← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 93

Sashe 64

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya tace, “Nidai kawai kayi hak’uri basai na fad’a ba. Ka yafe min kawai na koma dan Allah.” Sai yayi hanyar barin wajan tace, “zan fad’a ka tsaya.” Ya dakata yana kallon ta tace, “Allah ya sani tun kafin nazo gidan ka na tsani matar ka saboda ta fini kyau, duk abinda nake fad’a a kanta ina nuna ina sonta karya nake wallahi. Burina nazo gidsn kawai na fitar da ita na mallake ka ni kad’ai.” Yusuf ya kalle ta yace, “Me kika k’ulla me akan hakan?.”
“Tun daga kiran wayar ka da nace nayi ta d’auka ta zage ni, da zuwan su Yaya Maimuna kai kaya gıdan, da sace sark’a, da ce maka da nayi tace na sauka a hanya da muka tafi daga nan, da cewa Umma tazo ta mata wulakanci, da ranar ma da ka rabu da ita wallahi duk karya nake babu abinda Ameena ta sani a kai. Ina amfani da wayo na da basira da kuma rashin bincike da baka yi na isar da abinda nake so na isar kuma sai da Ameena ta bar gidan ka naji dadi. Gashi na fad’a maka dan Allah kayi hak’uri nidai ka mayar dani na dawo gidsn ka na cigaba da zama.”

Yusuf kallon ta yake yi dan abinda tace bai ishe shi ba yace, “Daga nan kuma sai akayi me?.” Asiya tace, “Nidai a bar maganar dan Allah.”
“Sai kin fad’a.”
“To shine na cigaba da yi maka magani wajan kar ka komawa Ameena sannan kome zanyi baza ka iya d’aukar mataki a kaina ba balle ka iya saki na, Nidai kayi hak’uri ka yafe min na koma dakina dan Allah.” Yayi Ajiyar zuciyar ya kalli su Ammah da suke kallon ta yace, “baki da hankali daman ashe? Baki ji nace miki saki uku ba tun farko? Kina so kice ana mayar da saki uku ne?.” Ta rausayar da kai tace, “to ai babu wanda yasan saki uku ne kawai ka mayar dani bazan fad’awa kowa ba.”

A fusace yace, “in na sake ganin ki a gidan nan wallahi sai na b’alla miki kafa ba hannu ba, zaki tashi ko sai na saka kare ya taka ki?”ya fad’a a fusace bata san ta zabura ba ta mik’e tana kallon sa tace, “kayi hak’uri dan Allah. Ammah ki bashi hak’uri ya mayar Dani.” Ammah tayi shiru bata ce komai ba Yusuf yace, “ki fita na ce, in Baki fita ba zan yi maganin ki wallahi.”

Mubakar ne yazo wajan gani Asiya sai ya kalle ta yayi dariya yace, “A’a b’eriya uwar y’an sace-sace, me kike yi a anan?.” Yusuf y kalle shi yace, “daga yau in ka sake ganin ta a k’ofar gidsn nan ko a k’ofar gidana ka saka ayi mata dukan tsiya.” Mubakar yace, “an gama yallabai.”
“Karen nan yana nan?.”
“Yana nan mana, a sakar mata shi ne?.” Jin hakan sai Asiya ta fita da sauri Mubakar ya bita dan wallahi sai ya sake mata karen kodan ta gane kuren ta. Yana fita zata fita daga gate din ya k’arasa wajan karen da sauri ya sake shi sai kuwa yabi bayan ta a guje ta fita da gudu shi kuma ya dinga dariya dan ya tsane ya tsana mai muni.

Gudu take a layin su Al’ameen sai da tayi nisa sannan ta tsaya tana waigen baya tana kuka shab’e-shab’e. Hakki take ga wajan babu kowa sai iya kad’ai a farko da k’arshen layin sai wasu maza da ta hango su uku suna nufo inda take. Suna zuwa tana juyowa ta kalle su gaban ta d’aya ya fito da wuk’a yace, “ko ki kawo kayan hannun ki ko na soka miki.” Jikin ta ya fara rawa sosai sai taji wuk’a an d’ors mata a bayan ta hannu na rawa ta d’auki wayar ta bashi gashi a bayan wayar atm din ta yake suka bar wajan a guje ita kuma haka ta tafi gıda tana kuka biyu abu biyu ya tarar mata.

Asiya na fita Ammah ta kira Yusuf da ya koma ciki yazo ya zauna Abbah ya kalle shi yace, “meyasa kayi mata saki uku? Meyasa baka dawo da ita ba?. A yadda kake din nan ai kana buk’atar mata.” Yusuf ya kasa magana yayi shiru dan ransa a b’ace yake sosai Ammah tace, “da ka sani ka dawo da ita dan wacce kake son dawo da ita baza ta dawo ha Yusuf.”

Sai ya kalle ta ya raussyar da kai yace, “ki daina min baki Ammah, ki taya ni da addu’a kawai zata dawo in sha Allah, kuma ai na fad’a muku ni na rabu da ita tun kafin tazo nan” ya kalli Abbah yace, “Abbah na canja bani bane wallahi, zan gyara kuskurena bazan saka aikata abinda na aikata ba, kayi hak’uri ku saka baki ta dawo wajena bazan saka ku dana sani a wannan lokacin ba, ina son Ameena ina qauanr Ameena, ban San Ina zan saka kaina ba in na rabu da ita ba, kayi hak’uri ka tallafa min wallahi bazan sake bata.”

Ganin kuka yake yi sosai sai jiki Abbah yayi sanyi Yusuf ya tashi akan guiwar sa ya k’arasa gaban su yace, “zuciyata kullum bugawa take yi bugu na wuce ka’ida, anyi kuskure na sani amma a bani dama na gyara kuskuren nawa, na aikata laifi na sani amma a bani dama ba gyara laifin bawa, ina son Ameena wallahi bazan sake yi mata abinda zatayi kuka ba indai ba na farin ciki ba. Kuna ji a nan abinda tace tun kafin tazo gidana bata son Ameena, Wallahi akwai saka hannun ta a lamarina duk da nasan wani abun laifina ne. Abbah tunda na had’u da Asiya shikenan zamana da Ameena ya lalace, a wannan lokacin in ba zancen Asiya akayi min ba bana jin dad’i Amma, hakan ya saka nake ganin kamar itace take sakawa ki hana ni kula Asiya, na yarda na amince nayi kuskure babba amma zan gyara in ka bani dama ta biyu. Ammah shaida ce ina son Ameena, wannan soyayyar tare tana nan sai ma gaba da tayi, wallahi ko a baya indai nayi mata abu ssi nayi dana sani, to meyasa nake yi din indai nasan zanyi dana sani? Shine ban sani ba…!” Ya fad’a yana kuka sosai mai tsuma zuciya mai kuma sauti.

Ya sake cewa, “Ammah a wannan Karon in ban samu Ameena ba zan iya rasa raina, abinda nake ji a zuciya a yanzu yafi wanda naji kafin na aure ta, ina sonta ina son dawo da ita amma ban san ya zanyi ba. Ina so na bata farin cikin da ban bata ba a baya amma guiwa ta sanyi take yi a ko wanne lokaci saboda bani da hanyar da zan bi dan na cika burina. Yayanta yace ya sake ganina sai ya saka anyi min duka, amma zan jure ko kashe ni zai saka ayi zan jure zan koma walalhi sai dai a dawo muku da gawata Ammah, in gawar tawa aka kawo ku yafe min ku cewa Ameenan ta yafe min kar naje lahira da hakkın ta a kaina kamar yadda zanje da soyayyar ta. Zan yi kokarin da yakin dawo da ita sai inda karfina ya k’are, addu’a nake so ku yi min kawai koda baza ku saka bakin ku ba, dan nasan akwai ciwo abubuwan dana aikata kuna jin kunyar Adam sosai, amma zanyi da kaina in sha Allah, nine na lalata kuma ni ne zan gyara, ko ni ko rayuwata” ya fad’a yana tashi ya fita yana goge idanun sa Ammah ta bishi da kallo tana hawaye sosai.

Bayan ya fita Ammah ta kalli Abbah tana kuka tace, “Yusuf zai rasa hankalin sa fa.” Abbah ya sauke numfashi yace, “barshi ya sha wahala koda Ameena zata dawo yasan ba ta sauki ta dawo hannun sa ba, koda zata dawo yasan da cewa tayi masa alfarma ne bata dawo dan wani abu nsa ba. amma ni nasan bazata dawo ba domin Adam bazai bar Ameena a hannun Yusuf ba a karo na biyu ba.” Ammah ta share idanun ta tace, “Allah Sarki zuciya, uwa da d’anta, tausayin sa nake ji sosai, duk da banza ce ina so ya dawo da ita ba in Humaira ce bazan ce ina so ta koma ba, Amma ina jin tausayin Yusuf sosai wallahi.”

Abbah ya sauke numfashi yace, “kiyi masa addu’ar kamar yadda yace Allah ya dawo dashi cikin hankalin sa kawai.” Ta kalli Abbah yace, “Amin, ko ina ya tafi ma oho. Shiru Abbah yayi bai amsa ba amma shi kan sa yaji tausayin Yusuf sosai ya kuma jii a ransa ya canja din kamar yadda yace. Da za’a bashi dama tabbas da za’a ga canjin amma damar cs baza ta samu ba.

A haka Asiya ta koma gıda a haukace tana ta samu Umma Sakina tana rashin mutunci akan kud’in ta Asiya na shigowa tace, “Ko ki bani kud’ina ko na kai Uwar ki tayi zaman prison.” Asiya tana kuka sosai cikin nadamar fitar da tayi tace, “a tare ni an kwace wayata da atm din nawa a hanya, nasan kaf kud’in da suke ciki yanzu sun kwashe. in ma ku kuka tura a karb’a wallahi sai an biya ni ai ba ku kuka tara min kud’in.” Umma tace, “Asiya ki bada kud’in kinga ganin rashin mutuncin da ake min.”
“To ina na gansu? Ina naga kudin bayan kun saka an kwace katin nawa? Wallahi sai Kun biya ni” ta fad’a tana ihu tana kuka sosai.

Umma Sakina tace, “wannan ku ya dama kuma ai, abinda na sani kawai kudina in gobe tayi banga kudina sun shigo ba wallahi sai na kama uwar ku Atika” tana fad’a ta juya ta tafi. Maimuna ta kalli Asiya a fusace tace, “Dallah malama ki bada kudin daga baya duk inda zan samo miki zan samo na biya ki.” Asiya kuka take yi cikin bak’in ciki tace, “Banda y’an dabar da aka saka suka kwace min katin nawa a hanya? Wanne kud’i kike so na baku bayan nan? Wallahi nima sai an biya kud’ina nasan duk shirin ku ne bazan yafe ba wallahi” ta fad’a cikin ihuuu dan kud’in ta kawai take ji in aka kwashe an cuce ta.
Chapter 64 · 0% Book details