Sashe 90
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zakiyya tayi murmushi tace, "kyakykyawar zuciyar kenan tana kuma so mata abinda yake sowa a kanta. Duk Wanda ya same ku matsayin kawaye ya gode Allah." Fiddausi tace, "ku fad’a mata ta daina b’atawa mijin ta rai akan hakan, ta daina maganata kar hakan ya kawo sab'ani tsakanin su dan wallahi bazan ma koma ba ni.” Ameena tace, "kedai ki jira muga me Allah zaiyi."
"Bafa zan koma ba nima wallahi, ko ya amince bazan amince ba. Balle ma bazai amince ba domin ban cancanci ya sake kallona matsayin mata ba, nayi rashi na har abada, dan babu lallai na sake samun miji kamar sa. Asarar da nayi bazan mayar da ita ba.”
"Harda wallahi baza ki koma ba Fidy?.”
"Kin ji abinda nace ashe." Ameena ta tab'e baki bata ce komai ba kafin su canja hira zuwa wata hirar daban.
#Mai daki
#Nana Haleema
#Book3
#paid
#500
Book3
044
Suna zaune suna hira aka kira Ameena a waya ta d’auka ganin mai kiran sai tayi murmushi ta saka a kunne tace, “Yaya Al’ameen ka manta dani, ba waya balle kazo kace zaka ganni.” Shiru tayi alamun yana bata amsa sai tace, “da gaske? To bara na tura maka” ta fad’a tana kashe wayar ta kalle su tace, “Bak’o zanyi yanzu” ta fad’a tana danna wayar.
Fiddausi tace, “Sai mu tafi daman aimın jima a gidan.” Zakiyya tace, “nima ina da abin yi” ta fad’a suna tashi suka fito tare har harabar gidan suna hira Zakiyya tace, “wannan gidan naki ya yafi wancan kyau nesa ba kusa ba wallahi, ni kullum sabo yake zamar min.” Tayi dariya tace, “Ni kuma nafi son wancan.” Wayar ta aka kira tace, “to ga Yayana yazo ku jira ku gaisa sai ku tafi” ta fad’a tana d’aukar wayar ta nufi bakin gate din ta yiwa mai gadin magana sai gashi an bud’e Al’Ameen ya shigo.
Dariya tayi da ta ganshi tace, “Yaya Al’Ameen barka da zuwa.” Yayi murmushi shima ya saka waya aljihu yace, “ba wani baraka da zuwa, ko waya kice yau kin tunda da Yayan ki baki tab’a yi ba, ai nayi kokari ma da na shigo mu gaisa” ya fad’a suna tafiya daidai lokacin da suka zo wajan su Zakiyya. Tayi dariya tace, “nayi laifi babba amma a yafe ni” ta kalle shi tace, “Yaya Al’Ameen ga k’awayena, Zakiyya da Fiddausi.”
Fiddausi ta fara gaishe shi ya amsa Zakiyya har ta shiga mota ta fito ta gaishe gashi ya amsa da murmushi Ameena tace, “To Fidy sai nazo gidan, Zakiyya a gaishe da Fahad. Ke kuma Fiddausi kafin nazo naji labari mai dad’i” Fiddausi tayi dariya tace, “to amaryar Yusuf.”
“Ke kuma ta Ibrahim.”
“Rufa min asiri kar Rukayya ta bindige ni” sukayi dariya tare ta shiga mota suka tafi ita kuma ta kalli Al’Ameen tace, “Yaya muje ciki ka sha ruwa.”
“A’a ni daman zuwa nayi na ganki kuma na ganki, gaki nan lafiya lau dake baki da damuwa to me zan shiga nayi kuma?.” Ameena tace, “Haba dan Alalh yanzu sai kazo ka koma baka shiga ba? Dan Allah ka shiga ko ruwa ka sha.” Babu yadda zaiyi haka ya shiga falon ya zauna ta kawo masa ruwa da lemo harda su kayan zak’i da bata rabo dasu. Yasha ruwan yana kallon ta yace, “na sha ruwa. Amma wannan cake din da cincin din nan ayi min packaging na tafi dashi.” Tayi dariya ta shiga ciki ta d’auko pack ta zuba masa ta zauna tace, “wancan satın Yaya Adam ma yazo kwanan sa d’aya ya koma.”
Al’ameen yace, “Haka yace min yazo ya ganki ya koma.” Tayi murmushi b’ata ce komai ba yace, “baki da wata damuwa dai ko?.” Ta girgiza kai tace, “Babu komai Yaya.”
“Kin tabbata? Kar Kiyi min karya fa.”
“Allah babu komai Yaya.” Yayi murmushi yace, “haka muke fata. Wannan k’awayen naki kamar na san su.”
Ameena tace, “ka san su mana, Fiddausi ce fa ta gidan Alhaji Mustapha k’anwar su Zahra’u. Sai Zakiyya ta gidan Malam Mamman.” Al’ameen yace, “ohh! Na gane Fiddausin, ita Zahra’un itace mate din mu duk kusan tare aka tashi. İkon Allah duk kun girma ko wacce tana da y’ay’a.”
Ameena tayi dariya tace, “Eh wallahi ko wacce mu tana da aure da yara. Fiddausin ce ma bata da aure sun rabu da mijin ta.” Al’ameen yace, “Alalh Sarki. To ni zan koma sai na sake shigowa sai mu gaisa.” Ta taka shi har bakin gate sannan ta dawo.
Babu jimawa da tafiyar sakawa yi sallar magriba tayi alwala tayi sallah sai a lokacin ta manya batayi girki ba ta hau saka tayi wanka ta sakko da niyar gkiki Yusuf ya dawo. Yana shigo falon kallon ta yayi yace, “bani abinci Yunwa nake ji sosai.” Ameena ta kalle shi tace, “Wallahi banyi girki ba, amma bara nayi maka yanzu.”
“A’a barshi kawai, bazan iya zama har a girka ba zanje wajan Ammah” ya fad’a yana fita ya bashi da kallo duk sai taji babu dad’i a zuciyar ta.
Bata ma yi girkin ba tana zaune aka yi sallah tayi sallah ta zaune a falon ya dawo shida Zaytun ya zauna ya kalle ta kamar zai mata magana sai ya share aka kira shi a waya yana amsawa. Tashi tayi ta hau saman bai tashi ba sai da ya gama duk abinda zaiyi suna zaune da Zaytun ganin shiru bata sakko ba gashi dare yayi sai ya kashe komai na falon ya hau saman da Zaytun da ta fara bacci.
D’akin ta ya shiga ya sake ta a zaune ya kwantar da Zaytun a kan gadon ya kalle ta yaga kamar bata ganshi ba abin ya bashi mamaki sosai bai ce mata komai ba ya fita ya d’suke kai daga kallon ta yayi kwanciyar sa. A haka suka kwana da safe ya shirya zai fita ya sakko ya sake ta ta shirya zata tafi makaranta ganin sa tace, “Ina kwana.”
“Lafiya lau, ina abincin?.”
“Ban yi ba.” Ya kalle ta yace, “baki yi ba kika ce?. Zaytun ba taje makaranta ba da kika yi Kaga meyasa baki had’a ba?.”
“Nata akwai nan girka ai.” Ya girgiza kai yace, “shikenan babu laifi.” Ya fad’a yana fita itama ta fita ta tafi makaranta. Gabad’aya zuciyar sa babu dai haka ya zauna bai dawo ba sai yamma lokacin da ya shigo ya dawo Zaytun na homework tana ganin sa ta taso tana masa oyoyo ya rik’e ta suka shiga ciki tace, “Sannu da zuwa.”
“Yauwa, ya school?.”
“Alhamdulillah” ta fad’a tana kallon Zaytun tace, “dawo mu cigaba.” Ta dawo suka cigaba da aikin yaga shiru bata kawo abinci ba shi kumayayi alqawarin bazai tambaya ba ya tashi ya hau sama.
Bai sakko ba sai magriba ya fita yaje masallaci daga nan ya shiga gidan Ammah sai bayan i’sha ya dawo gidan ya samu Zaytun tayi bacci ya zauna yana kallon ta yace, “sarkın magana anyi bacci da wuri yau.” Ameena ya kalla ya kalli dining din babu abinci ya sauke numfashi sai yaga t tashi ta shiga kitchen ta dawo tace, “Me za’a dafa maka?.” Ya kalle ta yace, “ki barshi bana ci” ya fad’a yana tashi ya d’auki Zaytun ya hau sama ba tare da ya kalle ya ta ba.
Bin bayan sa tayi ya kwantar da Zaytun idanun ta sun fara cika da hawaye tace, “Meyasa tun yanzu?.” Ya kalle ta bai magana ba ya share ta dan gudun ruwan ta yake so ya gani tace, “yau kwana uku kenan baka cin abincin gidan nan, meyssa haka?.” Cikin fad’a take magana ya lura haka take masa magana in ranta ya b’aci kamar zata dake shi da kuma ba haka take ba sai bai tanka ba ya fita ya barta.
D’akin nasa ta bishi tana shiga tace, “ina magana kayi min banza” sai muryar ta ta fara rawa ta fara hawaye yajuyo ya kalle ta yace, “ya zan miki? Abu kad’an da anyi sai ki fara yi min fad’a kamar ki kika haife ni. Kwana biyu da ya wuce da na dawo kika ce ga abinci me nace miki? Bana jin dad’i kaina na ciwo bazan iya ci ba, shekaran jiya na dawo kika ce ga abinci saboda kar kiga banci ba ja zauna naci amma badan Ina da lafiya ba. Jiya da nazo da Yunwa kika ce min baki girki ba, na tambaye ki dalilin da ya saka baki yi ba?. Yau da safe kika ce min Baki yi ba shima na tambaye ki?.”
Tayi shiru yace, “ban tambaya ba saboda nasan kin yi din duk yadda akayi akwai abinda ya hana ki yi shiyasa nace ki barshi kawai sai naje wajan Ammah naci abinci. Da safe na tashi zan tafi aiki kika ce min baki yi ba bayan kin tashi kuma kin yiwa Zaytun ta tafi makaranta, shima nace miki akan wanne dalili? Ban fad’a ba na wuce na tafi store a haka naje na dawo banci komai ba koda na dawo baki min tayin abincin ba sai da kika ga dama sannan kika ce min wai me zaki dafa min. Me nayi miki? Ban miki komai ba kin d’auki fushi a kaina wanda ban San dalilin sa ba, abu kad’an da nace sai ki fara yi min fad’a kamar kin haife ni akan me Ameena?. Nasan kina gani kamar na daina cin abincin kine kamar lokacin baya in kika yi min adalci da baya da yanzu ba haka abun yake ba, wannan dalilin ya saka da nayi magana sai ki fara fad’a shiyasa nake kyale ki na bar wajan in na tsaya abun bazai yi kyau ba ke kin sani, dan Ina da zuciyar da zata harxuk’a ni raina ya b’aci. Amma kika cigaba da irin wanna d’abi’ar da kike yi ko nace kika d’auka bazan iya jurewa ba.”