Sashe 20
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rukayya ta girgiza kai tana hawaye tace, “Haka ne Umma, nima na amince da hakan wallahi. Tunda nasan ina addu’a ba dare babu rana na kuma bawa Allah dukkan lamarina na kuma bar masa zab’i na tabbata shine ya zab’a min Ibrahim, zab’in Allah shine zab’i dan haka na karb’i abun hannu biyu Umma.” Umma tace, “Haka nake so naji daman daga bakin ki, Nima na tabbatar miki da baza Kiyi kukan bak’in ciki ba Rukayya, in sha Allah farin cikin da zaki yi sai ya ninka wanda kike yi a yanzu, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman Lafiya yasa babu saki ko yaji a zamantakewar auren ku.” A hankali ta amsa da amin ta tashi ta shiga cikin d’aki ta d’auki waya da niyar ta sanawar dasu Ameena abinda yake faruwa.
Tunda Yusuf ya shiga wajan Asiya da safe ya same ta a zaune bakin ta a kumbure alamun dukan da yayi mata jiya ne ya jawo hakan ya zauna yana kallon ta jiki a sanyaye kafin yayi magana tace, “Ashe daman kana shan giya ban sani ba?.” Ya runtse ido yana jin zafin kalmar yana shan giya har zuciyar sa, Allah ya sani yana so ya daina amma in ransa ya b’aci in bai sha ba baya jin dad’i.
Ya gyara zama yace, “Asiya tsautsayi ne ya kaini ga hakan amma ba halina bane, Kiyi hak’uri da abinda nayi miki a jiya ban san hakan ya faru ba.”
“Kenan ka daki banza ko? Ka shayu ka dake ni kana tunanin ka yiwa banza ko me?.”
“Shiyasa nazo na baki hakuri nasan ban kyauta ba.”
“Wallahi bazan hak’ura ba sai na sanar da iyayen ka, akan ne zaka dinga dukana ai ba dan duka aka kawo maka ni ba. Sannan daman har giya kake sha kuma nake zaune dakai ban sani ba?, ai wallahi bazan iya zama da dan giya ba sai maganar nan taje wajan iyayena, ko ka daina shan giya ko kuma kasan abinda za’a yi.”
Yusuf yace, “Haba Asiya hak’uri fa nake baki meyasa baza ki iya b’oye sirrin mijin ki ba?.” Asiya ta kalle shi tace, “na b’oye ka sake sha nan gaba kenan ko? In kaje ka sha tafi k’arfin kanka kazo ka sake dukana ga jaka an kawo maka har gida, wallahi bazan iya ba.”
Yusuf yace, “Meyasa kike haka ne? A kaf duniya daga ke sai Ameena ne kuka san da maganar nan, dan Allah ki fad’awa kowa nayi alqawarin zan daina In sha Allah.”
“Ita Ameena din sau nawa kace mata zaka daina? Ka daina din?. Kaga Yusuf ni wallahi ba Ameena bace bazan d’auki abinda ta d’auka a kanka ba, in manya suka shiga maganar ko baka so ai ka daina.”
Yusuf ya dafe kai babban tashin hankalin sa bai wuce iyayen sa su san da maganar yana shan giya ba yace, “Dan Allah kar ki fad’awa kowa.” Ta kalle shi tace, “Amma ka iya dukana bayan kasan ina da k’aramin ciki.”
“Na karb’i laifin nawa, Kiyi hak’uri.”
“Zanyi hakuri amma sai ka bani wani abun.” Da sauri yace, “Kamar ne kenan kike so?.”
“Zan rike sirrin bazan fad’awa kowa ba tunda kace baza ka sake ba, amma sai ka bani naira miliyan d’aya.”
Da mamaki yake kallon ta jin abinda tace yace, “miliyan d’aya? Yanzu dan zaki rufawa mijin ki asiri sai ya biya ki?, baza ki iya b’oye sirrin sa ba sai ya baki wani abun?. Kina da hankali kuwa?.” Ta Harare shi ta ce, “bani da hankali, ka bar kayan ka ni kuma wallahi sai yau Ammah tasan da labarin nan” ta fad’a tana niyar tashi zata bar wajan yayi saurin cewa, “shikenan zan baki, amma miliyan d’aya yayi yawa ai ba hauka ake ba, zan baki dubu d’ari.” Banzan kallo tayi masa tace, “Almajira ce ni da zaka bani dubu d’ari? Ko ni yanzu na kai matakin kyautar ta, in zaka bada dubu d’ari bakwai ka bayar in baza ka bayar ba gidan Ammah kai tsaye.”
Yusuf ya lumshe idanun sa ya rasa wacce mata Allah ya had’a shi da ita ace matar sa baza ta iya rufa masa asiri ba sai ya biya ta, ya kalle ta yana jin d’aci a zuciyar sa kafin yayi magana tace, “Wallahi bazan rage ba, in zaka bayar kanka in baza ka bayar ba duk bai shafe ni ba.” Ya zaiyi baya so Ammah tasan labarin dan Allah kad’ai yasan tashin hankalin da zata shiga hakan ya saka yace, “shikenan zan tura miki, amma koda wasa bana so wani ya samu labarin nan.” Tayi murmushi sannan ta jiyo ta kalle shi tace, “hannun kuturu da makaho, tura min sannan nayi nawa alqawarin.”
Waya ya d’auka yana dannawa kafin ya hasko mata wayar yace, “Gashi na saka miki.” Ta kalla taga kud’in sun shiga tace, “Nayi alqawarin babu wanda zai sani, amma wallahi ka sake sha ka dake ni sai na fad’a in baka so na fad’a kuma naira miliyan biyu, in kuma ba haka ba wallahi Ammah da Abbah sai sun San kana shan giya.”
“Ke baki iya rufin asiri ba a rayuwar ki?.”
“Ban iya ba, kud’i kawai na sani.”
“Wai ya akayi na d’auko ki ne?.” Da sauri ta kalle shi tace, “me kace?.” Baice komai komai ba ta kalle shi tace, “koma me kace zama da Asiya dole, kuma dole ayi abinda nake so in ba haka ba aga ba daidai ba”tana fad’a ta barin wajan ya bita da kallo ya sauke numfashi mai nauyi yana jin sa kamar ya rasa wani abu mai mahimmaci a tare dashi.
#Book3
Book3
013
A zaune suke a babban falo kai da ka kalle su kasan mayan mutane ne wanda suka ajjiye naira suke kan tara ta domin shigar su kawai zata tabbatar maka da ko wannen su ba k’aramin mutum bane ba. Suna zaune da alama tattaunawa ake mai mahimmaci dan kowa ya bada hankalin sa ga abinda ake yi Alhaji Bello yace, "ni ban gane abinda Boss yake nufi bafa, wa yake nufi a cikin mu." D'aya daga cikin su yace, "kai yake nufi fa, Taya zaka ce baka gane ba bayan kaine zuwan k’arshe New York da matar ka? Mu ai sai dai muyi maka murna harka ta sauka.”
Wanda yake zaune kusa da Alhaji Bello yace, "Shine abinda na gani, ita ya gani yace yana so a karo na biyu a bashi ita ta sati d’aya kasan akwai ribar da zaka samu ai, nawa ka samu da wacce take can wajan sa?, kawai ka fara murna mu ma kuma a cire mana namu in an samu kar a manta damu.” Alhaji Bello yace, "ni bawai bana son kaita bane tana da taurin kai bazata amince ba, kasan kuma shi bature ne bazai iya mata dole ba."
"Sanin da kayi masa, wallahi yanzu da k’arfi shima sai yayi abinda yake so, kawai ka d’auke ta gobe a kaita shine kawai. Dan wannan ba k’aramin business bane yazo mana.” Alhaji Bello yaja numfashi d’ayan ya kalle shi yace, "Ko kishi kake?." Ya kalle shi yayi dariya yace, "Kai kasan babu macen da zanyi kishi a yanzu, kawai dai ina jin babu dad’i ne in na tuna wacece ita." Mutane biyun suka mik’e d'aya yace, "haka zaka yi hak’uri ka San dabara da zaka yi ka a kaita, kar ka bari lokaci ya wuce in ba haka ba zaka rasa babbar damar da ka samu.”
Alhaji Bello ya mik’e yace, "nasan ma abinda zanyi zata je kuma koda bata so." Sukayi dariya suka d’aya yace, “Ai dole ma taje, ta isa tayi mana asarar wannan damar da muka samu.” Tare suka fito ya hau mota ya nufi gida dan dole ma Fiddausi ta amince ya kai ta New York dan ya samu kudi.
A gate na biyu na cikin gidan da ya hango Fiddausi da Naja’atu da kuma ma'aikatan wajan ana fad’a akan sai ta fita su kuma sun hana, Naja’atu tana janta baya tana sake kwacewa lallai sai ta fita. Kana ganin ta kasan akwai fitar hankali a tare da ita komai yin sa take ba a daidai ba kamar mahaukaciya. ganin motar sa duk sai suka bar wajan tayi sufa zata fita zuwa gate na gaba mai gadin wannan gate d’in ya d’auke ta cak yayi baya da ita a lokacin Alhajin ya faka mota ya fito yana kallon komai.
"Wallahi sai na tafi na bar gidan nan, ku barni na tafi dan Allah" ta zube a wajan tana kuka sosai Alhaji balle ya k'araso yana kallon ta. Naja’atu ta tsuguna kusa da ita tace, “ki tashi mu koma ciki Fiddausi baza su barki kije ko ina ba wallahi.”
“Babu inda zanje sai na bar gidan nan yau.” Alhaji ya k’araso inda take yace, "kina so kije gida ko?." Bata amsa ba sannan bata kalle shi ba yace, "in kin shirya anjima kad’an zan saka a kai ki a jirgi, in kina so ki taso ki biyo ni ki shiga gida in bakya so ki ta zama wallahi ko gate na gaba baza su barki kije ba.."
Ta d’ago tana kallon shi jikin ta har rawa yake yitace, "da gaske zan tafi?."
"Zaki tafi na tabbatar miki." Naja’atu tace, “kar kije Fiddausi kar ki bishi wata yaudarar ya shirya miki wallahi bazai kai ki gıda ba, kar ki shiga motar nan.” Fiddausi ta kalle shi dan a tsorace take dashi kafin tayi magana yace, “wallahi babu abinda zan miki jirgi zamu shiga na kai ki har gida, ban tab’a miki alqawari ba ko? To nayi alqawarin babu abinda zanyi miki.”