Sashe 83
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kyale shi tayi ta cigaba da abinda take yi kafin ta kwanta itama. Bai farka ba sai karfe tara na safe yana bud’e ido ya ganta a tsaye da kayan jiya a jikin ta tana mayarwa da Zaytun su da alama har tayi wanka ma. Ya tashi zaune yana sake dafe kansa ta kalle shi tace, “ka tashi safiya tayi sosai akwai sallah a kanka” tana fad’a ta fita ita da Zaytun sai kuwa ya tashi ya shiga band’akin ya fito ya tayar da sallar asuba yayi ya sake yin sallar walha a lokacin ya shigo ta d’auki mayafi suka had’a ido sai tace, “ina kwana.”
“Kin tashi lafiya?.”
“Lafiya lau, ya jikin?.”
“Alhamdulillah. Na gode Allah yayi albarka.” Tayi murmushi jin abinda yace sai tace, “Amin.
Ta nuna masa key tace, “na ari motar ka zanje gida na dawo.” Ya kalle ta kafin yayi magana tace, “Ammah ta aiko da abinci yana k’asa in zaka ci.”
“Su Yaya Adam din basu tafi ba?.”
“Sun tafi, zanje gida na d’auko kaya ne ga uniform din Zaytun yau ko school bata je ba.”
Ya tashi tsaye yace, “to ki jira ni nayi wanka sai muje.” Ya kalle shi tace, “yanzu zan dawo, ba lafiya ce dakai ba ka zauna.”
“Bazan iya zaman bakya nan ba, ina zuwa” ya fad’a yana fita daga d’akin tace, “sabon salo, wai bazai iya zama bana nan ba. Ayi dai mu gani.” Tana nan zaune sai gashi ya dawo ya canja kaya zuwa jallabiya blue yace, “muje.” Tashi tayi suka sakko ya shiga mazaunan direba ya shiga gaba ita da Zaytun suka fita daga gidan.
Gani tayi yana yawo akan titin kamar dan koyo alamun akwai abinda yake damun sa tace, “ka tsaya.” Sai kuwa ya tsaya ta fito daga gaba ta zagayo ta bud’e tace, “ni nasan baza ka iya ba, ka koma gaba.” Sai da ya rik’o hannun ta sannan ya fito ya koma inda ta bari ya zauna ta shiga taja motar zuwa gidan su. Mai gadi yana nan dan daman baya barın gidan babu kowa suka gaisa ta shiga ta bud’e gidan yana zaune a motar sai gata da jaka babba ta fito mai gadin yazo ya karb’a ya saka mata a boot ta sake komawa ta sake fitowa da wasu ya sake karb’a ya saka mata a motar. Kulle boot din tayi ta shiga ta sake jan motar suka koma gidan.
A falon suka zauna ta zata d’auki kayan ya hana ta kale shi tace, “ina da lecture ne ina sauri zan tafi.” Ya kalle ta jin abinda tace sai yace, “to, amma ki bari yanzu Mubakar zai zo sai ya hau miki da kayan sama.”
“Har sai na jira Mubarak? nace sauri nake”ta fad’a tana fara jan kayan sai ya tashi yace, “kawo na d’aukar miki” kafin tayi magana ya d’auki duka biyun yana hawa saman dasu tabi bayan sa Zaytun ma tana biyo duk duk inda suka bi ya shiga dasu har d’akin tace, “Sannu.” Abinda tace kenan ta k’arasa ta bud’e kayan ta d’auki kayan da zata saka ta d’auko na Zaytun ma ta fara saka mata yace, “Yanzu makarantar zaki tafi?.”
“Eh.” Yayi shiru baiyi magana ba ya fita ta shirya ta fito da jaka ta same shi a falon a zaune tace, “sai na dawo.” Sai ya tashi yace, “muje na kai ki.”
“Haba dai, kayi zaman ka zanje, yanzu da muka fita ma baka iya driving din ba.” Yayi shiru tana kallon sa kana ganin sa kasan bashi da lafiya karfin Hali kawai yake yi tace, “ka zauna ba jimawa zanyi ba” ta kalli Zaytun da take kusa dashi bata ce komai ba ta sauka ya bita da kallo ya lumshe idanun sa farin ciki da damuwa sun masa yawa a zuciyar sa har ya kasa sarrafa su.
Tun daga farkon estate din aka jin wari mai sanya amai gabad’aya wari ya addabi mutanen da suke zaune a wajan duk sun bar gidajen su dan wari ya game ko ina har cikin d’akin ki. Jami’an lafiya aka kirawo suka yi searching ko ina aka tabbatar warin daga gidan Alhaji Bello yake fitowa suna nufar gidan warin yana sake yin yawa.
Babu kowa a gidan ko mai gadi babu kamar kango gidan haka suka dinga shiga ana dubawa har suka zo k’ofar falon da aka kulle Alhaji Bello a ciki. Dukan k’ofar sukayi da k’afa duk sai da suka ja baya saboda duk da sun kulle hancin su amma warin da ya danno kai sai da suka ji shi har cikin bakin su cikin su ya juya a take wasu suka fara jin zawo saboda warin da yake fitowa bana wasa bane.
Alhaji Bello suka hango tsirara dashi a kwance ya zama tamkar skeleton naman jikin sa har ya fara zagwanyewa k’uda da kiyashi kamar saukar dasu akayi a wajan. D’aya daga cikin ma’aikatan yace, “wannan ya kwana biyu da mutuwa a wajan nan.” D’ayan yace, “gashi babu kowa a gidsn duk girman sa, waye wannan din?.”
A nan suka tattaro Alhaji Bello aka saka kwantar a harabar gidan aka nemo malami aka yayyafa masa ruwa dan bazai yu ayi masa wanka ba saboda ya gama lalacewa aka suka nannd’e shi a farin yanki aka d’auke shi aka je aka binne. An saka maganar a social media saboda y’an uwan sa su sani nan da nan magana ta baza duniya Alhaji Bello ya mutu ga kuma irin mutuwar da yayi.
Daya daga cikin abokan harkar Alhaji Bello yana duba waya yaga abinda yake faruwa gaban sa sai ya fad’i sosai ya kalli Nabila sa take kusa dashi yace, “kinga abinda na gani, kalli Alhaji Bello fuskar sa dan Allah” ya fad’a yana nuna mata wayar gaban ta ya fad’i itama tace, “wannan shine? Kalli yadda kuda suke bin abinda da aka rufe shi ba.”
“Ki karanta maganar; kwanan sa biyu da mutuwa an rass kowa nasa, damun mutanen unguwar yayi da wari suka je suka fito dashi aka samu ya mutu bayan haukan da yayi na kwana biyu aka yayyafa mai ruwa aka binne saboda ko da an kai shi wajan ajjiye gawa baza ta zaunu ba, saboda tun farko ya riga ya fara wari.
Nabila ta girgiza kai tace, “Allah Sarki. Shi ya riga ya mutu muyi magana akan abinda yake gabana. Ka bani kud’i na tafi Germany naje ayi min aikin nan. Komai nawa ya k’are Akan wannan lalurar da ku ne kuka samar min da ita, zama bana iya yi yanzu sosai kai ma ka sani.” Ya kalle ta yace, “babu abinda zan baki wallahi, domin kuwa ke ba mutuniyar da za’a taimakawa bace ba. Waye bai San ki da Alhaji Bello ba? tunda komai ya fara lalace masa kika gudu bama Kya yin maganar sa. Yanzu da yayi irin wannan mutuwar ko a jikin ki wai Allah Sarki shine abinda zaki ce a matsayin ki na budurwar sa. kinga Nabila bani na saka ki neman ko wanne namiji ba, a can kika kwaso ciwon da kika kwaso dan haka babu ruwana ko tashi ki bani waje ni.”
“Kasan Adadin abinda yake damuna kuwa? Ance in ba’a yi min aiki ba zan iya rud’ewa k’arshe kuma mutuwa ce.”
“Ki mutu mana shima gashi ai ya mutu lokacin sane yayi.”
“Ka taimaka min kaf kudina ya k’are akan wannan ciwon wallahi, dan Allah ka taimaka min ka bani ciwon nan yana damuna sai na saka wani abun na tare saboda ruwa ne yake fita daga jikina gaba da baya.”
“In ma jini ne ina ruwa na? Kinga ki tashi ki fita babu ni babu ke wallahi kije can ki k’arata amma kar ki sake zuwa inda nake.” Nabila tace, “yanzu baza ka taimaka min ba? In baka taimaka min ba waye zai taimaka min?.” Ya harare ta yace, “kije gawar Bello ta taimaka miki amma bani ba walalhi, in baki fita ba sai na yi ball dake a wajan nan. Ki barni naji da aabinda ya samu Bello mana, hauka ya dinga yi a gidan sa babu Wanda yake kula dashi kowa ya gudu babu y’an uwa balle mata, yanzu yayi irin wannan mutuwar amma ke bai dame ki ba saboda kudi kawai kika sani, ni ya dame ni saboda abinda Alhaji Bello yake shi nake yi.”
A haka ta fito jiki a salub’e shine mutumi na biyar kenan da taje wajan sa ko zasu taimaka mata amma bata taimakawa yanzu bata san ya zatayi ba kuma ciwon yana gab da cin karfin ta dan yanzu ruwa take fitarwa daga ko wacce kafa ta jikin ta.
Kwana biyu Kenan da tarewar Ameena babu wani canjawa harkar ta take bata shiga sabgar sa shi kuma har lokacin shayin ta yake yi baya iya mata magana mai tsaho gashi babu lafiya kirki gashi nan dai kawai. Da daddare ranar alhamis tana zaune a falo tana karatu dan tana da text juma’a. Zaytun bata nan tana gidan Ammah shi kuma ya hau sama bai sakko ba tun bayan da hau saman.
Gama karatun tayi ta tashi zata hau saman zata sai ga Mubakar ya shigo da Zaytun ta kalle shi tace, “har ina murna a can zata kwana.” Mubakar yace, “ta saka Rigima a kawo ta.” Tayi murmushi tace, “lallai Zaitun kin kyauta.” Mubakar yayi dariya yayi mata sallama ya fita ita kuma ta rik’e ta suka hau sama. Tana hawa saman a d’aki ta kwantar da Zaytun dan ta fara jin bacci tana cire kayan ta kafin ta gama Zaytun tayi bacci ta gama saka kayan ta kalli Zaytun din taga tayi bacci sai kuma ta kalli k’ofa taga bai shigo ba sai zuciyar take fad’a mata ko bashi da lafiya.