← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 93

Sashe 13

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukayya tace, "to meyasa hujjar taki?."
"Na farko kinga an san ibrshim an san halin sa da yanayin iya rik’e matar sa da yayi a baya nasan ke kanki kin shaida da hakan, an san bashi da wata halayya mara kyau yana kokari a kan gidan sa duk da bashi da wani k’arfi sosai amma iyalan sa sunfi k’arfin ci da sha. Na biyu kuma bashi da mata a yanzu in ya aure ki ke kad’ai ce matar sa sai Amir wanda nasan zaki masa tarbiyya fiye da yadda Fiddausi zatayi masa. Na uku kuma dangin sa basu da matsala zasu so ki su qaunace ki baki da fargabar dangin miji ko abinda yayi kama da haka ba. Na hud’u yana sonki da gaske ba da wasa ba, soyayyar da yake miki ce ta saka ya furta zai aure ki. Shi kuma Umar an san shi amma ba'a san wacece matar sa ba, watakila bata da ra’ayin zama da kishiya zata iya yin komai da ta fitar dake, sannan dangin sa sun karb’e ki ko A'a, wanne irin rik’o yake yiwa matar sa?, duk ba'a sani ba saboda duk binciken ka akwai abinda sai ka shiga zaka gani. Duk binciken Yaya Adam bai gano wata halayyar Yusuf ba sai da na shiga shiyasa nidai Allah ya sani nafi son ki auri İbrahim."

Rukayya da take jin ta tace, "Baba ma yafi son Ibrahim kawai baya so lokaci d’aya yace min na auri Ibrahim ne naga kamar yayi min dole shiyasa ya bani dama na Zab’i wanda nake so amma in a son ransa ne na d’auki Ibrahim. Ni kuma wani iri nake ji wallahi in na tuna mijin Fiddausi ne fa har d'a akwai tsakanin su sai naji yana fice min daga tunani gabad’aya."
"Yanzu fa ba mijin Fiddausi bane ki dinga cewa tsohon mijin ta."
"Tsohon mijin nata fa, meye bata sani nasa ba? In na aure shi nan gaba nasan tabbas zata zo gidan dan kin San ta ba kunya gare ta ba kuma zasu had’u zata ga kamar ma ragowar tane Ibrahim din ta rage ta yar na d’auka. Kin sanni da kishi in na tuna hakan sai naji ni auren sa baya zuwa kaina."

Ameena tayi dariya tace, "to ai a baya take matar sa ba a yanzu ba, dan ya aure ki kece kike a matar da ita kuma tsohuwar matar sa."
"Amma meye bata sani ba nasa?."
Ameena ta sake yin dariya tace, "ke dallah ki kawar da wannan tunanin daga zuciyar ki shaid’an ne kawai yake kawo miki wannan tunanin, nagartar sa zaki gani da cancantar sa ba wannan k'ananun tunanin da kike yi ba mara amfani."

Rukayya tace, "Shikenan dai kawai Allah zab’a mana abinda yafi alkhairi."
"Ameen. Ki dai tsaya kiyi tunani kar ki yi abinda zakiyi dana sani. İn zuciyar ki bata İbrahim kar ki d’auka ki zab’i Umar din.”
"Ni yanzu har bana so yamma tayi Baba ya kira ni yace na fad’a masa wa na d’auka, gabana har fad’uwa yake."
"To ke yanzu wa kika d’auka?."
"Ban sani ba wallahi."

Ameena tace, "yanzu in Baban ya kira ki zuwa zaki kice masa baki sani ba?."
"Ni kawai zan bashi dama Ameena ya zab’a min duk wanda yaga yafi cancanta dani, dukka su biyun zan iya zama dasu kawai ya zab’ar min in Ibrahim ne Allah yasa haka shine alkhairi, in Umar din ne Allah yasa shine mafi alkhairi."
"Shikenan kin huta, Allah ya tabbatar da alkhairi."
"Ameen ya Allah. Sai na shigo." Daga nan sukayi sallama ta kashe wayar.

Jingina tayi da bayan gado tayi shiru tana sauke numfashi idanun ta a kulle kafin ta bud’e ido a lokacin kiran Ibrahim yake shigowa cikin wayar ta, kamar bazata d’auka ba sai kika ta d’auka ta saka a kunne tayi sallama daga can b’angaren ya amsa tare da fad'in, "kin wuni Lafiya?." Rukayya tace, "Lafiya lau, yasu Hajiya?."
"Tana gaishe ki."
"Ina amsawa." Bata sake cewa komai ba tayi shiru yace, "Rukayyan Ibrahim zance ko?."

"Yaushe na zama ta Ibrahim?." Yayi murmushin da sai da taji shi a zuciyar ta yace, "Ni na fad'a kuma hakan ne zai tabbata."
"Sanin gaibu ai sai Allah."
"Nima bance nasan gaibu ba ai Rakiya, ina fadar abinda nake ganin zai yu ne."

Kamar yana gaban ta ta turo baki gaba tace, "nifa ba sunana Rakiya ba." Yayi dariya mai sauti wacce ta saka ta murmushi itama daman da ya tsokana tane ya fad’a yace, "ya sunan ki?."
"Rukayya!" Ta fad'a cikin salo wanda ya saka shi sake yin murmushi yace, "ni Rakiya na sani sunan ki."

"Allah nima zan ce maka Iro." Yayi dariya kad’an yace, "ni ai ba sunana bane dan Mu'azzam nake ke kuwa sunan ki Rakiya." Itama tayi murmushi tace, "kai kad’ai kake fad’a min sunan nan kaima dan tsoho ne daman tsofaffi ne suke b'atawa mutane suna." Yayi dariya yace, "na yarda da abinda kika ce kema ki amsa sunan ki Rakiya."
"Allah bazan amsa ba."
"Zaki amsa fa ni na fad'a miki." Murmushi tayi bata ce komai ba jin hakan ya saka yace, "Rukayya!."

Lumshe ido tayi ta bud’e a duniya tana jin dad’i in yace Rukayya tun suna tare da Fiddausi ta kan cewa Fiddausi ibrshim da larabci yake cewa Rukayya balle yanzu da in ya fad'a take ji har ranta tace, "Na'am."
"Zan kula da rayuwar ki in kika amince kika bani amanar kan ki ina tabbatar miki da babu dana sani a cikin zama dani, zan saka ki farın cikin da baki tab'a hasashen zaki kasance a cikin sa ba Rukayya. Nasan akwai wani tabo da kike kallona dashi amma ajjiye shi nake so ki yi a gefe ki kalle ni matsayin wanda yake neman auren ki baki san shi ba ya kawo kansa wajan ki dan neman alfaramar shiga zuciyar ki. Bana so ki dinga kallon baya ki kalli yanzu ki d’auka baki sanni ba ban sanki ba Rukayya, indai zaki kallo baya baza ki amince dani a zuciyar ki ba, fatana ki amince dani ina tabbatar miki da baza nadama ba sai farin ciki wanda zai mamaye dukkan rayuwar ki.”

Shiru tayi tana jin kalaman sa har zuciyar ta domin kuwa a nutse yake yin maganar dole ka saurara koda baka so saboda yadda yake kalaman a nutse zasu shiga jikin ka. Kafin tayi magana ya sake cewa, "Dan Allah Rukayya ki daina kallona a yadda kike kallona, ki kalle ni matsayin wanda zai aure ki kuma masoyin ki. Rukayya da gaske ina sonki son da nake miki shine ya kawo ni wajan ki, in kin tashi yanke hukunci ki tausaya min domin zuciyata tayi rauni sosai in taji akasin abinda take so taji zata iya shiga yanayin da baki yi tunanin zata shiga ba."

Kasa magana tayi sai shiru da tayi tana jin sabon yanayi a cikin zuciyar ta amma ta kasa ce masa komai, "Rukayya!." Ya sake fad'a tace, "Uhum!."
"Kina jina?."
"Eh."
"Naji kin yi shiru baki ce komai ba."
"Jira nake ka gama" ta fad'a tana wasa da gashin bargon da yake jikin bargon da take kwance a kai.

Yayi murmushi yace, "to na gama fad’i abinda zaki ce." Tayi dariya tace, "Baka gama ba ka cigaba da fada kawai." Murmushi ya sake yi yace, "Ina zuwa ana Kira na" ya fad'a yana datse wayar tabi wayar da kallo ganin sunan da tayi masa saving ya d’auke daga kan screen din alamun ya kashe ta kulle ido ta bud’e a bayyane tace, "Ibrahim kar ka manta kai fa tsohon mijin kawata ne Fiddausi, taya zan iya auren ka ina kallon ka matsayin mijina bayan kayi rayuwar aure da kawata?."

"Rukayya!." Jin muryar Umma ya saka ta mik’e zaune tace, "Na'am Umma."
"Ga bak’i kin yi ki fito ku gaisa" tana fad'a ta fita ita kuma ta tashi ta fito. Cousins dinta ta gani mata suka zauna suna hira sosai har akayi sallar la'asar suna tare.

Bayan sallar i'sha Baba ya saka Zuhra ta kira ta tunda taji kiran gaban ta ya fad’i haka ta tashi zuwa  d’akin sa ta same shi a zaune yana cin abinci ta shiga da sallama ya amsa yana kallon ta har ta samu waje ta zauna tace, "Baba gani." Ya ajjiye cin abincin yace, "ya maganar mu dake? Kin San yau nace zaki fad'a abinda kika tsayar ko?." Ta d’aga kai alamun eh yace, "To ina Jinki."

Ta da’go ta kalli Umma da take kallon ta ta sake sunkuyar da kai tace, "Baba ni na baka dama a cikin su biyun wanda Kaga ya dace dani ka aura min shi kawai." Baba ya kalle ta sosai a nutse yace, "meyasa kika ce haka? Bakya son su ne dukkan?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "to meyasa kika ce kin bani dama? Ai in kina son  mutum d'aya shi zaki fada, wannan Zab’i da kika bani kamar dukkan su bakya son su ne ai ko?" Ya fad'a tana kallon umma.

Umma tace, "Eh to, watakila dukkan su tana jin zata iya zama dasu ne shiyasa ta baka dama ka bata wanda kaga yafi cancanta." Baba ya kalle ta yace, "Haka ne?."
Ta d’aga kai tare da fad’in, "eh haka ne Baba."
"Kin tabbatar dukkan su zaki iya zama dasu a matsayin mijin ki?, duk wanda na baki kin tabbatar zaki iya zama dashi a matsayin mijin ki?.”
"Eh Baba zan iya."
"Kar ki cutar da kanki fa ki tilastawa zuciyar ki abinda so. Na fad’a miki in duk su biyun basu yi miki ba Wallahi babu mai miki dole, ki fad’i abinda yake zuciyar ki.” Ta gyara zama tace, "Zan iya Baba." Baba ya girgiza kai yace, "Shikenan to Allah yayi miki albarka yasa zab’in nawa ya kasance alkhairi a gare ki."
Chapter 13 · 0% Book details