Sashe 72
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
B'angaren Yaya Adam yana barin wajan Al'Ameen mota ya hau ya fita a nan yayi karo da motar a ajjiye ga alamun dukan motar nan a jiki, sai gaban da sa fad'i sosai da sauri ya faka motar ya d'auki waya ya kira Abbah yake sanar dashi abinda ya faru sai ya juya motar ya nufi asibitin a nan ya tarar dasu har Ammah a zaune ya k'arasa shigowa d'akin suka gaisa gabad’ayan su yace, "ya mai jikin?." Usman yace, "Gashi dai a kwance har yanzu da yake abin bai jima da faruwa." Adam yace, "Subahanallahi, naga fitowar sa daga wajan Al’ameen, Daman shima Al’Ameen din sai da yace min bai amince da yanayin sa ba, ai kuwa na fito na hau titi naga motar tasa a ajjiye badan ma na gane motar ba bazan kula da motar ta sa bace ba."
Abbah yace, "Allah Sarki ka kyauta wallahi, Allah ya bar zumunci. Allah ma ga taqaita ai, ciwo ne a fuska da kuma hannun sa kawai.” Ya amsa da amin kafin yace, “Allah ya cigaba da kiyayewa.” Nan ma suka amsa yayi musu sallama ya tafi.
Inda ya fito dan zuwa yaje sannan ya koma gıda ya tarar da falon babu kowa sai Zaytun da Shukra suna wasa, "Ameena!" Ya fad'a da k'arfi ta jiyo ta amsa daga ciki ta fito yace, "kin bar yara suna wasa su kad'ai sai sun yi b'arna?." Ameena tace, "Muna ciki Muna hira ne, Yayan Bauchii ce tazo." Sai ga Yaya ta fito ya kalle ta yace, "ke kuma zuwan yamma?." Tayi dariya tace, "barka da Yamma Yaya."
"Yauwa barka. Ya hanya?."
"Alhamdulillah. Ina zuwa kana fita shiyasa."
"Eh na fita ma sai na canja hanya na wuce asibiti, motar Yusuf na gani baban Zaytun a gefen titi ashe accident yayi sai naje na duba shi na dawo." Yaya tace, "Subahanallahi, amma dai akwai sauk’i babu babban ciwo ko?."
"Eh babu, Mahaifin da yace min bugawa ce kawai a hannu sai fuskar sa da taji ciwo."
"Allah ya kara Lafiya."
"Amin." Ya kalli Ameena yace, "baki ce komai ba, baki ji nace baban y’ar ki bane yayi accident?."
Tace, "Alalh ya bashi lafiya" ta fad'a tana juyawa ta koma ciki ya bita da kallo Yaya ma haka ya kalle ta yace, "me kika fahimta a yanayin ta? Tana son komawa Yusuf ne?." Yaya tace, "bana ce ba gaskiya, amma a zahiri bata nuna hakan amma ban san meye a zuciyar ta ba. Abu d'aya na sani har gobe tana son Yusuf." Yaya Adam yace, "meyasa kika ce tana son sa?." Tayi dariya kad'an tace, "Saboda shi so so ne." Yayi y’ar dariya yace, "kuma Yusuf din daga wajan Al'ameen ya tafi, duk naji abinda suka tattauna rok’on sa yake akan ya shiga gaba wajan sake samun Ameena, ina jin bai fahici shine zai auri Ameena b." Yaya tace, "Allah Sarki, watakila tunani ya saka shi yin accident din."
Yaya yace, "to wai ke a ganin ki zata iya komawa ko me?." Yayan Bauchi tace, "to ita nadama dai a bayyane take kuma Yusuf ya yita duk da zahirin sa muka sani bamu san abinda ya b’oye a zuciyar sa ba, amma indai har Yusuf da gaeke ya canja yayi nadama ya gane kuskuren sa Ameena ta koma ba wani abun bane."
"Saboda bakya kishin abinda yayi mata kenan?."
"Ba haka bane, abu ne a bayyane Yaya yana sonta tana sonsa wannan mikin abinda yayi mata shine a zuciyar ta, amma da za'a ce mata wannan ba wancan Yusuf din bane wani ne daban sabo wallahi a guje zata amince. Na farko dai suna da yarinya ya kamata ka tuna wannan, na biyu kuma tana tausayin sa sosai dan yana sonta wallahi ko a lokacin da abubuwan suka dinga faruwa ma yana sonta iskanci ne da kuma matar da ya aura. Dan haka a yanzu in ta koma masa wallahi a b’angarena babu damuwa dan nasan abinda ya aikata a baya wallahi bazai sake aikatawa ba a yanzu ba.”
Yaya Adam ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokaci yana kallon takamar mai tunani kafin ya tashi ya shiga ciki yana cewa, "kema kije ki huta." Tayi murmushi ta koma d'akin Ameena tana jin tausayin Yusuf har cikin zuciyar ta domin soyayya tana bashi wahala a bayyane hakan ya nuna yayi nadama aka sake bashi dama sai kowa yayi mamakin sa.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500
Book3
037
Alhaji Bello tun bayan guduwar su Fiddausi duniyar ta juya masa baya, duk yadda ya kai ga ganin ya daidaita lamarin sa kasawa yayi komai ya kwab'e, komai ya lalace tun yana ganin abun kamar wasa har ya daina domin kuwa tun yana hauka sama-sama har ya zama hauka yake yi tuburan sai da aka kulle shi a d'aki. Duk wani harkar kasuwancin sa ta d'urkushe kowa ya gushe shi babu wanda yake tashi daga shi sai y'an aikin da akwai a gidan. Babu wanda yake sauraren sa su kansu tunda suke kulle shi basa zuwa inda yake saboda duka yake yi gashi tsirara yake yi, a d'akin yake kashi ya cinye kayan sa yayi fitsari yabi ya shanye abin sa.
Y'an aikin ne gabad’aya suka had'a meeting akan k’ananun y'ay'an sa duk suka taru dan su tattauna akan su mutum d'aya yace, "Alhaji Bello dai ya haukace, hauka wanda aka kira tuburan shi Alhaji yake yi, haukan da yake yi dakyar ya warke gaskiya sai ma dai ya sake lalacewa. Ba shine abin tausayi ba wannan yaran sune abin tausayi, ko wacce uwa ta gudu ta bar masa yaro gashi yanzu shi ba hankali ne dashi ba balle yasan abinda zaiyi akan su. Kafin kowa ya tattara kayan sa ya gudu a fad'a mana ya zamuyi dasu?. D’a na kowa ne, dan min taimake su ba wani abun bane lada ma zasu samu akan hakan.”
Baba Ladidi tace, "bamu san dangin sa ba balle mu kai su, dan ni badan yaran nan ba wallahi da yanzu na Kama gabana. Bamu San inda iyayen da suke ba balle mu kai musu yaran su, gashi an kira uwar gidan sa an sanar da ita tace kar a sake mata waya akan lamarin sa, babu ita babu shi kuma babu yaran ta a lamarin sa." D’aya yace, "Akwai shawara, me zai hana mu nemi Nabila ko tasan wani nasa?."
"Eh shawara ce mai kyau, ina da lambar ta kuma bara na kira naji me zata ce." Aka kira Nabila wayar na ringing bata d’auka ba aka sake kira sai ta d'auka yace, "Hajiya Nabila an tashi lafiya?." Daga can b'angaren tace, "fadi Matsalar ka kawai malam."
"Daman akan rashin Lafiyar Alhaji Bello ne muka kira ki, daman...." Ta dakatar dashi tace, "kaga fad'a min Matsalar ka kawai bana son hayaniya."
"Daman muna so mu san wani nasa ne saboda mu kai yaran nan nasa." Tayi tsaki tace, "kai baka sanni ba ban San ka ba, ban san wani Bello ba balle ayi min zancen yara ka gane ko?. Daga yau ka goge lambata daga wayar ka kar wani abu nasa ya sake tasowa ka kirani ka mana yi min maganar banza ka gane ko?."
Kafin yayi magana ta katse kiran ya kalle su cike da mamaki da tsoro yace, "lallai duniya budurwa wawa, wai Nabila ce take cewa bata san shi ba kar a saka had'a ta dashi koda nan gaba." Duk suka girgiza kai kafin daya yace, "Yanzu meye abu na gaba?."
"Kawai mu yiwa yaran nan video mu d’ora a duniya iyayen su in sun gani su zo su kwashe yaran su."
"Shawarar tayi gaskiya, Tunda bamu da wata mafita sai wannan muyi hakan kawai." Sai kuwa suka d’auko yaran suka jera su akayi musu video suka fad'i komai a video.
Kafin wani lokaci abin ya zata social media wanda bai san ma halin da Alhaji Bello yake ciki ba yanzu ya sani wanda basu san halin sa ba sun tausaya masa sosai suna ta jimami, matan sa da ya saka wanda suka bar yaran da wanda ma bai saki ba duk an gani haka aka je ana d'auko yaran dan iyaye suna cewa babu laifin yaro da za'a barshi ya wulakanta.
Fiddausi bata san abinda ake yi ba tunda ba waya ce da ita ba sai da Yaya tazo take nuna mata tana fad'a mata abinda ya faru, hankalin ta ya tashi gashi bata da lambar su Naja'atu balle ya kira su ta fad’a Muş’u halin da ake ciki. A lokacin Abba yace zasu je kotu alqali ya raba auren tunda dai ya zama mahaukaci zama da mahaukaci bazai yu ba. Ai kuwa a washe garin ranar alqali ya raba auren su bayan an tabbatar da ya haukace, fiddausi kamar an saka ta a aljanna haka take ji saboda farin ciki abinda ya rage mata kawai son ganin su Naja'atu.
A ranar da aka raba auren Fiddausi tana zaune tana jimamin duniya da kayan cikin ta, wto komai ka aikata sai ka jirbe shi ko a duniya ko kuma a lahira. Yanzu meye amfanin rayuwar alhaji Bello? Ace mutum ya haukace yana cikin kashi da fitsari babu mai sauraren sa balle ma ass a wanne hali yake ciki? Kowa ya guje shi saboda mummunar dabi'ar da yake da ita, hatta masu zuga shi akan lamarin duk sun gudu daman sai dadi ake tare da kai da wahala ya samu sai a gudu a barka.
Tana zaune sai ga Mama ta bata waya tace, "Gashi neman ki ake yi." Ta goge hawayen idanun ta ta karb'i wayar ta saka a kunne daga can akace, "Fiddausi Naja'atu ce. Fiddausi tace, "Naja'atu! Kece?.”
“Nice Fiddausi, ya kike?.”
“Lafiya lau, daman kina da lambar Mama?."
"Bari kawai Fiddausi, da naje Abuja ne zan d'auko yaron wajena shine na shiga gidan na d’auko wayar nan da kika bani lamba kawai dan na neme ku keda Aliya. Dan in ba ta haka ba ban San a inda zamu ga juna ba.”