Sashe 81
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan ta kashe wayar ne Rukayya ta sauke numfashi tace, “Saura dawo da Fidy nan in sha Allah.” Ameena tayi murmushi tace, “ina ganin k’ok’arin ki in kina maganar nan, wai dan Allah bakya kishi ne?.” Tayi murmushi tace, “mijina ne fa taya bazan yi kishi ba Meenatuwa?.”
“Amma sai naji kina zancen zaki ce ya dawo da ita kuma babu wata fargaba.”
“To fargabar me zanyi? Matar nan itace matar sa ta farko, kafin nasan waye Ibrahim Fiddausi itace ya sani. To meye zanyi kishi a kai?. Ko a yanzu kallon fanko take min domin kuwa abinda ta rage ne na d’auka, shima in ya kalle ta wani lokacin babu halittar ta da baza ta zo idanun sa ba, to meye abin kishi da ita?.”
Ya girgiza kai tace, “kina da abin mamaki.” Rukayya tace, “Wallahi indai zai dawo da Fiddausi haka nake so, zanyi murna sosai dan ta cancanci a yafe mata kuskuren ta. Ya dawo da ita mu zauna lafiya ba fad’a balle tashin hankali.” Ameena tayi dariya tace, “watakila yayi accepting requests din naki.” Rukayya ta murmusa yace, “watakila yayi rejecting ba.”
“In ya karb’a fa?.”
“Allah ya bamu zaman Lafiya.”
“Lallai Ruky akwai daud’a a kanki.” Tayi dariya tace, “baza ki gane ba.” Ameena tayi dariya suka cigaba da hira.
Washe gari juma’a bayan sallar juma’a jama’ar masallaci suka shaida d’aure auren Ameena da Yusuf. Yusuf tunda ya tabbatar an d’aure aure nan da nan zazzabin farin ciki ya gama gauraye jikin sa, jikin sa rawa yake jikin sa yayi zafi daga masallacin ma asibiti aka yi dashi aka kwantar dashi dan a bashi magani.
Ameena kuwa a wannan lokacin tana gida ita da Anty, Yaya Adam yan shigowa gidan ta tabbatar an d’aura auren gaban ta ya cigaba da fad’uwa ya kalle su a zaune yace, “Kamar zaman makoki ake yi, ina su Sumayya basu zo ba?.” Anty Aysha yace, “suna hanya ni na sani.” Ya kalli Ameena yace, “to Ameena kin zama matar Yusufa a karo na biyu, ga sadakin ki Al’ameen shine ya bayar” ya fad’a yana mik’o mata sai jikin ta yayi sanyi sosai gaban ta yana fad’uwa.
“Zo ki karb’a mana.” Ta taso ta karb’a ta zauna a kusa dashi a kan carpet yana sama a kujera yace, “mijin naki kuma yana kwance babu lafiya.” Anty Aysha tace, “to! Meya same shi kuma a wannan ranar ta farin ciki?.”
“Farin ciki mana, wallahi ana d’aura auren ya tabbatar an d’aura sai zazzab’i ya rufe shi sai da aka wuce dashi asibiti, yanzu ma yana can.” Aysha tayi murmushi tace, “ikon Allah kenan, wata soyayyar bata bayyana sai an samu sila.”
Ya kalli Ameena yace, “baza kije ki ganshi ba?.” Sai ta kawar da kai yayi murmushi yace, “jibi dai zai zo ku tattara ku tafi, nima Monday mu wuce cross river.” Ameena ta share hawayen idanun ta ganin tana kuka sai ya kalle ta yace, “kar kiji komai Ameena, yadda akayi addu’a a kan wannan auren naki ba’a yi a lokacin baya ba, a zuciyata ina jin wannan Karon babu damuwa wallah, ki kwantar da hankalin ki babu komai sai alkhairi da farin ciki.” Ameena ta murmusa tace, “Allah yasa Yaya. Na gode Allah ya saka da gidan aljanna.” Ya amsa da amin ya tashi yace, “sai ki tashi ki shirya kafin y’an uwan ki su zo, da kunya ace amarya ko wanka batayi ba” ya fad’a dan ya tsokane ta.
Sai tayi dariya shima haka ya wuce ta ta tashi ta wuce daki. Tana zaune kuwa suka zo suka sakata a gaba wannan yace wannan waccan tace wannan, ita dai tak’i yarda ko lalle ayi mata balle kuma ace ta sha wani abun da sunan amarya, fir tak’i tace ita a barta a haka a hakan take son zama dole suka rabu da ita,
Har ranar lahadin Ameena babu abinda tayi ta kuma ce bazata yi ba, duk sun kyale ta babu Wanda ya tilasta mata har lokacin kuma basu yi koda waya da Yusuf ba dan tace bata bukatar hakan shima kuma har lokaci bai warware sosai ba. A daren ranar lahadin Anty ta saka ta ta shirya cikin kaya masu kyau tana zaune a kan katifa Zaytun tana zaune tana game itama a kusa da ita kayan su iri d’aya sai dai na Zaytun dinkin y’an kanti akayi mata Yaya Adam ya shigo ya kalle ta yace, “Ameena ga Yusuf yazo zaku tafi.” Ta kalli Yaya sai kuma idanun ta suka ciko da hawaye ya bata makulli a hannun ta yace, “koda zaki zo d’aukar kaya in Mun tafi ki bud’e gidan ki d’auka sai ki bawa Al’ameen makullin. İn baya nan sai ki rik’e a hannun ki.”
Hannun ta ya rik’e ya zauna kusa da ita yace, “matsayina na mahaifin ki kuma yayan ki ina ji a zuciyata nayi abinda ya dace na bada ke ga Wanda yake son ki ya kuma yi alqawari rik’e auren ki. Alqawari daya nake so ki yimin a yanzu.” Tayi shiru bata amsa ba yace, “Kiyi min alqawarin babu abinda zaki sake b’oye min na gidan ki, farin ciki ko akasin sa ina so na sani, koda ciwon kai kika yi bana so ki b’oye min Ameena.”
Tace, “nayi alqawari Yaya bazan sake b’oye komai ba. Nima bazan sake abinda nayi a bawa ba yin hakan shine ya cutar Dani.”
“Sannan ki yiwa mijin ki biyayya kar ki kalli baya ki kalli yanzu kamar yadda yace na tabbata zaki ga canjin da zaki ji dadi sosai.” Nan ma tayi masa alqawarin yace, “Allah ya baki farin ciki mai d’orewa, ya dawwamar da auren ku har aljanna.” Ta amsa da Amin ta kwanta a jikin sa tana kuka sosai yana murmushi yace, “ya İsa haka mana, lokacin auren ki dashi na farko ban samu damar magana dake ba, amma a yanzu da nake magana dake sai na kasance cikin farin ciki da annushuwa sosai, nake ji a raina na samu matsayin uba ba Yayan ki ba.”
Ya d’ago ta yace, “tashi muje yana zaman jiran ki ba Lafiya ce dashi sosai ba.” Tare suka fito Zaytun tana biye dasu da wayar Ameena din a hannun ta Yusuf yana gano su ya mik’e tsaye bai san ya mik’e ba Yaya Adam ya rik’e hannun sa ya saka hannun Ameena a ciki yace, “amana, alqawari, tabbatarwa, cikawa, dawwamar, samawar, farin ciki, nishadi, annushuwa, duka ina so su tabbata akan Ameena. Gata nan amana a wajan ka in ka wulakanta Ameena a wannan lokacin Allah ba zai barka ba.” Ya matse hannun Ameena a hannun sa yace, “na karb’i amanar na kuma ayi alqawarin tabbatarwa har a tashi duniya.” Al’ameen ne ya shigo yana cewa, “badai har an gama bada amanar ba?.”
Adam ya Harare shi yace, “sai yanzu zaka shigo?.”
“Ai ban makara ba tunda ga ta, na tsaya shirya mata bazata ne.” Ya kalli Yusuf yace, “Mun baka amanar autar mu Ameena, in ka saka mata damuwa ka tabbata a cikin munafukai, domin kayi alqawari ka sab’a, Muna amince maka muka kayi ha’inci. Ka dubu Allah duk abinda kayi mata bama wajan Allah yana kallon ka kuma zai sanar damu abinda kake mata mu kuma sai inda karfin mu ya k’are.”
Yusuf yace, “in sha Allah baza kuyi kuka dani ba, zan rik’e Ameena dakyau fiye da yadda na rik’e ta a baya.” Al’ameen yace, “in ka aikata hakan ka rik’e alqawari ka kuma cika dan halak.” Ya kalli Ameena yace, “kanwata akwai kyautar dana ke so na baki” ya fad’a yana saka hannu a aljihu ya d’auko key na mota ya mik’a mata yace, “sabuwar motar na siya miki irin wacce kike so, gata can a ajjiye tana jiran ki.”
Ameena ta karb’i key din tace, “Na gode Yaya, Allah ya saka da alkhairi.” Yusuf ma yayi murmushi yace, “Allah ya saka da alkhairi.” Ya amsa da amin hannun sa yana cikin na Ameena suka fito har harabar gidan ga sabuwar mota nan dal a ajjiye bak’a mai kyau sosai mai tsada ta kalli motar dan ta burge ta sosai ta kalli Al’ameen tace, “Na gode Yaya Al’Ameen, Allah yayi maka Zab’i na alkhairi, Allah ya baka farin ciki a duniya da lahira.” Anty Aysha ma tayi masa godiya sosai dan taya Ameena.
Yayi murmushi ya amsa Yaya Adam yace, “zaki bar motar a nan in yaso tunda na baki key na gidan duk sanda kike son d’auka sai kizo ki tafi da ita.” Ta d’aga kai cikin gamsuwa tana jin yadda ya matse mata hannu kamar zata gudu suka k’arasa cikin mota suka shiga suka ja motar suka bar cikin gidan zuciyar ta cike da kewa da kuma tunanin rayuwar da zata sake yi a gidan Yusuf.
Babu wanda yake magana a cikin mota hana tafiya tana gefe Zaytun tana baya har lokacin wayar Ameena ce a hannun ta kafin ta ajjiye ta mik’e a bayan motar tace, “Mummy unguwa zamu je da daddy?.” Shiru tayi bata amsa ba sai Yusuf ne yace, “Eh Ammata, Unguwa zamu je.”
“Daddy tare da kai?.”
“Eh dani.” Sai tayi dariya alamun farin ciki shima yayi ya saci kallon Ameena ya ganta fuskar ta gata nan dai ita ba farin ciki ba kuma ba akasin sa ba.
Gidan Ammah suka wuce ya tsaya da motar sai ya dafe kansa yayi k’aramin tsaki tace, “ciwon nan yana damuna sosai.” Ya kalli Ameena har lokacin bata kalle shi ba yace, “my choice zamu shiga wajan Ammah.” Sai a sannan ta juyo da ido ta kalle shi sai da gaban da ya fad’i haka nan Alalh ya dasa masa shakkar ta a zuciyar sa.
Idanu suka had’a yayi murmushi yace, “Ammah tana jiran zuwan ki.” Bud’e motar tayi ta fita shima ya bud’e shi da Zaytun suka shiga cikin gidan. Tana shiga falon sai ihuuu Humaira ta taso a guje ta rungume ta tana cewa, “Welcome back sis.” Murmushi tayi ganin su duk a falon gabad’ayan su har Yayan su ta Abuja da alama kowa zaman jiran zuwan ta yake yi tayi murmushi dan taji dadin hakan sosai ta kuma san indai akace so dangin Yusuf suna sonta, ta kalli Humaira cikin murya k’asa-k’asa tace, “kin zama lukuta.”