Sashe 25
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can gidan su Yusuf yana zaune a cikin iyayen nasa yayi shuru kai da ka ganshi kasan yana cikin yanayi na damuwa mai yawan gaske fuskar sa ta nuna hakan sosai a bayyane kana ganin sa abinda zai zo ranka kenan, Abbah yana ta masa fad'a yace, "Dan hauka da rashin sanin ciwon kai da rashin sanin dajarar matar ka ace d’an aikin kane zasu Kira mahaifiyar ka ya fad’a mata kuma fad’a da matar ka a harabar gida? Meye yake damun kane Yusuf?. Me ya shiga kanka kake aikata mugayen abubuwa haka?.”
Kansa yana k’asa ya kasa magana saboda ciwon da yake ji a zuciyar da Ammah tace, "Akwai zubar da mutuncin da ya kai wannan? Y'an aiki ace Sune suke raba ka fad’a da matar ka?” Ta kalli Abbah tace, “Wannan ba shine na farko ba anyi wani kuma nan gaba ma za'a sake tunda haka ya zab'arwa kansa."
Abbah yace, "wannan ai hauka ne da rashin tunani, matar ka ta aure har k’ofar gida gaban masu aiki kuzo kuna fad’a kamar wasu y’an bariki Yusuf?."
Abbah yace, "yanzu tana ina?." Yusuf yace, "Tunda na baro gidan ban koma ba, ban sani ba ko tana nan." Abbah ya sake yin tsaki ciki takaici yace, "ba’a tab'a yin irin wannan tozarcin ba a kaf zur'iar mu, mu ba’a san mu da d’aga hannu mu daki mace ba balle fad’a balle kuma ya kai ga duka a gaban masu aiki. Gabad’aya halayyar ta ta zamantakewar aure ka ta fita daban da ta kowa a gidan nan kamar kai kadai ne mai zuciya a cikin maza. Komai duka? Kai a ganin ka shine hukuncin da za’a yiwa mace? Baka San in ka saba mata ba wallahi kana d’aga hannun ka ka dake ta kafin ka sauke hannun ta rama har abada kuma mutuncin ka ya zube kuma kai ne ka jawo hakan.”
Humaira ce ta shigo da sallama Ammah ta amsa tace, "Abbah ga Asiya matar Yaya Yusuf da babar sun zo suna son ganin ka." Gaban Yusuf fad’i sosai ya d’ago ya kalli Humaira Abbah ya kalle shi kafin ya kalli Humaira din yace, "jeki ki shigo dasu." Humaira ta juya Abbah ya kalle shi yace, "Kaji kunya wallahi."
Da sallama Umma ta shigo Asiya na bayan ta suka k’araso Asiya ta zauna a k'asa kamar yadda Yusuf yake Umma ta zauna a akan kujera tace, "Barkan ku da dare da fatan na same ku lafiya." Abbah ya amsa da fad'in, "Alhamdulillah, ya masu jikin?." Umma ta kalli Asiya tace, "gata nan, daman abinda ya kawo mu kenan."
Umma tace, "Tsakani da Allah bazan d’auki duka a zamantakewar auren Yusuf da Asiya ba, ranar nan ya dake ta tayi hak’uri ta fad’a min nace tayi hak’uri yau an sake har hakan ya kai ga bazarana ga abinda yake cikin ta badan Allah ya kare ba da yanzu babu shi, akan me ai ba dan duka aka kawo masa ita ba."
Ammah tace, "Gaskiya ne."
"Yauwa shiyasa nazo dan a yiwa tufkar hanci, bazan lamunci duka ba wallahi in wani abun tayi ya kawo k'arar ta ayi mata fad’a amma duka ai ba na ma'aurata bane." Abbah ya girgiza kai yana kallon matar kafin yace, "haka ne, fad’an da muke yi masa Kenan yanzu."
Umma tace, "sannan koda wasa kar ka sake kira min ya da b’arauniya, me aka ajjiye ta d’aukar maka da zaka ce mata b’arauniya? Dan ita uwar gidsn ka tana yi maka sata itama sai kace tana yi maka akan me?. A'a Yusuf zamu samu matsala da kai akan abubuwa guda biyu dana fad’a yanzu, na farko sharrin sata da kuma duka. Irin haka ne yake kawowa mace ta fara rama duka a wajan mijin ta dan shine yake saba mata da dukan dole in ta gaji ta d’auki hannu ta rama, daga ranar da ta rama shikenan Kun zama y’an dambe.”
Ammah da Abbbah suka kalli juna babu wanda yace komai Umma ta sake cewa, "kai me ka kamata ta satar maka da zaka ce mata b’arauniya?." Yusuf dai ya kasa magana gabad’aya kamar an d’aure shi haka yake ji domin an tozarta shi kam sosai ya muzanta a gaban iyayen sa. Ace babar matar sace take wannan abun a cikin gidan su me ya kai wannan bak’in ciki.
Asiya tace, "balle ma Umma babu abinda na d’aukar masa kawai yasha tafi karfin kansa ne shiyasa" ta fad'a tana hararar sa ta k’asan idanu shi kuwa ji yayi ina ma k’asa ta bud’e ya shige ciki ya b’uya kafin a kai ga fad’ar abinda yasan sai ta fad’a. Umma tace, "kar kice min yana shan k’waya?." Asiya tace, "ba k’waya yake sha ba giya yake sha wallahi, ranar nan da ya shiga b'angaren tsohuwar matar sa na same shi yana sha har yayi min duka bakina ya fashe. Ya dinga rok’ona kar na fad’a, daman na fad’a masa indai ya kuma dukana walalhi sai na fad’a kuma gashi na fad’a kowa yaji.”
Ta kalli Ammah tace, "Wallahi Ammah yana shan giya, in ana ganin k’arya nake azo aje d'akin sa na b’angaren Ameena a duba za'a ganta, ko kuma a tambayi Ameena ai ita tasan yana shan giyar ai.”
Umma tace, "giya! Ahh gwara da akayi maganar nan a gaban iyayen sa. Bazai yu ba wallahi bazata sab'u ba wai bindiga a ruwa. D’an giya da y'ta ta cikina wacce na haifa inaaa!" Ta kalli Abbah da shi ya k’asa magana sai kallon ta da suke yi kamar tv tace, "Alhaji tsakani da Allah abubuwan da yawa, ko ya daina shan giya ko ya sakar min y'ata domin kuwa bazata zauna da dan giya ya dinga dukar min ita a banza ba wallahi bazai yu ba. In ya kashe ta Kun fi mu kud’i ya kashe banza, to bazai yu ba bazan d’auka ba wallahi.”
Abbah da Ammah dai sun kasa magana sunyi shiru babu wanda yake magana a cikin su dan basu da ta cewa shiyasa suka tsaya suna jin abinda take cewa Umma ta sake cewa, "ni zancen duka ya kawo ni sai ga maganar da tafi k’arfin dukan ma, dan giya da y'ata ina ai abun bazai yu ba wallahi, ko ka daina ko kuma ka sakar min ita bazan lamunci dukan da zata sha in ka bugu ba salon ka kashe min ka saka ni asara rana tsaka wacce bazan mayar da ita ba.”
Ta kalli Agogo tace, "To Alhaji Mun zo kuma gaban ku bani kunce komai ba.” Sai a sannan Yace, “Abinda
Kika ce gaskiya ne, za’a san abinda za’ayi.”
“mu zamu koma zan tafi da y'ata gıda in ya daina abinda yake yi yazo ya tafi da ita, amma batun shan giyar nan da akayi yanzu a sake dubawa sosai domin kuwa abu ne babba in ya sha zai iya kashe min y’a, in yaga bazai iya ba ya sake ta.”Abbah yace, "in sha Allah za'a san abinda za'a yi, Kiyi hak'uri dukkan ku."
Umma ta tashi tace, "Yauwa, na barku Lafiya." Ta rik’e hannun Asiya suka fita daga falon aka barsu su uku kowa ya kasa motsin kirki a cikin su abinda aka yi a wajan suke juyawa. Yusuf ji yayi kunyar duniya tazo ta lullub'e jikin sa, bai tab'a dana sanin shan giya a rayuwar sa ba sai a wannan lokacin, bai tab'a jin an ci mata musu mutunci ba sai a wannan lokacin, bai tab'a jin komai ya fita daga ransa ba sai a wannan lokacin. Bai tab’a jin rana d’aya an zare masa Shan giya a zuciyar sa ba sai wannan lokacin, bai tab’a gamsuwa da ya daina ba sai a wannan lokacin dan anyi mas abinda yafi tozarci tozartawa.
Ammah dai ta kasa magana tayi shiru domin abun babba ne yafi k’arfin tunanin ta tana so ta tabbatar da batun shan giyar nan dan tafi komai tsaya magana zuciya. waya ta d’auka tana dannawa kafin ta tsayar da dannawa ta saka wayar a speaker ana jin alamun tayi kira. "Asslamu alaikum Ammah barka da dare." Maganar Ameena ta bayyana sa cikin wayar Amma ta kalle shi taga ya lumshe idanun sa yana jan numfashi ta d’auke kai tace, "Wa'alaiki Salam, Ameena barka dai, ya gida?."
"Lafiya lau Ammah."
"Ameena kiran ki nayi na tambaye ki wani abu Allah yasa kar ki yi min k’arya."
"In sha Allah Amma bazan miki karya ba."
Ammah tace, "kin tabbatar?."
"In sha Allah." Ammah tace, "tsakanin ki da Allah a zamantakewar ku da Yusuf yana shan giya ko baya shan giya?." Shiru Ameena tayi kamar bata ji mai Ammah tace ba Amma tace, "kince zaki fad’a min gaskiya tambayar ki akwai nayi eh ko A'a?." Ameena tace, "Ammah." Ta dakatar da ita tace, "baku da wata alaqa a yanzu rufa masa asiri ba naki bane Ameena, a yanzu ba mijin ki bane balle ki kare shi kamar yadda kike yi a baya. Ameena Yusuf yana shan giya eh ko A'a?."
Jin yadda Ammah tayi magana a tsawace da alama ranta a b’ace yake sai Ameena tace, "eh."
"Yana sha kenan?."
"Uhum." Amma bata sake jin wani abun ba ta datse kiran ta juyo a fusace ta tsinke shi da mari mai zafi ta d’auki wayar ta cilla masa tace, "kaji kunya, Allah yayi wadara halin ka, ka cuci kanka ka kuma cuci Ameena hakkin tane ya fara bibiyar ka yanzu, ina so ka saka a sanka ba’a yi komai bama, yanzu ka fara ganin sakamakon abinda kayi Yusuf. Bana fad’a maka ba in kaine kake cutar Ameena zamu gani, in itace take cutar ka zamu gani yanzu waye yake kwashe kashin sa a hannu?. Kayi asarar rayuwar ka wallahi, ka b’ata tarihin ka ka b’ata na gidan nan.”