Sashe 5
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi yayi yabi bayan ta ya ya same ta sa tsaye a jikin bango tana sauke numfashi ya kalle ya yace, "Ameena me ya faru?." Murmushin yaqe tayi tace, "babu komai Yaya." Ya dafa kafadarta yace, "Kiyi hak'uri na bashi ita ba tare da na nemi izinin ki ba, zai dawo da ita gobe bana so ta dawo tana kuka tunda tana son kasancewa da mahaifin ta a barta tayi hakan."
"Babu komai Yaya, duk abinda kayi daidai ne."
"Ga chocolate nan da ya kawo mata sai ki ajjiye in ta dawo zata sha" Ajjiye mata ledar yayi a kan katifa kafin yace, "Ameena Yusuf ya sake ki saki d'aya."
K'irjin ya buga da sauri ta runtse ido tana sake Jan numfashi tana saukewa a hankali, hawaye yaga sun sakko daga idanun ta sai ta bashi tausayi sosai a shekarun ta in ba kaddara ba me zai kaita ga zaman gida da sunan mutuwar aure, sannan ya tabbatar tana son Yusuf duk da ya ragu sosai amma shi bazai iya barin ta tare dashi bane dole sai ya raba su. "Kiyi hak'uri Ameena tunda har ya furta baya son ki banga amfanin zama dashi ba, Ameena koda yana sonki abubuwan da suka faru sai na saka ya sawwake miki balle ma baya son ki. Gwara ace baya son ki yana zaune dake Lafiya akan ace yana sonki yana azabtar dake. Ameena matsayin mahaifi nake a wajan ki bazan cutar dake ba, duk Inda nasarar ki take a duniya da cigaban ki shi nake nema miki. Raba ki da Yusuf da nayi ba cutar ki nayi ba ko hanaki abinda kika so face nema miki mafitar damuwar ki dan gudun nan gaba."
Sai a sannan ta bud'e ido ta goge idanu tayi murmushi yaqe tace, "Wallahi babu komai Yaya, kar ka manya nima ina goyan bayan raba mu din kuma ina ji a jikina shine alkhair a gare ni, kawai dai naji wani iri ne da naji ka ambaci saki a kaina" ta fad'a tana sauke kanta kasa tana goge idanun ta. Yace, "nasan zaki ji hakan amma ki cire ranki daga gare shi, ki kalli rayuwar ki ta yanzu kar ki tuna ta baya domin ta riga ta wuce. Ki saki jikin ki duk abinda kike so zan miki, in ma makaranta kike so ki koma Ameena zaki koma kafin ki sake yin wani auren."
Kai take d'agawa tace, "To Yaya na amince da duk abinda kace, in sha Allah zan yi."
"Yauwa Ameena, wannan d'ar-d'ar din da kike yi ne bana so bana jin dad'i ko kad'an, ki saki jikin ki ba'a kanki aka fara mutuwar aure ba, ki manta da komai dan Allah ki sake kiyi. rayuwar ki ta farin ciki. Ina jin babu dad'i in naga kina zaman d'aki ko kina kuka, bana son hakan Ameena ki daina."
"Daga yanzu na daina in sha Allah Yaya." Yayi murmushi yace, "Ko Kefa, Saura na dawo naga kina kuka" ya fad'a yana fita daga d'akin yana fita ta k'arasa kan katifar ta zauna tana kallon ledar.
Baya tayi ta kwanta ta lumshe idanun ta tana jin wani iri in ta tuna a yanzu fa bata da aure sai gaba ta ya yanke ya fad'i tunawa Itafa bazawara ce a yanzu, idanun ta ta sake gogewa tace, "in sha Allah zan manta da komai daga yau in sha Allah, kodan saboda Yaya na daina saka damuwar komai a zuciyata." Hawayen take so ta tsayar amma sun k'i tsayawa sai kawai ta tashi ta shiga band'aki.
Yusuf a haka ya koma gida yayi parking mota ya fito ya rik'e hannun Zaytun suna takawa a hankali zuwa cikin gidan, kulle k'ofar yayi ya shiga ciki ya sau saman a nan ya samu Asiya a tsaye daga ita sai d'aurin kirji ta bishi da kallo tana kallon Zaytun zuciyar ta na bugawa. Bata ce masa komai ba shima bai ce ba ya shiga d'aki ya zauna a gefen gado ya zaunar da Zaytun akan gado yana kallon ta tana tacin biskit din da ya bata ta b'ata bakin ta gabad'aya da madarar dake jiki, ya kalle ta yace, "kin b'ata jikin ki."
Asiya ce ta shigo tana kallon Zaytun ta kalle shi tace, "A ina ka samo Zaytun kuma" sai ta tsuguna a kusa dashi tace, "zuwa gidan su Ameena din kayi?, me kaje yi to? Sakin ta kayi ko kuma me?." Yadda jikin ta yake bugawa saboda wari shine ya saka shi yin baya ya yamutsa fuska bai ce komai ba.
"Magana nake maka fa, wajan Ameena kaje ne?." Kallon ta yayi kamar zai magana sai akwai ya share ta ta sake cewa, "magana fa nake yi, an ina ka samo Zaytun ka tawo da ita? Kar kace min fa a nan zata zauna." Baice mata komai ba ya tashi ya shiga band'aki ta bishi da kallo kafin ta kalli Zaytun da take cin biskut din ta tace, "Chab, ai wallahi in ma ka dawo da ita ne wallahi bazan rike yarinyar nan ba gwara ma a san nayi" ta fad'a tana kallon ta a lokacin itama ta kalle ta sai kuwa ta zare mata idanu.
Zaytun sai ta tsorata ta kama kanta ta nutsu sosai Asiya ta fita ta bar d'akin, bai jima ba ya fito yana yamutsa fuska gabad'aya baya son zama a b'angaren da komai na dakin wari yake har bandaki. Tana ganin sa Zaitun ta sakko daga kan gadon taje ta rike shi tace, "tsoron ta nake ji." Kallon wajan yayi yaga bata nan ya rik'o hannun ya ya zauna da ita shima ya zauna ya saka tissue yana goge mata baki.
"Daddy ka kaini wajan Mummy" ta fad'a zata yi masa kuka yace, "kar ki yi kuka zan kai ki, wajan Mummy kike so kije?." Ta daga kai alamun eh yace, "to zaki je." Asiya ce ta sake shigowa sai Zaytun ta rik'e shi tana kallon Asiya ya kalle ta shima yace, "me kika yi nata daga shiga ya band'aki take tsoron ki?." Asiya tace, "Ka ji min mutum, me zan yiwa wannan yarinyar? Kawai makirci ta gado daga wajan uwarta shiyasa take wannan rarraba Idon kamar munafuka."
Kallon ta yayi yana jin zafi a zuciyar sa musamman uwarta da tace sai bai kula ta ba ya cigaba da rarrashin Zaytun ta kalle shi tace, "yauwa ka saka ta tayi bacci dan ni yau sai an bani hakkina ko me za'ayi. Haba kwana kusan goma sha fa kenan Kullum kace min baka jin dad'i yau dai bazan iya hak'uri ba wallahi. Ai nayi hak'uri na baka dama dan naga kana cikin damuwa na kyale ka amma yanzu ni wallahi bazan iya ba." Bacci Zaitun ta fara a jikin sa ya kwantar da ita yana bubbuga bayan ta har tayi bacci ya kalle ta tana tsaye a gaban sa tace, "kaji ai abinda nace, ni na gaji wallahi kazo muje dakina ko kuma mu kwanta a nan" ta fad'a tana murgud'a baki.
"Asiya fita ki bani waje." Da mamaki yake kallon sa ganin kamar ma abinda take yi a kansa baya tasiri wani lokacin taga yana aiki wani lokacin taga akasin haka kamar mai aljanu tace, "kamar ya na fita bayan na fad'a maka abinda ya kawo ni?, babu inda zani sai ka bani hakkina bazan iya jurewa ba n fad'a maka."
"Asiya nace ki bani waje."
"Wallahi bazan fita ba." Da sauri ya kalle ya yaga idanun ta kyam a kan fuskar sa babu alamun tsoro a tare da ita tace, "har yanzu ace ko ciki na kasa yi saboda rashin kula da nake samu daga wajan ka, wallahi bazata sab'u ba ko ka bani hakkina ko na kai k'arar ka wajan iyayen ka."
"Ki kai karata wajan wa?."
"Wajan na gaba dakai mana, ai wannan abu ne mai mahimmaci da duk wanda na fad'awa sai ya tsaya ya saurare ni." Mamaki take bashi sosai ya girgiza kai kawai ya kalle ta yace, "to baza ki samu ba, ki fita ki bani waje Malama."
"Wallahi in ban samu ba sai na kira Ammah na fad'a mata" ta fad'a tana niyar fita ya dakatar da ita yace, "Baki da hankali? Da gaske kike zaki iya fad'awa Ammah?." Ya matso kusa da ita yana kallon ta yace, "Sai ki fad'awa Ammah haka? Kice mata nak'i baki hakkin ki?."
"To ba so nake ba, kuma ai hakkına ne ko gaban alqali naje sai ya Karb'ar min" ta fad'a tana kallon wani wajan daban. Kallon ta akwai yake yi kafin ya koma da baya ya zauna yayi shiru baice komai ba dan ya rasa bakin magana sai kallon ta kawai. Matsowa tayi kusa dashi ta dafa kafadarsa tace, "My love kwana biyu kawai daurewa nake, dan Allah ka saurare ni yau din nan" tav fad'a tausashe tana kallon sa. Wallahi shi warin da take yi yafi komai d'aga masa hankali a wannan lokacin, taya zai iya yin wani abun da ita tana wari haka ai sai yayi amai.
Ya cire hannun ta daga jikin sa yace, "kije ki yiwanka dan Allah." Ta Harare shi tace, "ni bazan wanka ba sai bayan an gama, Nidai ka amince kawai bazan iya bacci ba." Kallon ta yayi suka had'a ido ta sake marairaicewa ya d'auke kai daga kallon ta ya kalli Zaytun da take bacci ya sunkuyar da kai baice komai ba.
Masifa yake so yayi mata ya kora ta waje inda hali ma mare ga ma amma sai yaji ya kasa yin hakan sai shiru ma da yayi ya sunkuyar da kai ya rasa ma abinda zai yi yaji dadi. Shafa jikin sa take yi dan towel ne kawai a jikin sa da ya fito daga wanka bai saka kaya ba ya d'auke hannun ta yace, "ki jira ni a dakin ki gani nan."
"Ka tabbatar zaka zo?." Ya d'aga kai alamun eh ta fita ya bita da kallo ya kalli Zaytun sai ya shafa goshin ta ya mik'e ya k'arasa kusa da window yana kallon window din Ameena dakin duhu kamar Kullum. _Shikenan Ameena ta tafi?._ sai yayi saurin barın wajan jin zuciyar sa na kawo masa abinda gangaar jikin sa bata so.