Sashe 88
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma kallon Asiya take yi tace, "Ai dole ne ma Yusuf ya sako wannan rashin tarbiyyar da kike yi shi kika nuna masa."
"Ai koya min akayi, da ba'a koya ba ban yi ba" ta fad'a bata kalli Umman ba sai kuma ta fara hawaye tace, "Wayyo Allah, bani da aure bani da mai sona ya zanyi ni Asiya?." Fauziyya tace, "Da wannan shegiyar k'azantar taki waye zai d'auke ki?."
Asiya bata kula ta ba ta zauna a k'asa tayi shiru kawai Tana hawaye in ta tuni bata a da aure sai taji gabad'aya yanayin ta ya canja komai taji yana yi mata zafi musamman in ta tuna gıda da ta baro. Fauziyya tace, "ke shegen halin ki shine ya saka ya sako ki ai."
"Akwai Wanda ya tab'a ce min na canja na daina ne a cikin ku? Akwai Wanda ya tab'a min fad'a akanabinda nake yi?. Umma ce min take in ya dake ni na rama, ta tab'a cemin ki daina yin abinda kike yi an tab'a fad'a min ne?."
Maimuna tace, "sau nawa ina yi miki magana akan k'azanta?."
"Bayan wannan kin tab'a cemin ga wanda zan daina?." Maimuna tayi shiru bata amsa ba ta kalli Umma tace, "Komai na gidan a kaina yake, ba'a tab'a cemin kar na d'auko na kawo ba Kullum cikin zuga ni kuke yi Ana cewa na nuna masa ina da y'anci. Ko yaushe maganar ku Kenan ba'a tab'a cemin abinda kike yi ba daidai bane. Sai yanzu dan a sake ni sai a dinga min ce dole ma ya sake ni saboda halayya ta?tun baya meyasa ba’a ce kin nan gab zai iya saki na saboda su ba?."
Baba da yake ji yace, "Yauwa Asiya tambayi babar ki ta baki amsa. Tun farkon auren ku na tabbatar mata da alkhairin auren ragagge ne amma tace ita ina sai kin je ko me zai faru. Ki bata amsa Atika kin tab’a cewa ta daina yiwa mijin ta rashin kunya?." Umma tayi shiru bata amsa ba ya kalle ta yace, "Yanzu kika fara ganin abubuwan da kika aikata ai, ke kina ganin ke kike komai a gidan nan ban isa nayi magana ba saboda karayar arzukin da na samu. Kika sake amfani da malama ki kika mallake ni babu abinda na isa nace koda akan yaran nan ne, to yanzu gasu nan na bar miki du ai sai ki basu tarbiyyar Dani bazan basu ba."
Fauziyya tace, "ina tarbiyyar Baba? Kowa gudun auren mu yake saboda bamu da tarbiyya, kuma nima na yarda domin Umma bata tab’a cewa mu girmama na gaba ba, ko yaushe cewa take duk Wanda yayi mana kar mu kyale shi. Koda a dangin kane cewa take yi basa sonta mu ma kar mu so su, Mun Raina komai babu Wanda yake son mu ko shiga muka yi babu mai kallon mu muma haka.” Baba yace, "ku kuma da yake ilimin addini bai ishe ku ba komai tace muku aikatawa kuke yi, bakwa koyi da k’awaye da y'an uwan ku duk abinda tace ku yi shi kuke yi koda bashi da kyau babu wacce ta tab'a cewa hakan ba daidai bane. Dukkan ku yanzu kuka fara gani ai, za Kuyi dana sani daidai abinda kuka aikata a rayuwar ku." Ya kalli Umma yace, "badan yaran nan da nake kallo ba wallahil azim da yanzu bakya gidan nan, to shekaru sun ja ko babu komai na duba yaran suna son kasancewa dake wallahi da sai kin bar gidan nan."
"Baba ta bari din kawai, ko zamu samu mu canja daga halayyar da muke yi. Tasan ana ajjiyewa na d'auka amma bata tab'a yi min fad'a ba tun kafin aure, in Kaga tayi min fad'a tabbas nata na d'auka amma in daga waje ne sai kaji tana ki dai kula kar a kama ki wata rana. Nidai gabad'aya cutar rayuwata akayi, nafi kowa cutuwa a cikin su” Asiya ta fad'a tana cigaba da kuka abinda yake zuciyar ta bai wuce gidan mijin ta Yusuf ba.
Baba yace, "to ai sai kuje ku cigaba da asirin ki sake komawa gidan nasa, dmaan auren ai ba na Allah da annabi bane, a gina shi akan turbar mallaka da kuma samun arzuki. Sai kuje a cigaba daga inda aka taaya ko za’a samu ya mayar dake" baba ya fad'a yana fita ya barsu Asiya ta kalli Umma dukkan su ma kallon ta suke yi ta rasa abinda zata ce musu sai ta shiga d'aki kawai tana kukan zuci.
Rukayya tana tare da mijin ta yana rik'e da Noor a hannun sa ita kuma tana gefen sa tana kallon sa, yana kula da ita sai yayi mata banza dan yaga magana ce a bakin ta sai yayi shiru kamar bai fahimta ba yace, "Noor kullum kyaunta sake bayyana yake, ma sha Allah har tafi Amir kyau." Sai kuwa Rukayya tace, "ai kuwa bata fi Amir kyau ba saboda mahaifiyar Amir ta fini kyau kuma da ita yake kama."
Yayi murmushi yace, "nidai ban gani ba."
"Wallahi ka gani" ta fad'a tana kallon sa ya sake yin murmushi yace, "harda wallahi?.” Bata bashi amsa ba sai Murmushin da tayi tace, "ni daman magana nake so muyi da kai." Ya kalle ta yace, "tunda naga bakin ki yana motsi nasan akwai abinda zaki ce, to Ina jin ki." Tayi y'ar dariya tace, "shiyasa ka k’i kallona ai, nima na gane." Kafin yayi magana tace, "Ka yafewa Fiddausi ko?."
Ya lumshe ido ya bud’e yana kallon ta daman ai tatsuniyar gizo bata wuce ta k’ok’i yace, "Eh mana, bata fad'a miki munyi magana da ita ba?" Ya fad'a ba tare da ya kalle ya ba yana yiwa babyn wasa. Ta girgiza kai tace, "Ta fad'a min. To Khalil tunda da gaske ka yafe mata meyasa baza ka dawo da ita gidan nan matsayin matar ka ba?." Da sauri ya kalli Rukayya ya wara idanun sa yaga da gaske fa itace tayi maganar ba wani ba yace, "Rukayya kin San abinda kike fad'a kuwa?." Ta girgiza kai tace, "na sani, so nake ka dawo da Fiddausi gidan nan matsayin matar ka tunda daman ai saki d'aya ne akayi mata shima kuma na gargad'i."
Girgiza kai yake yi yana kallon ta cike da mamakin abinda take cewa wanda a wajan sa bazai yu ba kafin yayi magana tace, "ka ajjiye batun kishi a gefe Khalil, matar nan tun kafin na fara kishin ka itace take kishin ka domin itace matar ka ta farko kafin na sanka itace ta sanka." Sai yayi dariya yace, "ke yanzu a ina zan saka Fiddausi? Ai bani da wannan wajan." Jin abinda yace sai tace, "Ba ga sabon gidan da ka siya ba, daman y’an haya kace min zaka saka to me zai hana ba zaka saka ta a gidan ba?."
Ya kalli Rukayya yace, "ai yayi mata kad'an."
"Kamar ya yayi mata kad'an?."
"Ba irin sa take mafarkin samu ba." Rukayya ta gane me yake nufi ya sassauta murya tace, "tayi nadama baza ta sake aikata abinda tayi a baya ba." Ya dakatar da ita yace, "kafin mu d’ora daga labarin da kike bani tsaya na baki wani labari tun jiya nake son fad'a miki sai na manta. Akwai wata y'ar Uwar Hajiya to yarta cousin dina kenan yarinyar ma sha Allah tana dakyau dan mahaifin ta yan sudan ne kika ganta dai kice bata jin Hausa. Tayi aure tana zaune a gidan mijin ta iftila'in wata annoba ya same ta a fuskar ta, kuraje masu ruwa duk suka fito mata a fuskar ta lalace ta zama kamar dodo in kika ganta. Kwatsam wannan mijin nata ya fara yi mata rashin mutumi dan so yake ya sake ta amma ya rasa taya zai yi hakan, zagi, cin mutunci har gaban iyayen ta fa kawai saboda yana son ya sake ta. K'arshe dai ya samu ya rabu da k'aya ya sake ta dan yace bazai iya zama da mai annoba ba. Ana tayi mata magani ba dare babu rana sai ciwo ya warke ya tafi gabad'aya tabo d’aya babu a fuskar ta sai ma sake kyau da tayi, yanzu zancen da nake miki mijin nan ya dawo dan Allah a bashi matar yayi kuskure bazai sake ba, ke in ke ce matsayin ta zaki koma dan Allah?."
Rukayya da take girgiza kai cikin masifa tace, "kan Bala'i! Me zai kaini komawa? Ai wannan ba dan Allah yake sonta ba dan kyau ne, gashi lokacin da ya gushe ya koro ta yanzu kuma da ya dawo ya sake dawowa dan bashi da kunya bashi da mutunci. Ka bata shawara kar ta koma wallahi ba don Allah yake son ta, dan wani abun da yake dashi ne in ya sake gushewa zai kuma sakin tane." Ibrahim yayi murmushi mai sauti ya kalle ya yace, "daman ai bazata koma ba."
"Wannan shine daidai, ta samu wani wanda zai so ta Tsakani da Allah ta aura."
"Ta samu ma."
"Shikenan Alalh ya basu zaman Lafiya." Ya kalle ta yace, "Amin. Kinga wannan labarin dana baki?; ina so ki juya shi ya koma kan Fiddausi."
Ta kalle shi yace, "Fiddausi ta guje ni saboda bani da kud’i, ni talaka ne bani da mota, bani da keke, zaman gıda babu haske, kullum bazata ci kaji ba, baza ta zauna a a.c ba, babun dai ta wajena tana da yawa. Wannan dalilin ya saka ta dinga rashin mutuncin da har a gaban su Hajiya bata raga min ba, idanun su Hajiya ta kalla tace bata sona bata qauanr zama dani aka tilasta mata sai ta kashe ni. Me nake dashi da zan dawo da ita Rukayya? Haka akwai na dawo da ita wata ran ta kashe ni bayan ina da mata da iyaye da yaran da suke bukatar kulawa ta?."