Sashe 78
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameena ganin ta sai tayi dariya tace, “mutanen Saudia.” Ta harare ta ta gaisa da Anty da Yaya suka shiga ciki sannan ta kalle ta tace, “yau kwana biyu da dawowa amma baki zo ba.” Ameena tace, “wallahi ina so nazo dan kina raina kawai ban samu na fito bane.” Rukayya ta zauna tace, “daman haka zaku ce ai, ya gidan?.”
“Normal wallahi, ya unborn?.” Rukayya ta tab’e baki Ameena tayi dariya tace, “munafuka.” Tayi dariya Rukayya tace, “ashe Fidy auren ya mutu, naji wallahi da aka raba auren cikin sanyi babu tashin hankali.”
Ameena tace, “bari kawai Ruky smart ai na taya Fidy murna, yanzu baki ga ta dawo hankalin ba tana idda abin ta da ta gama sai tayi aure dan tayi nadama na tabbata Allah zai zab’a mata miji na gari.” Rukayya ta sauke numfashi ta kalli Ameena tace, “naji batun Yusuf.” Ameena tayi y’ar dariya tace, “Ni nasan sai tayi miki zancen nan ai.”
“Ai ya kamata na sani. Ameena nidai da naje saudia nayi miki addu’a kamar yadda kika ce, wallahi har d’awafi nayi miki akan wannan lamarin nan. Nidai amma nafi son Yusuf saboda Zaytun da kuma Ammah.”
Ameena tace, “sai kuce saboda Zaytun meyasa saboda ita?, shin har yanzu bamu bar k’arnin komawa gidan tsohon mijin saboda yara ba?.”
“Yaci albarkar Zaytun da mahaifiyar sa mana. Kuma ana komawa gidan mijin da aka bari albakacin yara Ameena.”
“Hmmm Ruky kenan, baki san halin da na shiga bane, a gaban ki ya dinga min tsawa kawai dan wacce zai aure tayi min karya.” Rukayya tace, “wannan tsawa ko wacce mace ma mijin ta yana yi mata, wallahi fad’a da mukayi Khalil a saudia sai da nayi mamaki ya dinga zazzaga min masifa akan abu kad’an nace daman haka yake ban sani ba?, wannan ba komai bane kema kin sani. Zancen matar da zai aura kuma da yawan maza haka suke komawa in zasu yi aure balle ke da abin yazo harda asiri.”
Ameena tayi ajiyar zuciya ta kalle ta kafin tayi magana Rukayya tace, “Tunda har kin amince Fiddausi tayi nadama meyasa shi baza ki amince ba?.” Ameena tace, “saboda ita nadamar a bayyane take na tabbata baza ta sake gangancin da tayi ba.”
“To shima haka ai, laifin Fiddausi ai yafi nasa laifin kuma tunda kika ce tayi nadama ai shima yayi.”
Ameena tace, “ke yanzu da kike cewa na koma yayi nadama na yarda da hakan, amma kema zaki iya cewa Fiddausi ta dawo gidsn mijin ta tunda tayi nadama?.” Rukayya tace, “a guje kuwa Ameena, d’anta Amir fa ya manta da ita badan wannna zaman da yayi a wajan ta da bama nan ba, ina dawowa yana ganina a gidan Umma bai sake komawa wajan ta ba balle yace ya bini. Wallahi ko dan shi ya shak’u da babar sa ina so Ibrahim ya mayar da Fiddausi Ameena, har zuciyata nake fa miki wannan kuma so nake ya huta daga gajiyar tafiyar nan na isar masa da sak’on dan Allah ya mayar da ita.”
Ameena ta bita da kallon mamaki dan ita gatse tayi mata tace, “Wai da gaske kike? Mijin ki ne fa yanzu in ya dawo da ita kun zama ku biyu fa?.” Tayi murmushi tace, “kafin ni ai ita ya fara samu Ameena, da ita ya fara zama har suka haifi Amir sannan nazo, dan Fiddausi ta dawo babu komai daman can Mun saba aminai ne kowa yasan sirrin kowa ba wani tashin hankali zamuyi ba sai dai kowa da abinda yake ransa. Amma indai zai mayar da ita ina yi mata maraba, domin tayi nadamar da ya kamata a yafe mata.”
Ameena ta girgiza kai tana murmushi tace, “zuciyar ko mai kyau ce Ruky, ba ko wacce mace bace ce zata furta ma abinda kika furta ba yanzu koda wasa. Kema nayi mamaki saboda na san ki da kishi.” Rukayya tayi dariya tace, “tare muka taso fa dukkan mu, duk mun zama y’an uwa muna sows dan uwan mu abinda muke sowa kan mu.” Ameena ta girgiza kai kawai bata ce komai ba kafin Rukayya tace, “yanzu me kike gani akan batun Yusuf?.” Ta kalle ta tace, “kun cika naci.” Rukayya tayi dariya tace, “eh Mun ji.” Tayi dariya itama tace, “sai abinda Allah yayi.”
“To Allah yayi mana alkhairi.” Ta amsa da amin suna ta hira ta bata tsaraba har yamma sannan Ibrahim yazo ya d’auke ta suka tafi.
Ameena haka suka barta da tunani a zuciyar ta a haka ta wuni har dare. Da daddaren tana zaune a falo ana kallo Yaya Adam dai ba kallon yake ba waya yake ta dannawa amma yana kallon Ameena dan gani yake ba kallon ma take yi ba yace, “Ameenatuwa ya dai?.” Ta kalle shi tayi dariya kad’an tace, “babu komai Yaya.” Ya kyad’a kai ya cigaba da abinda yake yi. Ameena tayi shiru bata ce komai ba kafin ta tashi ta shiga d’aki a lokacin wayar ta ta fara k’ara ta duba taga sunan Yaya Al’ameen.
Ta d’auka ta saka a kunne tace, “Yaya barka da dare.” Yaya Al’Ameen yace, “barka dai Ameena, in kina gida ki fito yanzu ina kusa da motar ki ina so zamu yi magana dake.” Ta amsa ta kashe wayar ta fito da hijjabi Yaya Adam ya kalle ta alamun k’arin bayanı tace, “Yaya Al’Ameen ne yace yana son magana dani yana waje.” Baice komai ba ya cigaba da abinda yake yi ita kuma ta fita Zaytun ta bi bayan ta a guje.
Bata san tan bayan ta ba sai fad’uwar ta taji ta zame a tiles saka kuka ta juyo ta d’auke ta har bakin ta ya fashe saboda ta fad’i sosai tace, “Meyasa kika biyo ni?.” Al’ameen ya k’araso ya karb’a ta a hannun ta yace, “ta fadin sosai, Sannu Zaytun kiyi shiru.” Kuka take kawai tana kiran Daddy ya kalle ta yace, “wajan Daddy zaki je?.” Ta d’aga kai alamun eh tana kuka yace, “shikenan zan ki ki wajan sa, ki daina kuka.” Ya kalli Ameena yace, “in kin shiga ki bata magani wannan bugewar zata iya saka mata ciwon kai.” Ta d’aga kai alamun to ta kwanta a jikin sa tana Ajiyar zuciya ya kalli Ameena yace, “kina ta mamakin dalilin kira na ko?.”
Tayi murmushi tace, “babu komai ai nasan alkhairi ne.” Ya girgiza kai yace, “naje na duba mahaifin yarinyar nan ne yanayin da yake ciki bai min dadin gani ba Ameena, yana so ki koma wajan sa in kina da ra’ayin haka.” Ameena ta kalle shi yayi dariya yace, “kar ki damu dani kamar Adam nake yayan ki ne ni duk abinda yake daidai shi zan so naga kin d’auka. Mahaifiyar sa a yanzu kuka na tarar tana yi saboda jikin sa ya tashi ana tunanin ciwon kan da yake damun sa ma kamar ya tab’a kwakwalwar sa sai anyi hoto an gani. Kuma duk saboda ke yake a wannan yanayin Ameena, duk namijin da zai zube a gaban ki yana kuka akan ta amince dashi ba k’aramin so yake mata ba, a ajjiye batun so ma yayi nadama sosai na tabbatar bazai sake kuskuren da yayi a baya ba Ameena.”
Ameena ta sauke numfashi tace, “to ni yanzu ya ake so nayi?.”
“Tunani zakiyi, in har zaki iya cigaba da zama dashi ba dan halin sa ba dan mahaifiyar sa da kuma yarinyar nan kiyi hakan Ameena. İn baza ki iya ba kar ki cuci kanki sai a bashi hak’uri in silar hakan in ya samu cutar ajali dmaan lokacin sane yayi.” Ameena ta girgiza kai tace, “To Yaya Al’ameen zan yi tunani akan hakan.”
“Yauwa Ameena. Kar ki yi tunanina yayan ki ne nima shiyasa nake fad’a miki abinda nake ganin ni a raina na karb’e shi.” Ameena ta girgiza kai b’ata ce komai ba ya kalli Zaytun da tayi bacci a kafadar sa yace, “kuka take tana kiran Daddy rashin ganin sa shine ya saka ta bacci, tana son mahaifin ta a kusa da ita ki tausaya mata kar tayi rashin sa a kusa da ita.”
Ameena ta girgiza kai tace, “to Yaya zan yi tunani ina addu’a kuma abinda yake daidai Allah ya bani.”
“Shikenan kuwa zaki ga daidai a rayuwar ki, in ni ne na kasance daidai din zaki gani, in Yusuf din koma masa shine daidai duk zaki gani.” Ta girgiza Kai cikin gamsuwa yace, “karb’e ta kije ki kwanta, yanayin da na same shi ne ya saka na kasa hak’uri sai da nayi magana dake.” Ta karb’i Zaytun ta koma ciki shi kuma ya fita. Kai tsaye d’aki ta wuce Yaya Adam ya bita da kallo kafin ya tashi ya bita ya same ta zauna tayi tagumi yace, “Al’ameen yace miki?.” Ta kalle shi tayi shiru bata ce komai ba yace, “maganar Yusuf yayi miki ko?.” Ta daga kai alamun eh yace, “kinga ki ture maganar sa in dai har yanzu zuciyar ki bata amince dashi ba kar ki cuci kanki.”
Ameena tace, “Yaya kai ka amince dashi ne?.” Ya kalle ta sai ya zauna a kusa da ita yace, “A baya na fiki d’aukar zafi akan lamarin Yusuf Ameena, amma a yanzu tausayi yake bani Allah ya sani, dan nace yana bani tausayi ba hakan yana nufin ina so ki koma ba, ko kusa wallahi abinda yake daidai a wajan ki shi zaki d’auka, lokacin da kika sha a wahala a tare dashi babu wands ya sani, ynzu kuwa babu wanda zai saka ki koma wajan sa sai in ba ke kike son hakan.”
Ameena ta kalle shi tace, “badan shi ba ba kuma dan halin sa ba Yaya” ta kalli yayan sosai tace, “Saboda Zaytun da Ammah na amince zan koma Yaya, amma bana so yasan da hakan a yanzu.” Yaya Adam ya kalle ta yace, “Ameena kar kalaman Al’ameen suyi tasiri a ranki har ki amince da abinda baki yi niya ba. Kar ki yanke hukunci da gaggawa ki nutsu sannan ki yanke hukunci Ameena.”