← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 93

Sashe 32

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun sa ya kai jikin Fiddausi sai ya kalli Alhaji Bello yace, “jikin ta akwai zafi sosai kuma a yadda abun yake sai mai Lafiya fa, yanzu ya za’ayi?.” Alhaji Bello ya kalli Aliya tace, “wannan baza tayi ba?.” Ya kalli Aliya yace, “yanayin ta baiyi daidai da wacce akace ba gaskiya, sai dai ayi manage kawai” ya fad’a yana kallon Aliya da take kallon sa itama.

Zabura tayi ta k’arasa jikin madubin Fiddausi ta d’auki kwalbar turare tace, “wallahi duk wanda ya matso kusa Dani sai na buga masa, wallahi duk wanda ya tab’a ni sai na fasa masa kai.” Ganin da gaske take sai bata hankalin ta Alhaji Bello yace, “Mutumin zo muje kawai, wannan hauka zatayi maka daman da dai waccan zatayi ne sai a San abinda za’a yi. Amma zan saka likita yazo ya duba ta anjima sai a ka dawo” tare suka fita ta ajjiye kwalbar ta k’arasa da sauri ta kulle k’ofa ta koma wajan Fiddausi nan ta tarar da ita bata numfashi.

A guje tayi kan Fiddausi tana girgiza kafad’ar ta tana kuka tana cewa, “Fiddausi! Fiddausi!! Innalillahi wa’inna ilahir raji’un.” Da sauri ta k’arasa cikin band’aki ta d’auki kofin ruwa ta d’ebo ruwan ta dawo da sauri tana shafawa Fiddausi a fuskar a lokacin ake kwankwasa k’ofa ana cewa, “Aliya ku bud’e nice.” Jin muryar wacce take magana ya saka Aliya zuwa ta bud’e a lokacin Naja’atu ta shigo d’akin Aliya ta kalle ta tace, “k’araso dan Allah, bata numfashi wallahi na shafa mata ruwa duk da haka a sume take.”

Da sauri ta k’araso tana cewa, “Meya faru haka?.”
“Mijin ki ne ya kawo wani har nan wai yayi amfani da ita tana cikin jini, har da cewa yayi amfani dani tunda ita baza’a samu ba.”
“Mun shiga uku mu kam, Mun kawo kan mu inda ba’a san darajar aure ba balle darajar mace.” Aliya kuka take a lokacin Fiddausi ta bude’e ido ta dafe kanta da hannun guda d’aya tana kallon su suna ta aikin jera mata Sannu.

Kanta take dafewa saboda ciwon da yake mata sosai sai kallon su da take yi amma ta kasa cewa komai saboda yadda jijiyoyin kanta suke harbawa kamar zasu tsinke bata son yin magana gabad’aya. Aliya ta kalli Naja’atu tace, “Ko lokacin mu bamu sha wahalar da yake bawa Fiddausi ba, yafi takura mata sosai ya kamata mu san abinda zamu yi akai kafin ya kashe ta da ranta.”

Naja’atu ta koma da baya ta kulle k’ofa ta dawo ta zauna kusa da Fiddausi da take kwance tana hawaye tace, “Na samu waya a hannun masu aikin gidan nan bai sani ba, Akwai lambar wanda kika haddace a gidan? Fad’o na rubuta ko za’a dace ta shiga.” Jin abinda akace sai ta samu k’arfin guiwa ta mik’e zaune dakyar ta jingina da bangon gadon tana fad’ar lambar Abba ana sakawa. Ana kira ya nuna number busy Naja’atu tace, “fad’i ta k’anin ki ko yayar ki amma na tabbatar ta baban ki da babar ki baza tayi ba.”

Fiddausi ta rutse ido tana juya kai cikin azaba tace, “su kawai na haddace.”
“Ki tuna Fiddausi koda maqocin ku ne ko k’awayen ki, ki tuna bamu sani ba ko za’a dace ta shiga.” Kai take juya suwa domin kuwa daga lambar Abba sai ya Mamata haddace bayan su babu lambar wanda ta rik’e a kanta Aliya tace, “ki tuna ko waye ko wace zamu kira shi yanzu mu sanar dashi halin da muke dukkan mu ko za’a taimaka mana,”

“Ban haddace ba!, ban haddace ba!!.” Naja’atu tace, “ko tsohon saurayin ki ne ki tuna wannan ne lokacin da muke dashi. Na gwada na y’an gidan mu kaf bana samu ke mu gwada naki ko za’a dace.”
_ibrahim._ zuciyar ta fad’a mata sai ta bud’e ido da sauri ta kalli Naja’atu ta bud’e baki da niyar fara fad’a mata lambar sa sai kuma ta kasa ta lumshe idanu sai kuka ya dawo sabo.

“Kin tuna ko? Fad’o a rubuta.” Kai take girgizawa tace, “bazan iya ba, bazan iya kiran sa ba Naja’atu.”
Aliya tace, “indai kin haddace zamu iya kiran sa ko waye, a wannan halin da ake ciki neman taimako muke yi babu ruwan mu da waye shi.” Ta sake juya kanta tana kuka tace, “bazan iya ba, ban san da wacce fuska zan masa magana ba, Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un na cuci kaina ni Fiddausi.” Naja’atu tace, “Dan Allah ki fad’a ko za’a dace dan Allah. A yanzu neman d’auki muke ba zancen baza’a iya ba, ki tuna wannan damar kawai muke da ita in baki magana ba zamu rasa ta itama. Ni zan masa magana in ke baza ki yi ba.”

Bud’e ido tayi ta fad’i lambar Ibrahim da yake kanta har lokacin aka kira kowa yana jira yaji zata shiga, number busy ta sake sakawa Naja’atu ta sake kira ta sake rubuta haka ya sake kira cikin ikon Allah ta fara ringing. Kallon su tayi cikin farin ciki dukkan su kallon ta suke ko wacce kuka take yi ana jira aji za’a d’auka amma shiru ba’a d’auka ba har ta yanke. Hannu na rawa suka sake kira amma tak’i yi duk yadda suka kai ga naci tak’i shiga.

Aliya tace, “ki adana mana lambar na tabbata zata yi mana amfani gaba dan bamu tab’a gwada kira ta shiga ba sai a kanta, waye shi d’in ki?” Ta tambaya tana kallon Fiddausi. Ta lumshe ido tace, “tsohon mijina.” A tare suka kalle ta Aliya tace, “amma dai babu matsala ko? Kina ganin in muka fad’a masa koken mu zai taimaka mana?.” Cikin muryar kuka tace, “ban sani ba wallahi, abinda na sani kawai nayi masa abubuwa marasa kyau a zaman mu dashi, tunda nazo gidan nan na fara ganin sakayya akan abubuwan da nayi masa. Tun daga kan zubar da cikina da akayi, amfani dani ta k’arfi, saka ni a cell da duk abinda yake faruwa” ta nuna kanta tana kuka tace, “nice nayi silar rabuwar mu kawai dan nazo gidan nan.”

Hawayen nasu sun tsaya Aliya ta sauke numfashi tace, “babu wanda yake zuwa gidan nan sai ya aikata kuskure makamancin wannan, amma in sha Allah zai taimaka mana in muka same shi a waya.” Ta girgiza kai tace, “duk yadda kuke tunanin abun ya wuce haka, nayi masa abubuwa masu yawa dan ina jin kaf cikin ku na fiku aikata kuskure.” Naja’atu tace, “Gashi kina ganin sakayya ai kina kuma dana sani wacce bata da amfani.” Shiru kawai tayi ta kulle idanun ta bata ce komai ba tana ji kamar ta had’d’iye zuciya ta mutu saboda bak’in ciki.

Ibrahim lokacin da akayi masa waya wayar tana chaji a falo Rukayya tana zaune ita da Amir tana koya masa assignment taji kiran wayar amma bata motsa ba suka cigaba da abinda suke yi. A lokacin ya shigo falon ya kalle ta yace, “Amir baiyi bacci ba? Dare yayi akwai makaranta.” Rukayya tace, “na manta ba muyi assignment bane shiyasa muke yi yanzu. Amma mun gama yanzu sai ya kwanta.”

Ya zauna Amir ya kalle shi yace, “Abba kasan a makaranta Ya Sayyada tace na iya hadda ta.” Yayi murmushi yace, “dakyau haka ake so, ka cigaba da dagewa indai kayi kokari ka iya zan siya maka keke.” Sai kuwa farin ciki ya bayyana a tare dashi yana ta murmushi Rukayya ma haka.

A sannan suka gama ta rufe littafin ta saka masa a jaka tace, “d’auki school bag din kaje ka ajjiye a d’aki.” Ba musu ya d’auka ya shiga d’aki ya ajjiye ya dawo Ibrahim yace, “bani waya ta Amir gata can.” Zuwa yayi ya d’auko ya kawo masa Rukayya ta tashi suka shiga d’aki ita da Amir Jim kad’an ta fito ya kalle ta yace, “har ya kwanta?.”

Ta zauna sannan tace, “Uhum ya kwanta.”
“Number ce aka yi min waya na kira kuma bata zuwa.” Rukayya tace, “sharrin network ne.”
“Meyasa baki d’auka ba da aka kira?.”
“Kawai sai na d’aukar maka waya in an kira ka ban san waye ba?.” Ya kalle ta yace, “ai ni na baki damar hakan ko?.” Sai tayi murmushi tace, “kai wai ko irin b’oye waya da mazasuke yi yiwa matan su baka yi?.”

Yayi dariya kad’an yace, “to me zan b’oye miki? Y’an mata ne dani da zasu kira ni?. To yau ko y’an matan ne dani ai ke zaki fara sani.” Tayi murmushi tace, “Nidai bazan d’auka ba in kana kusa ka d’auki kayar ka amma bada ni ba d’aukar wayar ka in an kira .”
“Tsoro kike ji?.”
“Eh hakan ne, gwara naji tsoron na k’i d’auka dana d’auka kuma naji wani abun ba daidai ba.” Ibrahim ya kalle ta yace, “babu abinda zaki ji ba daidai ba a wayata, zan iya bar miki ita na fita na dawo babu abinda zai faru na tabbatar miki. Rukayya nida nake da mace kamar ki me zai had’a ni da wasu matan na waje?.” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba sai yaga ta fuskar ta canja daman tun d’azu ya lura da yanayin ta ba daidai ba yace,

“Me yake damun ki?.” Ta kalle shi tayi shiru batayi magana ba yace, “tambayar ki nake, me yake damun ki?.”
“Mun kasa samun wayar Fiddausi gabad’aya, bata kira ba’a kiran ta hankalin mu dana iyayen ta a tashe yake sosai shirun nan ko na alkhair ne yayi yawa.” Ibrahim ya kalle ta yace, “wace haka kuma?.” Kallon sa tayi taga babu alamun wasa a tare dashi sai tace, “Fiddausi k’awata.”
“Allah Sarki! Ban santa bama Ameena nafi rikewa, shine kika koma haka kamar mars Lafiya?.”
Chapter 32 · 0% Book details