Sashe 50
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D'agowa tayi ya kalle shi tace, "kayi hak'uri hakan baza ta sake faruwa ba. Ka fad'a min abin farin cikin da yake bakin ka." Ya tab'e baki yace, "ai banga farin ciki a fuskar ki ba." Tyi murmushi tace, "Allah har zuciyata ina cikin farin ciki so nake naji me zaka ce." Ganin tayi murmushi sai yaji dadi amma baiyi murmushin ba tace, "Haba dan Allah kayi murmushi ka fada min."
"Sai na ja miki aji kamar yadda kika yi min."
"Haba dan Allah kayi hak'uri." Ya kalle ta ido cikin ido kamar zai magana sai yayi shiru tace, "Dan Allah ka fad'a min." Yayi murmushi yace, "in na fad'a wanne goron albishri za'a bani?."
Ta kwanta a kafadar sa tace, "duk abinda ka zab'a na Baka zabi ni kuma zan baka."
"Kin tabbatar?."
"Na tabbatar."
"Kin yi alqawari?." Kamar zatayi kuka tace, "nayi mana, haba kaima dan Allah kamar wani Amir." Yayi dariya yace, "so nake na tabbatar ne ai." Ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa yayi dariya ta fara kukan shagwab'a tace, "ka barni cikin tunani dan Allah ka fad'a min."
"Ogan mu yau ya dawo daga lagos ya kuma zo har inda nake ya kira ni da kansa naje har office din sa a nan yake shaida min na shirya ina cikin Wanda ya bawa umrah a wannan shekarar. Farin cikin lissafin da aka fitar ta b'angarena tukwici shine umrah." Rukayya ta wara ido tana kallon sa tana murmushi shima haka tace, "da gaske kake?." Ya d'aga mata kai alamun eh ta sake komawa jikin sa tace, "Alhamdulillah! Kaii wannan labari ne mai dadi Wanda ban yi tunanin jin sa ba, Yanzun haka mana nufin da kai za'a tafi umrah a wannan shekarar? Kai Alhamdulillah naji dadi sosai."
Ganin ta gigice tana farin ciki sai yace, "nutsu mana."
"Taya zan nutsu bayan ka fad'a min abinda zai saka na fita daga nutsuwar tawa?." Yayi murmushi yace, "wallahi da ya fad'a min ji nayi kamar a mafarki, na rasa wacce irin godiya ma zanyi masa."
"Dole ka rasa, dole ka rasa abinda zaka ce. Allah ya saka masa da alkhairi ya biya shi da aljanna." Ya amsa da amin kafin yace, "amma ne kike ganin zanyi wanda zan nuna masa ina cikin farin ciki?." Tayi shiru kafin tace, "da kai da Alhaji zaku har gida ku yi masa godiya zai ji dadin hakan sosai, in mahaifiyar sa na da rai ko mahaifin sa mu siyi kaya ko wani abu na ci muje nida kai mu kai mata muyi mata bayani, na tabbata zai yi farin ciki da hakan."
Ya girgiza Kai yace, "wannan shawara ce mai kyau, amma zan samu Alhaji da maganar anjima naji abinda zai ce."
"Wai ni na fara sani?."
"Ina da wacce ta fiki ne? Ina da wacce tafi kusa dani bayan ki ne?." Dadi ya mamaye mata zuciya tace, "babu sai ni din." Yace, "yanzu ranar Monday zamu je ayi min passport."
"Kaga ikon Allah ko? Kawai niyar alkhairi da akayi za'a yiwa Alhaji da Hajiya sai gashi Allah kaima ya so ka a ciki." Yace, "bayan ya fad'a min abinda yazo raina kenan nima, nace ikon Allah kenan wato in ka ayyana alkhairi ko baka aikata ba Allah baya barkn ka haka."
Murmushi yaga tana tayi alamun tana cikin farin ciki yace, "in Allah yayi tafiyar sai mu tafi nida ke da Hajiya." Ta kalle shi tace, "Alhajin fa?." Ya sauke numfashi kafin yayi magana tace, "baza'a je dani ba ba sai Alhaji yaje, in kuka dawo kamar yadda Allah ya bayar da wannan damar Nima zai kawo tawa sai mu koma." Yayi murmushi yace, "in sha Allah dake za'a yi tafiyar nan." Ta amsa da Amin yace, "Anjima zanje na fad'awa su Hajiya sannan suma ina so nayi musu passport amma kuma bazata nake so nayi musu bana so su san na biya musu sai za'a tafi. Allah yasa tafiyar ta zama daidai ma baza'a yi saurin siyan ticket ba sai ya bani lokaci sai a daidaita tafiyar."
"Ai kawai ka fad'a musu tunda kaga za'a je passport."
"Za dai mu gani, kema har ke za'a yi bamu san me Allah zai kawo gobe ba." Tayi dariya tace, "Allah ya amince." Shima dariyar yayi suka cigaba da tattauna yadda abin zai kasance.
A gidan su Yusuf Ammah na zaune tana kiran Mubarak baya d'auka a haka Ysuf ya shigo ta kalle shi bayan ta amsa sallama tace, "kai da baka da lafiya me fito da kai?." Ya zauna yace, "naji sauki ai, barka da yamma."
"Barka dai, ya jikin?."
"Da sauki."
"Allah ya Kara Lafiya." Ya amsa da amin tace, "Kaga Mubarak?." Ya girgiza kai alamun A'a tace, "yazo ya mayar da Zaitun gida gobe taje makaranta."
Yusuf yace, "tana ina?." Bata kalle shi ba tace, "tana ciki." Zaiyi magana sai gata ta fito da babbar wayar Ammah tana game ta kalle ta tace, "yarinya ta iya game kamar babba?." Ganin sa sai ta tawo a guje ta fad'a jikin sa Amma tace, "kina fasa min waya sai baban ki ya biya." Murmushi yayi ya rik'e ta tace, "Daddy ka kaini wajan Mummy." Ammah tace, "Yanzu Mubakar zai zo ya kai ki." Ta kalli Ammah kamar zatayi kuka tace, "ni Daddy zai Kai ni." Ammah ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa sai taji yace, "muje na kai ki." Da sauri Ammah ta kalle shi sai taga ya tashi tsaye itama haka ya rik'e hannun ta zasu fita.
Batayi magana ba suka fito ya saka ta a mota suka tafi gidan Yaya Adam kirjin sa na bugawa sosai. Suna tafiya tana ta yi masa surutu ya had'a ta da waya tana game ya tsaya a wani shago ya siya mata kayan ciye- ciye suka nufi gidan Kai tsaye. Tunda ya doshi gidan gaban sa yake fad'uwa sosai amma kuma yana jin karfin guiwar zuwa shiyasa bai dakata ba har ya iso k'ofar gidan ya faka ya hango Yaya Adam din a tsaye shida Al'ameen ya fito daga motar Zaytun ma ta fito.
Yaya Adam bai gasnu ba sai ji yayi an rik'e shi ta baya ya juya ya ga Zaitun yace, "A'a Zaitun an dawo." Dariya tayi sai ya kalli Yusuf da ya k'araso wajan kamar munafuki sai yace, "Yusuf kaine da kanka? Sannu da zuwa." Jin abinda Yayan yace sai ya samu kwarfin guiwa ya gaishe shi ya amsa suka gaisa da Al'ameen yace, "ya jikin naka?."
"Alhamdulillah naji sauki."
"Allah ya k'ara Lafiya." Ya amsa da Amin Yaya Adam ya kalli Al'ameen yace, "Baban Zaytun ne fa."
Kallon sama da k'asa Al'ameen yayi masa kafin yace, "ga kama nan na gani tun kafin kace."
"Abba ina Mummy?."
"Mummy bata nan amma yanzu zata dawo." Yusuf yana tsaye ya kasa magana ko kad'an zuciyar sa na wani irin bugu mai sauti ya rasa meya kawo hakan. Yusuf magana yake so yayi amma bakin sa yayi nauyi sosai Yaya Adam ya lura da hakan sai yace, "Akwai sak'on da Alhajin ya bayar ne?." Yusuf yace, "eh yace yana gaishe ka."
"Ina amsawa, nima ka gaishe shi sosai. Zaytun jeki gıda gani nan zuwa." Maimakon tayi hanyar gida sai yaga ta nufi wani waje tana cewa, "Mummy!." Kallon wajan sukayi gabad'aya suka ga Ameena ta d'auke ta sai kuma ta sauke ta ta rike hannun ta suka nufo wajan.
Zuciyar mutane biyu ce take bugawa a wannan lokacin, Al'ameen zuciyar da bugawa take cike da kishin Yusuf yana wajan ga Ameena ta dawo baya qaunar Ameena taga Yusuf balle wani abun ya shiga ranta, shi kuma Yusuf zuciyar sa bugawa take saboda ganin ta da abinda yake ji a k'asan zuciyar sa wanda ya jima yana ji gangar jikin sa bata bashi had'in kai akan hakan amma a wannan lokacin yaji ya game jikin sa gabad'aya. Wajan tazo tayi murmushi tace, "Ina Wuni." Al'ameen yayi murmushi bai amsa mata ba sai tayi dariya kad'an zata shiga gida Zaytun tace, "Mummy ga Daddy."
Sai da gaban ta ya fad'i itama ta jiyo ta kalle shi suka had'a ido kuwa sai ta d'auke kai kamar bata gane shi ba ta wuce zuwa gida ba tare da ta sake kallon inda yake ba. Kai ya dafe yayi baya kamar zai fad'i Yaya Adam yayi saurin rik'eshi yace, "Yusuf Lafiya?." Ya kalli Yaya Adam yace, "Kaina ne ya Sara."
"Sannu, daman ai ba lafiya ce da kai ba ai,
shiga motar ka zauna daman me ya Kai ka fitowa kai da Baka da lafiya." Yusuf yace, "babu komai."
"Zaka iya tuk'a motar?." Yayi murmushi yace, "zan iya Yaya. Ga wannan na Zaitun ne." Yaya Adam ya karb'a yace, "to an gode. Ka tafi gida saboda ciwon." Kai ya d'aga ya shiga motar ya jima kafin yaja motar ya tafi.
Yana barin wajan Al'ameen ya kalle shi yace, "kai kace min in kana da rai Ameena baza ta komawa wannan ba." Adam ya kalle shi tare da hararar sa yace, "ai gashi nan ta koma yanzu." Al'ameen yace, "nidai Ina so a tsayar da magana gaskiya Adam indai Ameena zata iya zama dani ayi auren nan a huta, jikina bai amince da wannan mutumin ba."Yaya Adam yayi murmushi yace, "kar ka damu babu abinda zai faru, abinda ya saka na kyale shi har nake sauraren sa saboda y'ar sa kk babu komai mun had'a jini dashi tunda ta shiga tsakanin mu amma bayan wannan kar ka d'auka da wani abun." Al'ameen ya girgiza kai yace, "Nidai jikina bai amince ba dole nasan abinda zanyi gaskiya." Yaya Adam yayi dariya ya shiga gida ya bar Al'ameen a wajan.