Sashe 74
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Had'a ido sukayi sai kuwa ya gane mai take nufi ya kulle ido ya bud'e a sanyaye yace, "Na daina, in kina tunanin k'arya nake ki tambayi Ammah zata baki labarin wannan Yusuf din na yanzu. Wallahi na daina duk abinda kike tunani, na daina duk abinda kike hange a lokacin baya. Tun daga lokacin da aka sanar da su Ammah ina s.." kafin ya k'arasa ta katse shi tace, "a baki kake fad'a sai na zauna dakai sannan zan sake tabbatar wa, kamar yadda ban san halin ka na b’oye ba a wancan lokacin sai da ma zauna da kai, haka yanzu ma bazan sani ba sai na zauna dakai."
"Wallahil azim duk wani abu da kike tunani a kaina na sauke shi Ameena, shi kuskure in ka aikata abu kad'an ne yake sakawa ka gane ka kuma canja. İn kuma kayi alqawarin canjawa kana addu'a Allah sai ya baka dama kaga ka canja." Ta tab’e baki tace, "to Ina taya wace zata aure ka murnar canjawar ka Yusuf, zata auri sabon Yusuf ba wanda na bari a baya ba. Ina taya ta farin cikin samun ka a hakan.”
Ya rausayar da kai yace, "Ameena kar kice haka dan Allah!." Ta girgiza Kai tace, "na riga nace, ina kallon ka matsayin mahaifin Zaytun zan cigaba da yi maka wannan kallon har abada, na kuma yafe maka duk abinda kayi min. Amma batun na koma gidan ka ka cire shi daga cikin ranka Yusuf, domin ba abu bane da zaiyu ba a yanzu."
"Baki yafe min din ba kenan Ameena, baki daina fushi dani ba, baki cire abinda nayi miki a ranka ba kenan tunda har kika ce haka."
"Na yafe maka Yusuf, na manta da duk abinda kayi kawai bazan koma gidan ka bane saboda yanzu bana sonka!, bana qaunar sake zama dakai a matsayin mijina wanda zamu zauna inuwa d'aya." Yusuf sai a lokacin hawaye suka fara zarya a fuskar sa yace, "na yadda ko bakya sona ki yarda ki koma, a hankali na tabbata zaki so wannan Yusuf din domin ba na baya bane ba wallahi." Ameena ta kalle shi sai ta rufe ido ta bud'e tace, "sam bazan aikata hakan ba, Yusuf yadda kace wancan Yusuf din ya mutu to nima Yusuf ya jima da mutuwa a rayuwata, wannan sabon Yusuf din mahaifin Zaytun ne shi nake kallo a haka amma ba wai wancan ba."
Yayi shiru dan bai san mai zaice ba sai ya zuba mata ido yana kallon ta cikin rashin sanin abinda zai ce tace, "ka manta dani bazan sake komawa gidan ka ba Yusuf, ka cire ni daga ranka bazan sake zama dakai matsayin miji ba. Amma zan cigaba da magana dakai a matsayin mahaifin Zaytun, na kuma yafe maka abinda ma aikata kana sane da wanda ka aikata baka sane duk Ameena ta yafe maka. Amma ka cire batun zata saka zama dakai a gida daya, domin kuwa bazai sake faruwa ba har abada.”
Sai yayi murmushi ya girgiza kai yace, "kodan Zaytun ki taimaka ki sake tunani Ameena." Itama sai tayi dariya kad'an tace, "kai baka san zamanin komawa gidan miji zaman yara ya wuce ba? Kai baka san wannan lokacin ya k'are ba Yusuf?. Ai in zan koma sai dai na koma dan ra'ayin kaina ba dan Zaytun ba, sai na koma ko dan saboda Ammah ban koma dan Zaytun ba ka gane?. Ka cire hakan daga ranka Yusuf domin bazai yu ba, aurena saura kwanaki kad'an ya rage ka ajjiye wannan batun a zuciyar ka domin ba abu bane da zai yu ba Yusuf."
Ya goge idanun sa ya kalle ta yace, "shikenan Ameena na gode da kika yafe min din ma, amma ina so ki sani ko yanzu na fita kika ji labarin na mutu Ameena ki amince akwai soyayyar ki da damuwar wannan abun a zuciyata zan koma ga Allah. Bazan cire rai da na rasa k'i ba sai ranar da na tabbatar an d'aura auren ki, daga wannan ranar ban san a inda rayuwata zata taya ba, kina jin abun kamar wasa ko kamar film ko Ameena?." Sai yayi murmushi yace, "wallahi na rasa ki in ba Allah ne ya kiyaye ba za'a iya rasa ni nima." Ameena tace, "daman lokacin kane yayi, kuma komai yana da sila ma tabbata silar taka kenan."
Sai yayi Murmushin takaici ya kalle ta yace, "haka ne, na tabbata wannan shine silar barina duniya. In kin samu labari ki taya ni d addu'a." Sai jikin ta yayi sanyi sosai a lokaci d'aya ta bud'e baki zatayi magana ya riga ta yace, "tunda zan mutu babu hakkin ki a kaina na gode Allah, amma zan zo ace na mutu a matsayin mijin Ameena ba tsohon mijin Ameena ba, sai dai kash na rasa wannan damar, nayi wasa da damar da na samu a hannuna, nayi wasa da amanar Ameena daka bani, shiyasa na kasa ganin daidai a rayuwata har yanzu. Gani dai yanzu a zaune kamar mai hankali amma ni nasan babu hankalina tare dani.”
Ya kalli su Yaya Adam da yake kallon sa Yayan Bauchi harda hawaye yace, "na gode da damar sake magana daku da kika bani. Yaya Ameena tace bazata sake zamana dani ba, banga laifin ta ba dan ita kad'ai tasan zaman da tayi dani a baya, amma na shaida mata na canja zuciyar ta tak’i amincewa da na canja din. Shikenan Yaya ba hak’ura, amma bazan cire rai da samun ta ba daga nan har Allah ya tashi duniya."
Shiru yayi dan kuka ne yazo masa lokaci d’aya kusan sacan goma yana a haka kafin ya goge idanun sa yace, "kuyi hak'ur" ya tashi tsaye duk da kansa da yake masa ciwo sosai yace, "Na gode da yafe min din da kuka yi iya wannan ya ishe ni duk da na rasa farin cikina na har abada, na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya sake had'a fuskokin mu a aljanna" ya fad’a yana saka takalmin sa yayi hanyar fita har zai fita sai ya juyo ya kalli Ameena a lokacin tana goge hawayen idanun ta tace, "Ameena ki saka ranki har gobe Yusuf yana sonki da kuma sonki zai mutu, yaso ki bashi damar nuna miki ya gane kuskuren sa amma bai samu ba. Ki tabbatar da yana sonki son da a baya baiyi miki shi ba, ki tabbatar da yanzu Yusuf yake sonki soyayyar baya ba komai bace Ameena. Na gode ko bana da rai na tabbata baza ki bar Zaytun tayi kukan maraicin uba ba, Allah ya baki zaman Lafiya a sabon gidan da zaki je, ya baki farin ciki wanda ban baki ba lokacin da kika tare dani" yana gama fad'ar hakan ya fita daga dukka su sun kasa motsawa daga inda suke zaune dan ya gama tafiya da zuciyoyin su baki d’aya.
#Mai daki
#Book3
#paid
#500
#Nana Haleema.
Book3
038
Yayan Bauchi da take zaune a kusa da ita ta kalli Yaya Adam da jikin sa yayi sanyi sosai kana kallon sa zaka fahimci hakan ya kalli Aisha ya sake kallon Ameenan yayi karfin hali yace, “to meyasa kike kuka kuma?.” Yayan Bauchi ta dafa ta tace, “meyasa kike kuka kuma?, kin fad’a masa abinda yake zuciyar ki meye na damuwa?.” Ameena ta goge idanun ta tace, “babu komai.” Yaya Adam yace, “Ameena!.” Gaban ta ya fad’i jin kiran da yayi mata tasan yana nuni da ta nutsu yace, “da ace kin sake sabon aure da ace kin koma gidan mijin ki kar ki tunanin Yusuf ne kawo wani ne daban mahaifin Zaytun a zuciyar ki wnne kike so?.”
Ameena ta sauke numfashi tace, “Yaya maganar nan ta wuce ai ni bana son tuna ta ma wallahi.” Yace, “tambayar ki nayi kawai ki bani amsa.” Tayi shiru bata ce komai ba ta kalli Yayan Bauchi itama ita take kallo ta sauke numfashi ta kulle ido ta bud’e amma batayi magana ba. Yaya Adam yace, “ki bani amsa.”
Tace, “Yaya indai zan samu chanjin da nake fata, bazan sake shiga abinda na fito daga ciki ba, Yaya aure biyu ko a zuciyata bana so Alalh ya sani. Amma ni gidan Yusuf ne bana son komawa, in aure biyun shine alkhairi ne a wajena Allah yasa hakan alkhairi ne dan na tabbatar Yaya Al’ameen bazai yi kwatankwacin abinda Yusuf yayi ba.”
Yaya Adam yace, “shikenan to, Allah yasa hakan shine alkhairi a rayuwar ki.” Suka amsa da Amin ta tashi ta shiga ciki jikin ta a snayaye sosai ya kalli su Yaya da suke goge hawaye yace, “tabbas da ta amince zata koma zan bada goyan baya a kan hakan, Al’ameen bashi da damuwa domin shi da kansa ya amince da Yusuf ya gane kuskuren sa, kuma ko giyar wake yasha abinda ya aikata a baya a yanzu bazai yi ba” ya ja numfashi yace, “tace bata so babu lallai babu dole.”
Yayan Bauchi tace, “Amma yana sonta wallahi bana tunanin shi Al’Ameen yana mata son da Yusuf yake mata a yanzu. Namiji kamar sa yana hawaye akan mace wacce ba uwa ba ai kasan ba abu mai sauki bane ba. Kawai in ta tuna abubuwan da yayi ne baza tayi marmarin komawa ba, sannan tana tunanin in fa ta koma ta koma gidan jiya ne duk da daman akwai halin da bazai canju a halayen sa ba amma daman ko wacce mace akwai halin mijin ta da take hak’uri dashi. Abinda bama ganewa a yanzu in mace ya fito daga gidna mijin ta ya nemi ta koma sai ace sam bazata koma ba, eh da Gaskiyar su saboda in maciji ya sare ka sau d’aya baza kazo ya sake cizon ka ba, amma wani lokacin komawa gidsn mijin shine alkhairi wallahi, ni na gani akan mutane da yawa an koma kuma an canja din abinda aka bari babu sai halayya wacce ba’a raba d’an Adam da ita.”