Sashe 70
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Book3
036
Yusuf ya samu sauk’i babu laifi sai yawon gidajen yayyen Ameena yake yana basu hak'uri har Zakiyya da Fiddausi bai kyale ba duk sai da yaje ya same su amma babu nasara har ya fara sarrewa da lamarin. Ameena kuwa duk wanda ya samu zai zo yayi mata maganar duk bata sauraron su dan bata so ma maganar tayi tasiri a zuciyar ta shirin biki take yi ita da sabon angon ta Al'ameen. Yusuf gab yake da fita daga hankalin sa saboda yadda ya koma kamar ba shi ba musamman a kamannin sa ya rame lokaci d’aya.
A falon Ammah Humaira ce a zaune ta saka Ammah a gaba tana kuka tace, "Ammah yanzu baza ki saka baki akan Ameena ta dawo gidan Yaya Yusuf ba? Ya kusa haukacewa ku taimaka masa dan Allah bazai sake aikata abinda yayi ba." Ammah ta kalle ta tace, "a goshin ki ya rubuta miki bazai daina ba? Ke yanzu a cikin zuciyar ki kina ji kin yarda Yusuf ya daina abinda yayi a da?."
"Wallahi Ammah na yarda ya daina, dan Allah dan Annabi ki amince ki saka baki Amesna ta dawo gidan sa wallahi yana sonta yana kuma qaunar ta."
Ammah tayi murmushi tace, "bara nayi miki misali, d'auki kanki a matsayin Ameena ace mijin ki yan dukan ki, yana zagin ki, yace miki b’arauniya, ya wulakanta ki saboda amarya, ya daukaki amarya akan ki, k'arshe ya saka miki ciwon da kike shan magana, ya kaurace miki daga shinfidar aure har hakan ya kai ga kina Shan magani. Sai kuma ya rabu dake ya zauna da amaryar ya sha wahala ya fahimci mahimmacin ki daga baya sai ya lallab’o yace zai dawo dake ya daina wallahi bazai sake ba, yayi alqawarin bazai kuma ba bayan kafin ya aure ki yayi alqawari zai rik’e ki har mahaifin ki ya yiwa alqawari yana gab da barin duniya. Zaki amince ki koma masa?."
Humaira ta bud'e baki zatayi magana Ammah tace, "kar kiyi son kai ki fad’i tsakanin ki da Allah, zaki koma ko baza ki koma ba?." Humaira tace, "indai ya shiru da gaske ya daina wallahi zan koma Ammah."
"To ya ya zaki san ya shiru?."
"In n koma din."
"In kika koma kuma duk karya yake bai daina din ba fa?." Humaira tayi shiru bata ce komai ba Ammah tace, "dan yana jinin ki kiyi adalci, in akwai wacce take so Ameena ta dawo wajan Yusuf a bayana take amma bana so ta dawo din dan halin da ta bari yana nan shi zata sake samu."
Humaira taja numfashi ta sauke tace, "Dan Alalh Ammah ayi wani abun wallahi yana sonta." Ammah tace, "son banza da wofi, son da bai amfana masa da komai ba meye amfanin sa?. Shi da yaci amanar so, wanne irin so ne Ameena bata nuna masa ba amma yayi burus ya watsar da ita saboda ya auro b’arauniya mai suffar aljanu?." Humaira ta goge idanun tace, "ko me ya faru shine ya jawo amma kuma akwai asiri a lamarin sa."
"Uwar asiri da uban sa, asiri yana tarar da hali tun kafin asiri daman da halin sa Humairah. Kiyi adalci ki daina fad'ar son zuciyar ki saboda Yusuf ya kasance naki. Itama jinin wani ce yadda kike kare naki yanzu suma ita zasu kare.”
Ta sauke ajiyar zuciya a lokacin ya shigo falon Ammah ta kalle shi yana bata tausayi itama sosai ya rame matuk'a sai haske da ya sake yi sosai, fuskar sa duk ta tari da gashi wanda bai sa shi ba in ya ganshi sai ya d'auka mahaukaci ne. "Sannu Ammah" ya fad'a yana wucewa ya shiga d'aki Humaira ta kalli Ammah tace, "Ammah dan Allah." Ammah tayi tsaki tace, "zancen kike so." Humaira tayi shiru tana nan zaune ya sake zuwa ya fita bayan ya canja kayan jikin sa.
Kai tsaye Yusuf gidan Adam ya wuce ya tsaya a k'ofar gidan daga can gefe yana zaune a mota ba tare da ya fito ba. Yaya Adam da dawo ya ganshi a wajan bai ma nuna ya ganshi ba ya shiga gidan ya samu Ameena tana aiki a falon ya kalle ta yace, "wai Yusuf din nan haukacewa yayi ne? Kullum sai yazo k'ofar gidan nan ya zauna tun safe har dare? Me yake yi a nan?."
Aysha tace, "to tunda ba shigowa yake ba ka kyale shi kayi kamar baka ganshi ba mana, ka cika mita." Ya yi k’wafa ya shiga ciki Aysha ta kalli Ameena da take mopping tace, "duk saboda Ameena yake zuwa kai ma ka sani amma ka dinga yin abu kamar baka sani ba. Kuma tunda ba shigowa yake ba meye na maganar?.” Fita Yaya Adam yayi sai ya samu sai motar amma baya nan ya girgiza kai yace, "Ko Ina yaje ai zai dawo ya same ni."
Yusuf kuwa Adam yana shiga gida ba jimawa sai ga Al'ameen ma ya dawo zai shiga gidan sa da ake ta aikin sa yayi kyau sosai sai ya fito daga motar ya k'araso inda yake Al'ameen ganin ya tsaya sai ya sauke glass din motar yana kallon sa dan kamar bai gane shi ba sai Yusuf yayi murmushi yace, "Yusuf." Sai Al'ameen yayi murmushi yace, "sai kace min mahaifin Zaytun sarkin magana. Ban gane ka ba naga ka canja kamar ba kai ba.” Sai shima yayi murmushi Yusuf yace, "in babu damuwa ina so zanyi magana da kai."
Al'ameen yace, "mu shiga ciki to." Al'ameen ya shiga da motar shi kuna ya shiga da k'afa Al'ameen ya faka motar ya shiga ya kalli Yusuf yace, "bismillah muje ciki." Suka shiga falon da yake kaca-kaca babu gyara saboda aikin da ake yi a gidan ya kalli Yusuf yace, "sai hak'uri, gidan ana ta aiki shiyasa gashi nan dai.”
Yusuf yace, "babu komai hakan ma na gode." Al'ameen yace, "zauna." Suka zauna akan kujerun da aka rufe su da leda saboda kar su b'aci da fenti Yusuf yace, "nasan kana ta mamakin ganina."
"To ba abin mamaki bane tunda nasan zuwan yana da nasaba da Ameena ko?." Ya d'aga kai alamun eh kafin tace, "to ina jin ka. " Yusuf yace, "hakurin dai nazo bayarwa naga kaima tamkar Yayan ta kake. na san nayi kuskure abubuwan da aka aikata a baya amma a yanzu na canja duk abindaa aka san ni dashi a baya na daina meyasa baza'a sake bani dama a karo na biyu ba?, Muna yiwa Alllah laifi ya yafe mana meyasa baza'a yafe min a bani dama ba ko dan saboda y’arda take tsksanina da Ameena?."
Al'ameen ya sauke numfashi yace, "to Yusuf shi kuskure ana aikata shi ne a lokacin da ba'a yi tunani ba musamman ina anatunanin abinda aka aikata kuskuren a kai bazai kubce ba, a lokacin da ya kubce kuma ana so a dawo dashi a goge wancan kuskuren mutum ya kan iya ko wanne basaja dan ganin ya goge wancan kuskuren an bashi wata damar. Wannan marairaicewar da kake yi watakila plan kake shiryawa kana so Ameena ta dawo sannan ka koma halayen da ka bari."
Yusuf girgiza kai yake yi yace, "Ko kusa, ko kad’an wallahi. Da gaske na canja ba basaja nake ba Allah yana ganin zuciyata, meye riba ta in aka sake bani Ameena na wulakanta ta?, Me zan samu in na tozarta Ameena?, Me zan cimma in nayi akrya da Allah akan na canja kuma kawai dan cikar burina?. In ka yiwa abu rik’o mara kyau ya kubce maka a lokacin da yake gab da fad’uwa ka fahimci hakan kayi saurin rike shi ka dawo dashi hannun ka na tabbatar ba zaka sake yiwa abun nan irin wannan rokon ba. Ka taimake ni ban san ka ba amma ina ganin ka da Yayan ta sai na tabbatar kana da mahimmaci a wajan sa da ita kanta, ka amince min a sake bani dama na zauna da Ameena, in na sake maimaita abinda nayi a baya na amince bayan an raba mu ayi min duk abinda ake ganin za'a wuce, amma dan Allah kar ace min zata auri wani daban bani ba, bazan iya jurewa ba."
Al'ameen yayi shiru yana sauraren sa yana girgiza kansa kafin yace, "ni ban San abinda zanyi maka ba da ka same ni da wannan maganar, Adam dai shi ya kamata ka komawa bani ba."
"Na kasa na kasa sake komawa, ka taimaka ka shige min gaba wajan gyara abinda na b’ata. Baza ka so ace yau Zaytun ta tashi ba'a tsakanin iyayen ta ba, baza kace ace ta tashi a wani waje daban ba, baza kaso ace Ameena da yarintar ta ace tana raba yara a gidajen maza biyu ba" Yusuf ya zamo daga kan kujerar Al'ameen yace, "ka koma ka zauna dan Allah kar kace zaka durk’usa min." Yusuf bai fasa ba yace, "dan ka amince da gaske nake ba wasa ba, ina son a sake bani Ameena dan Allah."
Al'ameen yace, "naji tashi ka koma ka zauna." Yusuf ya koma ya zauna Al'ameen yace, "kar ka damu zan same shi da maganar, amma kamar baka gane ni ba a ranar da kaje wajan Adam har kuka yi magana da Ameena, baka gane fuskat ba ko?." Yusuf kamar yayi kuka yace, "bana fahimtar komai a lokacin, bana gane komai bana ganin komai indai ba ita da Yaya Adam din ba." Yayi murmushi yace, "shikenan kar ka damu za'a san abinda zanyi a kan maganar, in rabon kace zaka sake samun ta, in ba rabon ka bace duk yadda da kaso ga sake samun ta zata zama mallakin kana karo na biyu ba. Kaje kai ta addu’a a kan hakan shine maganin damuwar ka.”