Bata ce komai ba ta saka hannu ta goge idanun nata bata d’ago ba har lokacin balle ta sake kallon sa, sautin murmushin sa taji sai ta d’ago ta kalli gefen sa ta gefen ido sai suka had’a ido yayi dariya ganin tayi saurin d’auke fuskar ta yace, “ana kiran sallar Isha zanje nayi sallah na dawo” ya fad’a yana tashi tsaye yace, “amma dan Allah kafin na dawo hawayen nan su tsaya ganin su yana sakawa wani abu ya d’arsu a raina sai naga kamar baki farin ciki da kasancewa a gidan nan” ya koma ya tsuguna a gaban ta ya saka hannu ya d’ago fuskar ta idanun ta suna kallon kasa yace, “ganin hawaye a wannan fuskar yana tab’a zuciyar Ibrahim, dan Allah ki daina zubar da hawaye yana sakawa naji d’aci a zuciyata.”
Naga motsa ba balle ta dago kai yace, “ki d’ago idanun ki ki kalle ni.” Bata d’ago ba yayi murmushi yace, “baza ki d’ago ba?.”
“Za’a tayar da sallah” ta fad’a a hankali tana motsa bakin ta cikin salo na musamman.
Har cikin ransa yaji d’adin yin maganar da tayi yayi murmushi yace, “in na fasa zuwa masallacin fa?.” Ta d’aga ido ta kalli fuskar sa tace, “sallar fa?.”
“Sai nayi da matata, ko akwai aibu a hakan?.” Ta sake mayar da idanun ta k’asa bata ce komai ba ya tashi ya fita. Kallo tabi wajan dashi tayi shiru na wani lokaci kafin ta tashi itama ta tayar da sallah.