Sashe 24
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kar ki raina min hankali mana Asiya, ba ke kika shiga d’akina ranar da muka dawo daga Saudia ba? Kin mata ne?."
"Kodai kai ka dainawa rainawa kanka hankalin ba, ta ina nasan inda abu yake da zan d’auka daga dawowar mu ban tab’a shiga d’aki ba ace har nasan inda sark’a take?. Kaga malama bana son sharri."
"Ni nake miki sharrin?."
Tayi tsaki tace, "kai din mana, ubana ne kai?. Ba sharrin kayi min ba? In ba sharri ba an ina nasan inda sark’a take balle na d’auka?.” Bai san ya tsinke ta da maruka biyu ba sai da yaji saukar nata hannun a fuskar sa tana zare idanu ta nuna shi da yatsa tace, "ai na fad’a maka ake ka sake kuskuren dukana sai na rama ko? Na fad’a maka ranar da ka sake dukana sai na rama kuma gashi na rama din. Ka sake kuskuren sake marina wallahi sai na rama.”
Suman tsaye yayi yana kallon ta dan kwakwalwar sa taje hutun rabin lokaci dan ya daina gane komai sai kallon ta akwai da yake yi zuciyar sa na bugawa sosai saboda abinda aka yi wanda bai tab'a zaton za'a yi shi ba. Shi mace ta saka hannu ta mara macen ma matar sa da yake sa iko da ita tace ta mare shi dan raini da kuma iskancin da bai san da me zai Kira shi ba. "Me nayi maka da zaka dake ni? Dan kaje kasha giyar ka tayi maka yawa zaka zo kana yi min hauka? To wallahi nawa yafi k’arfin ka duk abinda kayi min daidai nake dakai wallahi. Uban me zanyi da sark’ar ka da zan d’auka? İn sata nayi ai baza ka ganta a wajan ba tun lokacin har yanzu ai da tuni na siyar, Uwar gidsn kace b’arauniya bani ba.”
Har lokacin bai dawo daidai ba maganar da tayi ce ta saka shi dawowa hankalin sa ya tuna marin sa fa tayi ya kalle ta dan ya rasa ma abinda zai mata ma ya wuce ya kalli sark'ar da take hannun sa ya tuna abinda ya faru a lokacin da ya rasa sark’ar bai San lokacin da ya saka k’afa yayi ball da ita a ba a wajan. Ihu tayi ta mik’e tayo kansa ta chakumi rigar sa tana cewa, "wallahi baka isa ba, shege dan giya dan iska, kuma ka sake dukana wallahi sai na nuna maka mahaukaciya ce ni.” Fincike ta yayi daga jikin sa ya sake ba marika guda biyu wanda ya sakata gigicewa tace, "Allah ya isana, banza dan giya, na fad’a dan giya" ta sake fad’a da ihu ya sake tsinke ta da mari.
Kuka take sosai tana zagin sa ya fita yana jiyo gudun a bayan sa ta biyo shi har bakin gate daga ita sai d’aurin kirji sai mayafi da ta yafa, "na fad’a sai dai kayi duk abinda aka yi min, wallahi ni bazan d’auki ka dinga dukana a banza a wofi ba. Kuma na fad’a dan giya, karya nayi maka ba Shan giyar kake yi ba?. Sai kayi dana sanin kirana b’arauniya a rayuwar ka, wallahi sai na nuna maka ni ba irin matan da zaka wulak’anta a banza bace” Ta fad’a da k’arfi hakan ya fusata shi ya juyo ya tankad’a ta baya ganin tana k’ok’arin rik’o rigar sa ta fad’a jikin mota da ciki tayi k'ara mai k’arfin gaske shi kuma ko ta kanta bai ba ya hau mota ya fita daga cikin gidan ransa a matuk’ar b’ace.
#Mai daki
#Paid
#Book3
#500
Book3
015
Motar Yusuf tana fita k’anwar ta Momi ta shigo gidan gano a kwance a k'asa ta k’arasa wajan a guje tana kiran sunan ta cikin mamakin abinda ya kawo ta wajan, hankalin ta ya tashi ganin idanun ta biyu amma yadda take cize baki tana yarfe hannu zai nuna maka tana jin ciwo sosai. A guje tayi waje k’arasa inda taga direban Asiya din aka taimaka aka saka Asiya a mota aka tafi asibiti.
Da yake private suka je karb’ar gaggawa aka yi mata aka kwantar da ita Momi ta kira Umma ta sanar da ita abinda yake faruwa zuwa wani lokaci kad'an Umma ta hallara a asibitin hankalin ta a tashe sosai. Bayan sun fito daga d'akin da Asiya take dan ba private room bane d’aki ne mai mutane guda biyar dole suka fito waje dan su tattauna ta kalli Momi tace, "Wai Meya faru ne haka? Meya same ta?.”
Momi tace, "wallahi ban sani ba, Nidai nasan motar mijin ta tana fita na shiga na ganta a kwance a harabar gidan masu aiki na kawaye da ita." Umma tace, "kenan yasan tana wajan a kwance ya fita ya barta? Karfa shine ya sake dakar min ita wallahi bafa kyale shi zanyi ba."
"Wallahi ban sani ba Umma, sai dai in ta farka zamu ji abinda ya faru."
Umma tace, "da aka duba ta ne aka ce?."
"Nurse din cewa tayi cikin jikin ta bai zube ba amma in aka sake maimaita irin buguwar da tayi zai iya fita dan ta bugu a cikin nata sosai.” Umma ta girgiza kai tace, "nasan sai zuwa gobe zamu bar nan, zanje gida zan dawo zuwa anjima keda Fauziyya ku zauna da ita kafin na dawo. In ta farka goben naji abinda ya faru" daga haka Umma tayi gaba ta koma gida
Asiya tun daren ta tashi daga bacci ta tashi zaune Fauziyya ta kalle ta tace, "Sannu, ya ciwon ciki?." Asiya ta shafa cikin tace, "kar kice min cikina ya zube." Fauziyya tace, "bai zube ba yana nan, amma dai yana gab da zubewar dan bugewar da kika yi kiris ya rage mai zubar dashi ba." Bata sake cewa komai ba tayi shiru tana kwafa a zuciyar ta dan wallahi sai Yusuf ya gane kuren sa akan abinda yayi mata.
Da safe kafin Umma tazo ma sun baro asitinin kai tsaye gida suka wuce Asiya sai cize baki ake kamar wacce take nak’uda. Bacci tayi sosai koda ta farka abinci taci sai yatsina take abincin ba nama ba haka ta saba ci ba, sai da Umma ta tabbatar ta huta sosai sannan ta kira ta ta zauna duk suka zagaye ta kowa so yake yaji abinda ya faru Umma tace, "ya kike jin jikin naki?." Asiya tace, "da sauki Umma."
"Meya faru haka? Fad’uwa kika yi a harabar gidan naku?." Asiya ta had’e rai tace, "Yusuf ne ya dake ni, wai ni zai kalla yace nayi masa sata harda marina shine na rama dana sakko sai ya ture ni na fad’i cikina ya bugi mota. Yanzu da cikin ya zube bashi da asara.”
Umma da mamaki tace, "ya kuma dukan ki kuma dai? Wai shi waye ya fad’a masa na kai ki gidan sa dan ya dinga dukan ki? Dan yana da kud’i muna samun abinda muke so ba hakan yana nufin zai mana iskanci mu d’auka bane bafa. Zan bashi mamaki fa bai San wacece ni akan y’ay’ana ba.”
Maimuna tace, "Ai wallahi Umma laifin ki ne, ace wai namiji kamar Yusuf ya gagara zama yadda muke so?." Umma tace, "Barni dashi ai ya tab'a abinda yafi karfin sa yanzu kuma ai. Ke Asiya kiyi wanka anjima muje gaban iyayen sa a yiwa tufkar hanci domin bazan lamunci duka ba wallahi. Dan na kai shi kotu a wannan yanayin ba wani abun bane ba a wajena. Gwara na sanar da iyayen sa san abinda za’ayi.”
Momi tace, "kuma dan wulakanci ta kwana ta tashi a asibiti amma ace ya gagara zuwa ya ganta yasan wanne hali take ciki, an raba shi da uwar gidan ma amma duk da haka bai zama yadda ake so ba, Kullum lamarin sa sake yin gaba yake yi, in aka taro shi a nan sai ya koma nan.” Umma tace, "ai bazan jira komai ba wallahi daga nan sai gidan su dani da ita zamu je, banga dalilin da zai dinga dukan ta ba ai ba baiwa aka kai masa ba, shi ya gano yace yana so. In ma satar tayi sai me ba kayan mijin ta bane ba?."
Baba da ya shigo yake jin mai yake cewa ya kalle ta yayi murmushi tare da girgiza kansa ya rasa wacce irin macece da ba’a tab’a mata yara a zauna lafiya, ko waye kai zaku yi fito na fito dashi bata kunyar hakan ko kad’an yace, "Ai Atika a haka duk yaran ki zasu k’are wallahi, akan turbar da kika d’ora su babu mijin da zai iya zaman aure dasu. Duk inda suka je sai sun dawo gaban ki kamar yadda babbar su take a gaban ki yanzu, Ita kanta Asiya din k’arshen ta irin na Maimuna zai zama indai baki d’ora su akan turbar gaskiya ba. Ko bani da rai ki rubuta ki ajjiye matuk’ar baki canja daga yadda kike ba a haka za’a k’are wallahi.”
Umma ta kalli Baba tace, "a kanka, babu abinda zai samu auren ta in sha Allah. Ni ban tab’a ganin uban da yake yiwa yaran sa bak'in ciki ba sai kai, tana zaune a gidan ta muna samun duk abinda muke so kace wai k’arshen ta irin na Maimuna zai zama?, bana son irin haka in baza kace Allah ya gyara ba kayi shiru ba ka kyale mu ai babu lallai sai kayi magana a kai. Wannan ai bak’in Hali ne kamar ba kai ne uban su ba?.” Baba baice komai ba ya wuce su kawai Fauziyya ta kalle shi bayan ya wuce tace, "Baba yana da damuwa wallahi."
Umma tace, "kyale shi, ke tashi kije ki canja kaya kizo muje gidan nasu kafin dare yayi." Asiya ta tashi dakyar ta shiga d'aki tana jiyo Umma na mita ta saka kayan Momi da hijjabi ta fito ta tarar Umma har ta saka hiijjabi suka fita daman driver Asiyan yana waje tunda suka dawo ko ya fita zai dawo dan haka aka ce masa suka shiga mota sai gidan su Yusuf.