Sashe 22
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mariya tace, "in sha Allah wanna ta daban ce, addu'ar da akayi ai bazata fad’i k’asa a banza ba." Hajiya tace, "abin mamaki mahaifin ku yace mahaifin Fiddausi ne ya amashi auren Rukayya kuma shine ya bada sadaki. Yace sai murna yake kamar komai bai faru ba."
"Ai Hajiya daga jin yadda aka k’are da d'aurin aure daga zuwa kai kudi kema kin san farin ciki ne ya jawo hakan, Alhaji yace ai baki ji yadda ya dinga bashi hak’uri akan abinda Fiddausi tayi ba nace ashe sun sani" Hadiza ta fad'a tana d’aukar lemon da yake Leda tana b’arewa .
Hajiya tace, "sun sani mana, ai zancen duniya baya b’uya. Kinga wannan kulle shi din da ta saka akayi? Wallahi kamar yayi kuka haka ya dinga bawa Alhajin ku hak’uri. Shi kansa ya san d’iyar sa tayi rashin miji, Bawai yabon kai ba amma duk inda taje sai dai a fishi da kud’i ba dai kwanciyar hankali ba." Mariya ta kalle shi baice komai ba har lokacin tace, "ikon Allah kenan, kaga sai ku tare a sabon gidan ka. Kai babu Wanda ya kai Allah iya tsara wa mutum lamuran sa, ka rabu da tsohuwar mata, tsohon gıda, tsohuwar damuwa, tsohon aiki. Yanzu kuma sabon gida, sabon abin hawa, sabuwar amarya, sabon aiki. Ka gode Allah Ibrahim Allah yana shiga lamarin ka” ta fad'a tana dan dukan sa a kafad’ar sa a lallai sai yayi magana.
Murmushin ya sake yi amma bai yi magana baHajiya tace, "Yanzu sai a fara batun lefe ko? Kud’in da kake tarawa a wajena sai a fito dasu ayi hidima. Yadda suka karrama mu muma mu karrama su." Sai a sannan Ibrahim yace, "Eh gobe in Allah ya kaimu Yaya da Mariya zasu je su fara siyo abinda ya kamata, Tunda akwai kudi a hannnuna ina ganin zasu isa dan ba karya za'a yi ba."
Mariya tayi dariya tace, "Allah ko ango? Wallahi a shirye kake tsaf abin ka.” Yayi dariya ya tashi ya fita yana jin su suna cigaba da tattaunawa akan lamuran auren yana jin dad'i a har zuciyar sa kamar auren fari yayi.
Ameena tana zaune a falo suna charting ita da Rukayya tana bata labarin abinda ya faru sai murmushi take yi na farin ciki in kaga yadda take yi sai ka d'auka kalaman soyayya ake fad’a mata take murmushi.
Yaya Adam ne ya shigo ganin tana ta murmushi ita da waya ya zauna yace, "Aminatuwa keda wa kike murmushi haka?." Sai a sannan ta kalle shi tace, "Rukayya ce Yaya, Sannu da zuwa." Bin ta yake da kallo cikin farin ciki ganin ta dawo kamar ba ita ba ta manta da komai yace, "Yauwa. Da Rukayyan kike wannan murmushin?."
"Ai abin farin ciki ta fada min ne Yaya." Yayi dariya yace, "ai naga alama."
Dariya tayi ta cigaba da danna waya kafin yace, "in kika gama idda ne kike so kiyi Ameena? Aure ko karatu?." Sai da gaba ta ya fad’i ta ajjiye wayar a cinyar ta tace, "Karatun dai Yaya."
"Auren fa?." Ta sauke numfashi tace, "nayi daga baya."
"Allah ya bada nasara" ta amsa da amin kafin tace, "Yaya gobe zanje gidan su Rukayya."
Ya kalle ta yace, "waye yace miki wacce take idda tana fita?." Ta rausayar da kai tace, "ai ba wani wajan zance ba iya gidan su ne kawai."
Yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "zan gani zuwa goben in akwai damar na bari kije din." Tayi murmushi tace, "to na gode." Zaytun ce ta tawo tayi wajan sa tana kiran Abba ya d’auke ta yana yi mata wasa iya kuma ta cigaba da danna wayar.
Bud’e k’ofar akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo ya kalli Ameena ya ganta da riga doguwa kamar yadda ta saba shigar ta ya kalli Al'ameen yace, "muje ko?" Ya fad'a tana tashi tsaye. A sannan Ameena ta kalli wanda ya shigo tayi murmushi tace, "ina wuni Yaya Al'ameen?."
Murmushin shima yayi yace, "Lafiya lau Ameena." Daga haka bai sake cewa komai ba itama haka suka fita. Tare suka shiga mota guda d'aya Al'ameen yayi shiru yana tuk’a motar baice komai ba shima Adam din baya magana sai daga baya Al'ameen yace, "Adam dan Allah ka bani Ameena a karo na biyu."
Adam ya kalle shi yace, "Wai meye ya shiga kanka ne? Na fad’a maka idda yarinyar nan take yi meyasa kake kawo zancen ta a wannan lokacin?." Al'ameen yace, "na sani, ai ba tunkarar ta nayi ba kai na samu da maganar. Kai kasan tun kafin Ameena ta girma nake sonta Allah baiyi ni zan aure ta ba. A wannan lokacin ka bani dama dan Allah ina sonta har gobe, kafi kowa sanin waye ni." Adam yaja tsaki yace, "ka daina min wannan maganar dan Alalh ka bari ta fita daga idda komai zai biyo baya." Da to ya amsa ya cigaba da tuk’in sa amma zuciyar sa na wajan Ameena.
A b’angaren ta ma bayan ya fita Anti Aysha tazo ta zauna tace, "Ameena yayan ki shida waye suka fita?." Ameena tace, "Al'ameen ne, wai Yaya bashi da aure ne?."
Tayi dariya tace, "bashi da aure." Ta wara ido tace, "sa'an Yaya ne fa?.."
"To shima yaushe yayi auren?."
"Amma dai yayi ai."
"Ke ya tab'a aure, matar ce ta rasu a wani hatsari da sukayi da ciki a jikin ta."
Ameena tace, "Allah sarki, Allah ya jikan ta." Aisha tace, “Ameen. Kowa baki ga murnar da yake yiwa matar sa ba saboda ta same shi, Wato namijin ne tsayayye kan abinda ya shafi iyalan sa wallahi, lokacin da suka yi auren ma baiyi kud’in haka ba ana tunanin in yayi kudi zai canja mata amma ko kusa bai canja mata ba gashi ta jima babu ciki, aka dinga zai k’ara aure bata haihuwa amma bawan Allah nan bai d’aga kai ma ga kalle su ba balle yayi auren.Kai yana da nagarta sosai.”
Ameena tace, "Allah ya bashi wata mai alkhairi." Ta amsa da amin suka cigaba da wata hirar.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500
Book3
014
Fiddausi tana cikin cell na turawa an kulle ta sai kuka take tana zaune a jikin bango tana kallon kowa sama-sama dan jiri take ji sosai. Ba komai ne yake zuwa kanta ba sai lokacin da ta saka aka kama mata Ibrahim, kallon inda take tayi gashi mai kyau harda gado ta tunda inda Ibrahim yake duk fitsari wajan ga daud’a ta lumshe idanun ta hawaye na cigaba da sakkowa. A bayyane tace, “ka yafe min ibrahim, ka yafe min hakkin kane yake bina, duk abinda nayi maka sai da ya faru dani, ka yafe min” ta fad’a cikin kuka sosai kamar yana gaban ta. D’ago kai tayi tana kallon waje ta hango Alhajin a wajan y’an sandan yana tayi musu magana amma ina sun k’i amincewa su bashi dama yaje inda take, dakyar suka amince ya k’arasa ya tsaya yace, "ke wacce irin mahaukaciya ce iyee? waye ya fad’a miki a wannan danyen aikin a k’asar turawa?, waye ya fad’a miki nan Nigeria ce? Dan baki da hankali sai ki d’auki kwalba ki fasa masa kai da ya mutu fa?.”
"Kaina ciwo yake yi, ka bani magani zan mutu, kaina zai rabe gida biyu, ka taimaka min ka bani magani” abinda take cewa kenan tana juya kai cikin mayuwacin hali yaja tsaki ya bar wajan ya koma yana ta zagaye bai san ya zaiyi ba. Zuciyar sa ta fara kitsa masa kawai ya tafi ya barta in sun kaita prison shikenan ita ta jiyo shi bai dame shi ba. Ana haka sai ga Ogan nan ya shigo kansa d’aure da bandage daga gefe ya k’arasa wajan y’an sandan yayi musu bayanin yadda zasu bar Fiddausin yayi singing aka fito da Fiddausi.
Ganin yanayin da take ya saka aka wuce da ita asibiti aka kwantar da ita aka saka mata ruwa da allurai. A lokacin Alhaji Bello ya samu damar yi masa magana yace, "Sir kayi hak'uri da abinda ya faru, bata jin magana ne na rasa ta yadda zan nuna mata mahimmaci ka a wajena ta gane, ban san ya zanyi mata ba.” Yayi murmushi cikin yaren sa yace, "ina sonta kar ka damu , zan bi da ita ta ko wacce hanya dan samun cikar burina a kanta. Ka koma Nigeria ka da ita zanje meeting k’asar Germany in na dawo zaka dawo min da ita, kafin lokacin zan saka maka balance na kawo ga da kayi in komai ya faru zan mallaka maka duk abinda kake so domin kuwa ba’a tab’a kawo wacce ta burge ni kamar ta ba.” Alhaji Bello yayi dariya yace, “godiya nake Boss.”
“Ka tafi da Zainab ma, amfanin ta ya k’are.”
“An gama boss.”
Alhaji Bello yaji dad’i sosai dan baya so ya fasa in yace ya fasa ya tafi da ita gida yayi asarar kud’i masu shegen yawa, amma yanzu da yaji wannan bayanin ya gamsu sosai duk da ta b’ata masa rai da ta amince da yanzu an cika masa bankin sa da kud’i. Da wannan b’acin aka d’auke ta aka kaita gıda aka kwantar akan gado aka barta ita kad’ai sai bacci take yi bata an ma an dawo da ita ba.
Mafarki tayi wanda ya saka ta zabura ga mik’e sai a sannan ta tuna rabon ta da sallah tun a Nigeria ta sakko dakyar ta shiga band’akin da ta gani a d'akin tayi alwala ta fito tana kallon d’akin nan taga alama ta alqibla ta tayar da sallah ba tare da ta canja kaya ba dan bata dasu.