Sashe 39
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowa yayi daga motar ta gama kulle gate din ya kalle ta itama shi take kallo yace, "Meyasa kika kulle bayan kin san aikina ne? Na hana ki aikin gate d’in nan amma bakya ji ko?.” Shiru bata amsa masa ba sai kallon sa da take yi ya murmusa yace, “kiyi hakuri." Kallon sa tayi kawai bata ce komai ba yayi murmushi suka shiga ciki ya tarar da Amir a kwance a falon yana ta bacci yace, "lallai nayi dare har Amir yayi bacci?" Ya fad'a yana zama ta wuce shi ta kawo ruwa da lemo da abinci ta zauna bata ce komai ba yayi murmushi yasan tayi fushi shi kuma dad’in hakan yake ji dan ko babu komai yasan kula dashi ne ya jawo haushin.
Abincin yaci yasha ruwa sai a sannan ya kalle ya yace, "ayi hak’uri a daina fushi naje wani waje ne shiyasa na jima."
"Shi wajen da aka je ba’a d'aukar waya kenan?." Ya dan sosa kai yace, "ai kinga babu dadi ina wajan wata na d’auki wayar ki ko?." Da sauri ta kalle shi sai taga baiyi dariya ba alamun da gaske yake yi ba zolayar da ya saba bace yace, "Shiyasa bana d'auka in na dawo nace zan miki bayani. Kin san dai kece k’awar shawara ta ko? To wata na gani ina sonta shiyasa naje gidan su daga wajan aiki."
Kallon sa kawai yaga tana yi amma bata ce komai ba kana ganin kallon kasan bana Lafiya bane yace, "ta karb’e ni hannu biyu sosai amma ta sanar dani iyayen ta basa son bikin ta ya d’auki lokaci, ni gashi ban wani shirya sosai ba ya kike gani za’a yi?.” Shiru nan ma bata ce masa komai ba sai ta tashi daga inda yake ta shiga d'aki yayi dariya mai sauti yana jin dadin tsokanar ta har zuciyar sa. İn yana tsokanar ta nishad’i yake yi sosai shiyasa baya rabo da zolayar ta. Da kansa ya kwashe kayan ya kai kitchen ya kashe hasken falon ya d'auki Amir ya kai shi d’akin ya kwantar dashi ya shiga wanka sai da ya gama shiryawa sannan ya shiga inda take.
A kwance ya ganta a kan gado ta juya baya ya kunna hasken d’akin ya k’arasa Inda take kwancen ya tashe ta zaune yaga tana kuka, yace, "Subahanallahi wai kuka kike? Haba Habibty kin San wasa nake miki fa meye na dawowa d’aki kina kika bayan kin san ba ke kadai bace ba?." Hawayen ya share mata yana murmushi yace, "Kiyi hak’uri na d'auka zaki tunanin wasan nake yi shiyasa na tsokane ki amma wallahi wasa nake yi, ki daina kuka dan Allah. Da nasan zakiyi kuka ai da ban yi ba.”
Ta kalle shi yace, "in wasa ne meyasa baka d'aukar wayata? Bayan kasan dare yayi baka tab’a kaiwa haka a waje ba kasan dole na damu, meyasa baka ni ka fad’a min ba? Indai da gaske ba inda kaje din ba kenan meya hana ka sanar dani?." Ya zauna a kusa da ita sosai yace, "Allah wasa nake miki nace a wallahi ya kamata ki yarda."
"To ina kaje? Me ya hana ka d'aukar wayata?." Yayi dariya kad'an yace, "Ina Wanda na bawa kudina ana juya mana?.” Ta kalle shi ya d’aga kai yace, "To an siyar da kayan riba ta samu Habibty fiye da tunanin ki. An samu albarka sosai Allah ya sakawa kasuwacin nan albarka. Wajan sa naje akayi lissafi aka bani ribar, kin San abin da yawa shiyasa na jima sosai, kuma muna zaune a wajan shiyasa ban d’auki wayar ki ba."
"Amma da ka fito meyasa baka kira ni ba?."
"Na karb’i laifin ayi hak’uri bazan sake ba." Ta kalle shi tace, "Meyasa ka tsokane ni?." Yayi dariya yaja hancin ta yace, "ina so naga kina nuna kishin ki a kaina, ina jin dad’in tsokanar ki Allah ya sani.”
“Saboda me kake son tsokanata?.”
“Sboda yana bani nishad’i.”
Rukayya tayi murmushi tace, "wata ran wannan kalaman naka zasu iya zama na gaske."
"Kinga mu bar zancen nan, muyi maganar wannan alkhairin da muka samu. Ribar da yawa ya kike ganin zamu yi da ita?. Daman kin san akwai kudina na gidana na farko da aka siyar canjin aka fara juyawa ga wanda nake tarawa na albashi ga kuma na gidan da muka baro kinga shi yafi yawa ma, shiyasa aka samu riba Alhamdulillah."
Rukayya ta gyara zama tace, "to yanzu ya akayi kenan?."
"Me kike ganin za'a yi da kudin?."
"A sake juya su mana, ka k’ara a kan jarin naka a sake juyawa su ninka abinda aka samu."
"Uhuummm nayi wannan tunanin amma sai na fasa na dai rage wani abu a ciki a k’ara ragowar suna wajena, ki fad’i abinda za'ayi dasu me kike so?."
"Me kake ganin za'a yi dasu?."
"Alhaji da Hajiya nake so na yiwa bazata wacve zasu yi farin cikin sosai, dalilin farin cikin nasu ya haifar min da wani cigaban a rayuwa ta, to na rasa me zan musu wallahi.”
Rukayya tayi dariya tace, "Shawara." Yace, "ina ji."
"Ka kai su umrah indai kud’in zai isa, ina tunanin duk abinda zaka yi musu bazai kai wannan farin ciki ba." Murmushi yayi yana kallon ta cikin jin dadin abinda tace, "Ban mu tafa dan Allah." Dariya tayi ta bashi hannu suka tafa ya rike hannun yace, "Gaskiya shawarar nan taki tayi sosai ba kad’an ba, tabbas zasu yi farin ciki musamman Hajiya ace yau ga a saudia ai sai ta suma saboda murna." Rukayya tace, "ai kowa ma sai yayi murna koda ya tab'a zuwa balle basu tab’a zuwa ba.”
Ibrahim yace, "kinga dai ni yanzu ban san nawa ne kud’in zuwa ba bana tunanin kuma kud’in zai iya na kai su su biyun sai dai mutum d'aya." Rukayya tace, "to wa zaka kai?."
"Zab'i naji a cikin su wa za'a kai?."
"A’a bani da zab’i a cikin su duk wanda ka kai daidai ne." Yayi dariya yace, "to ko a kyale su muje nida ke nan gaba sai su je?."
"A'a wallahi, su ya kamata ka fara kaiwa sannan mu biyo baya, zuwan da zasu yi farin ciki da addu'ar da zasu yi maka wallahi sai kafa kafin su dawo Allah ya hore wanda zamu je nida Kai din." Kai ya girgiza cikin gamsuwa yace, "haka ne, Ina ma Allah ya hore muje ni da ke da hajiya da Alhaji duk a rana d’aya." Rukayya tace, "yanzun ma baka san me Allah zaiyi ba."
"Haka ne. Yanzu gobe bazan fita ba tunda Amir babu makaranta zaki raka ni muje mu tambayi kud’in da za'a kashewa mutum d'aya in zai isa suje su biyu in bazai isa ba sai ki zab’i wa za'a kai."
Tayi dariya tace, "nifa babu wanda zan zab’a a cikin su kowa a kai daidai ne." Ya dungure mata Kai yace, "Allah ke zaki zab’a bara dai muje mu ji." Ta kwantar da kanta a kafadar sa tace, "ashe baza'a zab'a ba.” Cikin ta ya shafa yace, "baki fad'a min ya akayi a asibitin ba."
"Ban je ba wallahi, Ameena da Zakiyya ne suka zo muka zauna Muna ta hira."
"Amma ya kamata kije." Tayi shiru kafin tace, " zan je . Su Ameena suna gaishe ka, sun so ka dawo ku gaisa ma baka dawo ba."
Yace, "ina amsawa" abinda yace kenan yayi shiru itama haka zuciyar ta ta tafi tunanin Fiddausi shi kuma yayi shirun ne dan kar ta sake cewa wani abun tayi masa zancen Fiddausi. Wayar sa ake kira ya d'auka ganin lambar da bai sani ba ya saka shi saka wayar a speaker yace, "hello."
Daga can b'angaren akace, "Hello kana jina? Hello kana jin abinda nake cewa?." Ya kalli Rukayya da take kallon sa yace, "ina ji,wacece?."
"Nice Naja'atu daga nan Abuja, Mun tare da tsoh......!" Dufff sai wayar ta d'auke ya kalli Rukayya yace, "Naja'atu, daga ina kuma?." Rukayya tace, "ka kira kaji naji kamar hankali tashe ake maganar." Ya ajjiye wayar yace, "ban Santa ba bazan kira ba watakila ma kuskuren lamba akayi." Rukayya tace, "maybe." Ta fad'a tana kulle idon ta dan bacci take ji sosai.
Daga b'angaren su Fiddausi Naja'atu tana fara magana a wayar suka ji motsi sai suka kashe da gaggawa suka zauna amma kana kallon su kasan basu da gaskiya ko kad'an. Alhajin ne ya shigo yana bin su da kallo d’aya bayan d’aya yace, "wannan zaman meeting din da ake yi akai-akai fa ban amince dashi ba, in ma wani shiri kuke shiryawa gwara ma ku daina babu abinda zai fitar daku daga gidan nan sai in ni naso."
Ya kalli Fiddausi ya kalli wanda yake kusa dashi yace, "ga amaryar can in tayi maka a akai maka ita d’aki dan tana da gardama sosai." Ya kalli Fiddausi yace, "tayi, ni ai baza tayi min gardama ba saboda ba harkar ku nake ba ni ba irin ku bane ba, kai kasan gaba zan bi ba baya ba." Yayi murmushi yana kallon ta yace, "y’an mata muje ko? In akwai abinda kike so ki fad’a min sai a baki."
Alhaji ya kalli Fiddausi yace, "tashi kuje, ba abinda kike tsoro zaiyi dake ba Malama." Girgiza kai take yi alamun bazata ba ya kalli Alhajin yace, "ka gani na fad'a maka daman taurin kai ne da ita, ina zuwa" ya fad'a yana juyawa ya fita shi kuma yazo wajan Fiddausi da niyar tab'a ta sai tayi baya ta tankad'a shi da karfin ta da ya rage mata. Aliya ta d’auki plate din da yake kusa ta buga masa a kansa Naja'atu zaro drawer da take jikin bedside drawer ya maka masa da karfin gaske.
Da sauri yayi hanyar waje ko waigen su bayayi Naja'atu ta kalle su tace, "mun daina bari ana mana abinda ake so daga yanzu wallahi, koda Alhajin ne abinda zamu yi masa kenani in ta kama mu kashe shi wallahi kashe shi zamuyi. Mu koma zama waje d’aya hatta kwana mu dawo yi a d’aki d’aya daga lokacin zai fara shakkar mu. An daina cutar wata a cikin mu mu kasa komai sai dai muyi kuka mu share hawaye, wannan lokacin ya wuce wallahi.”