Sashe 43
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mubakar ya kalli Abbah yace, “Hankalin Ammah ya tashi sai waya take yi na rasa me zance mata.” Abbah yace, “kaje ka d’auko ta ka kawo ta nan anjima sai ta tafi kai ka zauna dashi a nan, Nima zan koma yanzu zamu je a san yaddda za’ayi a kashe case din nan.” Mubakar yace, “Tafiyar taka fa Abbah.”
“Sai dai wani lokacin kuma.”
“to bara naje na d’auko Ammah din”ya fad’a yana barin wajan Abbah ma ya tafi su kuma suka zauna a kujerun da suke kofar d’akin.
Fiddausi ta farfad’o ta idanu ta biyu a kwance a kan gadon amma tak’i magana sai kuka kawai da take yi wanda Mama ta rasa kukan na meye. Gaji tayi da ganin ta tana kukan tace, “Fiddausi Ki yimagana naji ki daina wannan kukan dan Allah. Tunda kika tashi baki yi magana ba ko wani abun ya same ki kika daina magana?.” Ta lumshe ido ta bud’e ta kalli Mama kamar zatayi magana sai ta share kawai bata ce komai ba.
“İn baza ki magana ba ki daina wannan kukan ance jinin ki ya hau kukan ma zai k’ara miki.” Sai a sannan tace, “Mama dama na mutu.” Jin tayi magana sai hankalin Mama ya kwanta tace, “Alhamdulillah! Da na d’auka kin daina magana ne ai, bara na fad’awa likita” ta fad’a tana fita Jim kad’an suka dawo da likita yazo kan Fiddausi ya tsaya yace, “me kike ji yanzu?.” Fiddausi tace, “babu komai.”
“Kanki baya ciwo?.”
“Yana yi amma ba sosai ba, sai dai jikina babu dadi.”
“Eh naga alamun duka a jikin ki, wannan dukan ne ya saka kike jin haka amma a hankali zaki dawo daidai.”
“Likita an yi min test?.”
“Anyi miki?.”
“Bani da HIV?.” Da sauri ya kalle tajin abinda tace Mama ma kallon ta take yi yace, “Bamu gwada jinin ki a wannan b’angaren ba, amma yanzu a siyo sirinji sai a gwada a gani.”
Fiddausi ta kalli Mama kamar zata yi magana Mama tace, “ga wani d’azu da akace a siyo za’a yi mata gwajin malaria kuma ace anyi.” Karb’a yayi yaja jinin ta yayi rubutu a takarda ya bawa Mama yace, “aje lab a gwada.” Mama ta karb’a tana kallon Fiddausi gaban ta yana fad’uwa sosai tace, “gwajin k’angamau Fiddausi? Me ya had’a ki dashi?.” Fiddausi tace, “ayi kawai Mama.” Mama tace, “bara naje.” Jim kad’an sai ga Mama ta dawo ta bawa likitan Sakamakon gwajin ya kalla ya kalli Fiddausi yace, “Baki da cutar hankalin ki kwanta?.” Tayi Ajiyar zuciya bata ce komai ba ya kalli Mama yace, “To ai zaku iya tafiya gida, aje tayi wanka taci abu mai kyau a sake bata dama tayi bacci sosai dana akwai rashin sa sosai a idanun ta.”
Mama tace, “to shikenan bara na kira mahaifin ta sai mu tafi.” Waje ta fita ta samu yana wajen ta fad’a masa ta koma ta kwaso kayan su a dawo ta rik’e Fiddausi suka fita daga d’akin suka shiga mota suka tafi.
Kamar yadda yace kuwa an saka tayi wanka ta sha shayi tayi sallah ta sha magani sai kuwa baccin ya sake d’auke ta. Sai bayan i’sha ta farka ta fito falo ta tarar da Mama da y’an gidan su gabad’aya harda Abba da Kawu tana fitowa kowa ya kalle ta tace, “Sannun ku.” Yaya tace, “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Fiddausi haka kika koma?.” Bata ce komai ba ta wuce tayi alwala ta dawo tayi sallar i’sha a falon a zaune dan bata iya tsyauwa sosai bayan ta isar ta kwanta akan sallayar bata ce komai ba.
Mama tace, “sannu Fiddausi.” Kai kawai ta d’aga bata ce komai ba Abba yace, “sannu Allah ya baki Lafiya.” Lumshe ido tayi ta bud’e sai ta fara kuka Mama ta lura da ita tace, “Wai kukan nan da kike aikin yi na meye?.” Batayi magana ba sai ta share hawayen ta a nan bacci ya sake d’auke ta. Ganin hakan y’an uwa ta duk sai suka tafi aka kashe mata haske aka barta tayi baccin.
Washe gari tun kafin ta tashi y’an uwan ta sun zo kowa burin sa yaji me ya same ta ina kuma mijin nata yake ta koma kamar alamajira haka, sai da tayi wanka aka bata abinci taci sannan Abba ya zauna da ita ya fara jera mata tambayoyi daman tasan sai anyi haka yace, “Fiddausi d’an sandan da ya rako ki yace kun gudo ne daga wajan yan garkuwa da mutane haka ne?.” Ta girgiza ki alamun A’a hawaye ya zubo daga idon ta Abba yace, “to me ya faru? Ina kika shiga ko a waya ba’a samun ki? Ina mijin ki yake?. Meya same ki kika koma haka?.”
Cikin muryar kuka tace, “Daga gidan sa muka gudo ba wajan garkuwa da mutane ba, mun fad’awa y’an sanda haka ne kawai dan kar su mayar damu gidan.” Abba yace, “to ina kika shiga har gidan da aka kai ki anje amma bakya nan?.” Sai ta fashe da kuka mai sauti tace, “karya yayi min Abba, naga tashin hankali da bala’i a gidan sa, na wahala naga masifa kala-kala wacce ko a mafarki banyi tunanin ganin irin ba.Shi ya hana ni amfani da waya ya kulle ko wacce number ta mutanen gidan nan babu wanda zan samu ko daga wacce waya zan kira. Kullum cikin fargaba nake da tashin hankali, bana bacci, bana iya cin abinci, kuka shine abokina shine abokin shawarata” ta fad’a tana kuka sosai wanda ya hana ta kasa cigaba da maganar.
Abba yayi murmushi ya kalli Mama ya sake kallon Fiddausi yace, “ina jin ki.” Ta tsayar da kukan tace, “Abba dan luwad’i ne.” A tare kowa yace, “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!.” Mama tace, “luwadi Fiddausi?.” Ta daga Kai tace, “eh Mama, ba kuma da iya maza ba har matan sa babu wacce take tsallakewa.” Abba ya sauke numfashi ya kalle ta sosai yace , “kema baki tsallake ba kenan?.” Ta runtse ido ta sake fashewa da kuka ganin hakan kowa yasan ne yake nufi jikin kowa yayi sanyi banda Abba.
Tace, “Alhaji ba mutum bane dabba ne, rayuwar gidan sa babu wanda zai sani sai ya shiga Abba. Domin kuwa duk wata hanyar da zaki bada labari ya toshe domin baza kije ko Ina ba har sai in shine ya sake ki. Nida Aliya da Naja’atu matan sa muka had’a plan Allah ya bamu sa’a muka fad’a hannun y’an sanda. Baya bari aje ko ina saboda kar ki fad’a wani halin sa, in ma fitar ta zama dole za’a had’a ki da masu kula dake ta yarda waya baza ki yi ba dan hatta bandaki zaki je sai an raka ki. Na sha wahala ko mak’iyi na bana fatan yasha wahalar da na sha a gidan sa.”
Abba yace, “wahala ai basai kin fad’a ba Fiddausi gata nan a bayyane a tare dake.” Ta kalli Abba tace, “Abba duk yadda zan kwatanta tashin hankalin da na shiga baza ku fahimta ba ni kawai nice nasan halin dana fad’a.”
“Daidai kenan ai Fiddausi, Ba ke kina zab’i kud’i akan kwanciyar hankali ba? Yanzu kin banbance tsakanin guda biyun kenan?.” Ta runtse idanun ta danasani ta gama mamaye zuciyar ta da jikin ta tace, “na banbance Abba, na gane yanzu kwanciyar hankali daban kudi daban. Ko a gidan akwai kudin duk abinda kike so akwai amma babu kwanciyar hankali Abba. Nayi danasanin zab’ar kudi, nayi nadama wallahi.”
“Nadamar ta banza ce ai ba tunda ba ta Tsakani da Allah kika yi nadamar ba sai da kika sha wahala sannan kika yi, saboda tsabar son duniya kika kashe auren ki da kanki, kika kashe dan cikin ki da kanki
kawai saboda zaki auri mai kud’in da kike ganin shine farin ciki a wajan ki. Kuka had’a baki da Kawun ki akayi aure bana nan balle nace zan hana saboda bincike ko wani abun. Yanzu gashi kin je kin dawo kina kuka kina dana sani bayan kin aikata babban zunubi a wajan Allah. Ke a tunanin ki wannan abubuwan da ya faru a kanki meye?.”
Kuka take yi sosai ta kasa magana dan muryar ta ta dashe tana shashsheka a haka ta bude’e baki tace, “Ban aikata ina sane ba Abba, ta k’arfi akayi amfani dani, wallahi nan aikata ina sane ba.”
“K’arya kike, akan kud’i babu abinda baza ki yi ba dan an biya ki anyi luwadi dake a wajan ki ba komai bane. Tunda kika iya kashe d’an cikin ki akan kud’i dan ance min an biya ki Kinyi luwad’i ai ba wani abun bane ba.” Kai take girgizawa hawaye wani yana bin wani tace, “A’a Abba, wallahi ban aikata ba, wallahi banyi ina sane ba, wallahi Allah d’aya kenan fin karfina akayi.”
Abba yace, “to my yanzu da kika dawo mana me zamu yi miki? A abinda kika fada kaf banji kince ya sake ki ba kinga matar sace sai ki tashi ki koma gidan kud’i da kwanciyar hankali dan a nan bamu dasu.” Tayi hanzarin rik’e kafafun Abba tace, “ka yafe min Abba nayi kuskuren da bazan manta dashi ba, na aikata abinda har abada bazai daina bibiyata ba ka yafe min dan girman Allah. Gwara ka yanka naman jikina da kace na koma wannan gidan, kayi hak’uri Abba ka yafe min.” Abba yace, “ni ance miki kin yi min laifi ne? Zab’ar abinda kika ga shine daidai a rayuwar ki kika yi to meye na laifi a nan?. Kin kashe auren ki, kin kashe d’an ki, kin saka an kama tsohon mijin ki kin wulakanta shi saboda kawai kina ganin ke a lokacin ba d’aya kuke ba. Kin auri mai kud’i daidai ke wanda kika ce shine farin ciki ki je kina farin cikin ki to meye na dawo min gida kina kuka?.”