Sashe 62
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari da safe Abbah ya fito yana karyawa shida Ammah da Mubakar ya kalli Ammah yace, “banga Yusuf ko a sallar asuba ba, ya fito kuwa?.”
“Anya kuwa ya fito? Mubakar jeka wajan sa ka gani.” Mubakar ya tashi ya shiga ya same shi a zaune da alama bai jima da tashi ba dan a lokacin ya idar da sallah yace, “Sannu, ya jikin?.” Kawai kawai ya girgiza masa yace, “kazo in ji Ammah tana zaune.” Yana fad’a ya fita shi kika ya tashi fito ya same su a zaune.
A kan carpet ya zauna dan yafi jin dad’in hakan Ammah tace, “ga abinci nan zo kaci.” Y kalle ta yace, “Abbah barka da safiya, Ammah barka da safiya.” Suka amsa Abbah yace, “ya jikin naka?.”
“Da sauki” ya fad’a a takaice yana kulle ido ya bud’e.
“Likita yace a dinga baka abinci kana ci dan haka ka taso kazo maci abinci ka sha maganin ka” Ammah ta fad’a tana kallon sa. Yace, “Bana jin yunwa ne ko kad’an.”
“Zaka ji, tashi ka zuba kaci.”Mik’ewa yayi ya zuba tea kawai ya koma ya zauna yana sha a hankali yana kallon wani wajan daban. Usman ne ya shigo bayan sa Abie ne da Yaya suka k’araso suka gaida Abbah ya amsa Usman ya kalle shi yace, “Yusuf ya jikin?.”
Kai ya d’aga kawai kafin yace, “Allah ya kara Lafiya.” Ya amsa da amin kafin yayi shiru baice komai ba kowa ma kuma babu Wanda yace wani abun. Kallon Usman yayi yace, “muje ka raka ni wani waje.” Ya fad’a yana ajjiye tea din Ammah tace, “ina zaka je kai da baka da lafiya?.” Ya kalli Ammah yace, “Yanzu zan dawo.” Bata sake magana ba ya fita harabar gidan ya kalli Usman yace, “wa kake ganin zan sake samu akan maganar nan? Wa kake ganin zai iya rarrashin ta ta dawo koda bata sona ita da Yayan ta?.”
Usman yace, “Yusuf ya kamata ka cire Ameena daga ranka daga yanzu, baka ji me akace maka ta kusa aure bane ba?.”
“Ko yau ne d’aurin auren ta bazan hak’ura ba sai naga ta zama mallakin wani Usman, sannan babu wanda zai mallaki Ameena sai ni bayan ni babu wani a duniya.” Usman ya girgiza kai yace, “to naji, ni ban san wani waje ba kaje kayi jinyar kanka ni kuma na wu wajan aikin.”
“Usman ka yarda dani in ban samu Ameena ba mutuwa zanyi, ka daure ka amince min ka shige min gaba wajan sake samun Ameena.”
Usman yace, “Dani aka je wajan Adam, Dani yake yiwa fad’a yana cewa muka sake zuwa sai ya b’alla ka. Yusuf zan iya komai dan samar maka da farin ciki amma ina so ka sani kayi kuskuren da sai kabi a hankali zaka samu Ameena, wannan gaggawar da kake yi babu abinda zata haifar maka dashi sai dana sani.”
“İn banyi gaggawa ba me zanyi Usman? Ya kake so nayi ina zan saka raina?.”
“Hak’uri zakayi ka cigaba da addu’a Alalh zai kawo maka mafita.”
“Ina yi Usman.”
“To ka samu Ammah da maganar.”
Da sauri ya kalle shi shima shi yake kallo yace, “eh ka fad’a mata, saka sha fad’a amma zata taya ka addu’a in Ameena rabon kace Allah ya sake had’a zaman auren ku.” Ya girgiza kai yace, “da wanne Idon zan iya kallon Ammah na fad’a mata wannan maganar dan Allah?.”
“Da Idon sa ka kalli Adam mana, dashi zaka je wajan Ammah.” Ya sauke numfashi yace, “zo muje yanzu.” Usman yace, “A’a babu ruwana kaje kai kad’ai, ni zan wuce akwai bak’in da suke son fara kawo kaya suna son ganina Yanzun nan” ya fad’a yana barin sa ya shiga mota ya fita daga cikin gidan.
Yusuf ya shiga falon ya samu suna tattaunawa harda dariya ya k’araso ya zauna a kusa da Ammah yana kallon tea din da ya ajjiye zuciyar sai bugawa take yii kamar lofin ne Ameena. Ya sauke numfashi mai nauyi ya runtse ido ya bud’e ya kalli Ammah da yake kallon sa kamar zai magana sai ya fasa yaja bakin sa yayi shiru.
Juyowa yayi ya kalli Ammah yace, “Ammah!.” Sai kuma yayi shiru ta kalli Abbah da yake kallon sa ta kalli Yusuf din tace, “Na’am.” Ya kalli Abbah yace, “Dan Allah ku yafe min adadin b’ata muku ran da nayi a kwanakin baya, Nidai nasan ni Yusuf ne amma wani abun ina yin sa kamar ba ni. Wani lokacin ina cikin nutsuwata wani lokacin bana ciki dan Allah kiyi hak’uri ku yafe min.” Abbah ya kalle shi yace, “ai babu abinda kayi mana in ma akwai min yafe.” Ammah ta girgiza ki tace, “mun yafe kam.”
Yusuf ya sauke numfashi yace, “Ina son na dawo da Ameena.” Ammah ta kalle shi tace, “me kace?.” Ya dago kai yace, “Ina son dawo da Ameena gidsn Amma, nasan nayi kuskuren da babu lallai ta yafe min amma ina so ki shige min gaba dan wallahi in ban same ta ba zan iya rasa raina.” Ammah ta girgiza kai tace, “Ahh lallai Yusuf akwai abinda ya tab’a maka kwakwalwar ka, da ace baka daina shan giya ba da nace giyar ce har yanzu bata sake ka ba. Ni zaka kalla ka cewa kana so ka dawo da Ameena? Yanzu kenan kana sonta?.”
“Wallahi Ammah soyayyar Ameena bata tab’a barin zuciyata ba, nasan wani abun ina sane amma wani abun sai anyi nake dana sani Ammah.”
“Karya kake, ka manta cewa kayi nice nace kaje ka auro Ameen Yusuf? Ka manta cewa kayi ba son ta kake ba alfarmar ta take ci kake zaune da ita?. Ka manta cewa akayi badan ni ba da yanzu ta jima da zama bazarawa?.”
Ya girgiza kai yace, “Ko a lokacin karya nake wallahi, na fad’a ne saboda dalili na amma wallahi k’arya nake yi Ammah ina son Ameena har yau har gobe har jibi har na mutu.”
“Yi min shiru kafin na buge maka bakin ka, ni zaka cewa kana sonta har gobe? Ka manta abubuwan da kayi mata ne da zaka zo ka saka ni a gana da yake ka Raina ni?.”
Yace, “Ammah har zuciyata nake fad’a miki ina son dawo da Ameena ki amince dani.”
“Oh na gane abinda kake nufi, ka auri b’arauniya, kazama, mara tarbiyya, mahaukaciya yar gidan k’ananun mutane kaga baka samu abinda kake so a wajan ta ba shine yanzu ka dawo kake son dawo da Ameena ka cigaba da dukan ta yadda kake so ko? Dan Kaga waccan bata kyale ka in ka daka ramawa take shiyasa kake son sake d’auko Ameena domin ka cigaba da dukan banza ko?.” Ya girgiza kai yace, “A’a Ammah, ba haka bane ki fahimce ni. Wallahi bazan sake kuskuren ma dukan Ameena ba, na canja wallahi.”
“Har abada bazan fahimce ka b indai akan Ameena ne, duk soyayyar da nake nunawa yarinyar nan hakan bai hana ka wulakanta ta ba, ka ci zarafin ta ka lalata mata rayuwa ka d’ora mata ciwon da ko ni babar ka bani dashi. Ka dake ta, ka zage ta,kayı mata k’arya da sharri da k’age, ka daina sauraron ta har ta Kai ga tana sahan magani domin kare kanta daga fad’awa halaka, itace zaka zo kace min kana so na yarda?. Itace zaka ce zaka dawo da ita na shige maka nayi iso a wajan ta da yake bani da kamar kai ko?.”
Ya kulle ido nadasani ta gama dabaibaiye shi ji yake ina ma ana dawo da abinda ya wuce da ya dawo dashi ya goge rayuwar sa da Ameena da duk b’ata mata rai din d yayi. Ammah tace, “y akayi shiru? So nake kace min ai ba haka bane kai kana sonta Yusuf, har kana da bakin cewa zaka dawo da Ameena dan baka da kunya baka da mutunci baka San ma kawaici ba ko?.” Yusuf ya bud’e ido yace, “Tun kafin Asiya ke shaida ce Ammah ina sonta, har na aure ta ina sonta wallahi kawai kuskurena abinda na aikata mata nasan nayi kuskure shima kuma….” Abbah da yake gefe yace, “shima me Yusuf?.” Ya juya ya kalle shi Abbah yace, “Yusuf in y’ata ce Ameena ta gama auren ka har abada, dan haka itama ta gama auren ta dan kamar ni na haife ta haka nake ji, kar na sake jin maganar Ameena a bakin ka dan baka cancanci ambatar sunan ta ba, dan haka babu kai babu Ameena kar na sake ji ko ganin kaje gidan su akan wannan maganar.” Kamar zaiyi kuka yace, “Amma Abbah…” ya dakatar dashi yace, “Umarni na baka ai ba shawara ba, in matar ka kake son dawo da ita kaje ka samu Asiya ka dawo da ita amma ba Ameena ba Kaji na fad’a maka” ya fad’a yana tashi ya fita Ammah ma ta fita aka bar Yusuf a zaune a wajan cikin tunani da kuma tashin hankali.
Book3
033
Yusuf jiki a salub’e ya tashi ya bar falon Abbah yaja tsaki bayan ya bar wajan cikin takaicin saken da yayi ya rasa yarinya kamar Ameena Ammah tace, “ikon Allah, wai dan ma bashi da kunya Ameena yake so ya dawo da ita ya manta abubuwan da yayi mata a baya.” Abbah yace, “bai san abinda yake yi ba ai, in yasan abinda yake yi bazai yi gangancin aikata hakan bama.” Ammah ta sauke numfashi tace, “gaskiya dai kam bai san abinda yake yi ba. Ya manta abubuwan da suka faru a falon nan wanda aka zayyano mana ya aikata, amma yanzu dsn bashi da kunya yana so ya sake komawa.” ta fad’a a bayyane amma zuciyar ta tausayin sa take ji sosai ma kuwa.
Yusuf tunda ya koma d’aki ya kwanta yana juyi ya rasa me yake masa dad’i, rana zafi inuwa k’una haka komai ya zamar masa, zuciyar sa kamar dutse aka saka mata a sama da k’asan ta haka yake yin zafi da rad’ad’i a ciki. Tashi yayi ya fito yazo ya wuce su a falon ya fita daga gidan gabad’aya ya koma gidan sa ko zai ki kewar Ameenan ta neman yiwa zuciyar sa illa, ko wanne lokaci Ameena, ko wanne yanayi Ameena haka zuciyar sa take kasancewa a yanzu.